Babaji

5692 Posts

Shettima ya isa Ivory Coast halartar rantsar da Shugaba Ouattara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa birnin Abidjan na ƙasar Côte d'Ivoire inda zai wakilci Shugaba Bola Tinubu yayin taron rantsar da Shugaba Alassane Ouattara a karo na huɗu a karagar mulki. Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ya bayyana haka a wata takarda a daren Lahadi wayewar Litinin. Shettima zai shiga sahun sauran shugabannin ƙasashen Afirka da wasu daga ƙasashen ƙetare da za su halarci taron, wanda za a yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke birnin Abidjan a yau Litinin. A…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ceto 100 daga cikin ɗaliban Neja da aka sace

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta yi nasarar ceto ɗalibai guda 100, kamar yadda wata majiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da wani rahoton gida suka bayyana a ranar Lahadi. Ɗaliban, waɗanda ƴan Makarantar St Mary's Catholic School Papiri ne na Jihar Neja, za a miƙa su ne ga jami'an ƙaramar hukuma a Neja yau Litinin, a cewar majiyar. Mai magana da yawun shugaban ƙasa Sunday Dare ne ya tabbatar wa AFP batun sako yaran duk da cewa har yanzu akwai wasu guda 165 da ba a san halin da suke ciki ba da suka haɗa da ɗalibai…
Read More

Shugaban sojin sama ya ziyarci matuƙa jirgin da ya yi hatsari a Neja bayan sun tsira

Shugaban sojojin saman Nijeriya (NAF), Air Marshal Sunday Aneke, ya ziyarci matuƙa jirgin saman NAF Alpha Jet da suka yi nasarar tsalle daga jirgin kafin ya yi hatsari a ƙauyen da ke yankin Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja. Jirgin ya yi hatsari ne ranar Asabar yayin da ake gudanar da gwajin aiki (post-inspection functional check flight) a sansanin NAF da ke Kainji. A sanarwar da rundunar sojin saman ta wallafa a Facebook, NAF ta ce ziyarar ta shugaban hafsan sojojin saman na da nufin jinjina jarumtaka, ƙwarewa da hangen nesan matukan a lokacin matsalar da jirgin ya samu a…
Read More

Tsaro: Ribaɗu ya gana da ƴan majalisar Amurka a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya ce ya gana da tawagar ƴan majalisar Amurka a yau Lahadi a Abuja. Hakan na zuwa ne bayan da ta iso Nijeriya domin bincika gaskiyar iƙirarin yi wa Kiristoci kisan gilla da ya tada hazo a makonnin da suka gabata. Ribaɗu ya bayyana cewa ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba. A wani saƙo ta kafar X Ribaɗu ya ce tawagar ta…
Read More

Rundunar sojoji ta dakatar da karɓar ritaya daga jami’anta

Rundunar Sojin Nijeriya ta dakatar da dukkan nau'ukan ritaya ga wasu zaɓaɓɓun hafsoshi bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci akan lamuran tsaron ƙasa. A wata takarda da rundunar ta fitar a ranar 3 ga watan Disamba, ta ce an ɗauki matakin ne domin a cigaba da amfani da ƙwararrun hafsoshi yayin da ake faɗaɗa yawan dakarun saboda rashin tsaron da ya ta'azzara. Dakatarwar ta shafi waɗanda suka kure a shekarun aiki. Rahotanni sun ce hafsoshin da ba sa son ƙarin wa’adin za su iya yin ritaya kamar yadda aka saba, amma wadanda suka cigaba da aiki ba za…
Read More

‘Yan sanda sun kama shahararren ɗan bindigar da aka danganta da kisan jami’ai a Benuwai da Nasarawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Jihar Benuwai, ta kama wani da ake zargi da hannu a manyan hare-haren da suka yi sanadin rasa rayukan jami'ai a jihohin Benuwai da Nasarawa. A cewar ƙwararre akan lamuran tsaro, Zagazola Makama, an kama wanda ake zargin ne ai suna Yongu Justine Makwagh daga Kadarko, Nasarawa da misalin ƙarfe 8 na daren Juma'a, a garejin Balcony Park da ke Makurɗi bayan tsawon watanni ana neman sa ruwa-a-jallo. Ya ce, an gudanar da atisayen kamen ne bayan samun wasu bayanan sirri ƙarƙashin DPOn yankin Daudu da haɗin-gwiwar jami'an leƙen asiri…
Read More

Babu juyin mulki a Ƙasar Benin, gwamnati na nan daram, inji Ministan Cikin Gida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Harkokin Cikin Gida na Ƙasar Jamhuriyar Benin, Alassane Seidou ya ce dakarun tsaron ƙasar sun yi nasarar daƙile yunƙurin kifar da gwamnati. An tabbatar da cewa yunkurin kifar da gwamnatin ƙasar Benin da wasu sojoji suka yi a safiyar Asabar ya ci tura, bayan dakarun gwamnati sun sake karɓe ikon cibiyoyin gwamnati da gidan talabijin na ƙasa. A safiyar ranar Asabar ne wani kwamanda, Pascal Tigri, tare da wasu runduna na sojoji, suka kutsa cikin gidan talabijin na ƙasar, inda suka gabatar da sanarwar cewa sun hambarar da Shugaba Patrice Talon, tare da…
Read More

Sojoji sun karɓe mulkin Jamhuriyar Benin a hannun Shugaba Talon

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Lahadi wata tawagar dakarun sojin ƙasar Jamhuriyar Benin ta sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon, wanda aka tsara zai sauka a karagar mulkin a watan Afrilu mai zuwa bayan shekaru 10 a kujerar. Sojojin, waɗanda ke kiran kansu da "Military Committee for Refoundation" (CMR), a wata kafar talabijin, sun ce sun tattauna a tsakaninsu inda suka cimma matsayar tsige shugaban ƙasar. A yanzu haka dai ba a san inda Shugaba Talon yake ba, sannan ofishin jakadancin Faransa kamar yadda ya wallafa ta kafar X, ya ce an jiyo harbe-harben bindiga…
Read More

‘Yan ƙabilar Igbo sun mamaye Abuja da Legas, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jinjina wa ƴan ƙabilar Igbo, inda ya bayyana su a matsayin waɗanda suka fi tasiri a harkokin al'amuran ƙasa da kasuwanci. Shettima ya faɗi haka ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata yayin taron masu ruwa da tsaki na tattali na Imo da aka gudanar a birnin Owerri. Ya ce, Inyamurai mutane ne da ke ƙoƙarin kutsa kai a kowane ɓangare na ƙasa don gudanar da harkokin kasuwanci da naman ilimi. Shettima ya bayyana cewa, ƴan ƙabilar sun taimaka wajen bada gagarumar gudumawa ga ci-gaban ƙasa don…
Read More

Akpabio ya musanta shigar da sabuwar ƙara akan Sanata Natasha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce bai shigar da wata sabuwar ƙara ba akan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. A wata sanarwa da mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Jackson Udom ya fitar, Akpabio ya bayyana cewa batun ya shigar da ƙarar neman biyan sa biliyan N200 akan Natasha ba gaskiya ba ne, abu ne da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al'umma. "Ikirarinta cewa an shigar da ƙarar, ba gaskiya ba ne, ruɗarwa ne, kuma da nufin rikita tunanin jama'a akan al'amarin", inji Udom a sanarwar, ranar Lahadi. Ya ce, an shigar da…
Read More