Babaji

5692 Posts

A shirye nake na gabatar da hujjata – Natasha kan ƙarar biliyan N200 da Akpabio ya shigar akanta

Sanatar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce ta shirya tsaf domin gabatar da shaidu a kotu bayan da Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya shigar da ita ƙarar biyan sa Naira biliyan 200 akan zargin ɓata masa suna. Akpabio na tuhumar Natasha ne bisa zargin ta masa laifin cin zarafi a bainar jama’a, lamarin da ta ce yanzu kotu za ta ba ta damar da majalisa ta ƙi bayarwa wajen sauraron ƙorafinta. An tsayar da ranar farko ta sauraron shari’ar a 21 Janairu 2026, kuma ana sa ran dukkan ɓangarorin biyu za su gabatar da hujjoji. A…
Read More

Cikakken jaddawalin wasannin Kofin Duniya na 2026

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a aka tabbatar tare da fitar rukuni guda 12 na wasannin gasar Kofin Duniya na 2026, wanda ƙasashen Amurka, Kanada da Mexico za su jagoranta. Za a gudanar da wasannin ne daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga Yulin shekarar, kamar yadda jaddawalinsu da aka fitar a Birnin Washington DC ya bayyana. Kimanin ƙasashe 48 ne za su fafata a gasar, wadda aka faɗaɗa a wannan karo inda masu masauƙin baƙi suke jagorantar rukunonin A, B da D. Ga jaddawalin rukuni 12 na ƙasashen kamar yadda Blueprint ta ruwaito: Group…
Read More

Yanzu-yanzu: Jirgin sojoji ya yi hatsari a Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin saman yaƙi na rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) ya yi hatsari a kusa da kauyen Karabonde da ke ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja, inda matuƙa biyu suka tsira daga cikin jirgin kafin ya kama da wuta. Wani mazaunin yankin ya shaida cewa jirgin ya tashi ne daga sansanin sojin sama na Kainji. Haka kuma al’ummar yankin sun ce abin ya faru ne misalin ƙarfe 4:10 na yamma, inda aka ga wutar da ta tashi daga wurin da jirgin ya faɗi. Wani shaida mai suna Lukman Sulaiman ya…
Read More

Ɓatanci: Akpabio ya shigar da ƙarar neman biyan sa biliyan N200 akan Natasha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya maka Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ƙara a kotu akan zargin ɓata masa suna, yana mai neman ta biya shi diyyar Naira biliyan 200. Sanata Natasha mai wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya, ta tabbatar da karɓar sammacin a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna jin daɗinta tana mai cewa ta samu damar bayyana hujjojinta akan zargin yunƙurin lalata da ta zarge shi da yi da ita a baya. "Yau 5 ga watan Disamban 2025, na karɓi sabon sammacin kotu kan ƙarar diyya ta naira biliyan 200 da Sanata Godswill…
Read More

Kano: An gargaɗi jagororin kasuwa a Bichi akan kiyaye jagoranci na gari

Alkalin Kotun Shari'ar Muslunci ta Ƙaramar Hukumar Bichi, Malam Mubarak Ado Abdullahi ne ya yi wannan jan hankalin a yayin da ƙungiyar ƴan kasuwa ta (Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited) ta kai masa ziyara a unguwar Buden Gari. Da yake jawabi, Mai Shari'a Mubarak Ado Abdullahi, ya nuna jin daɗin wannan ziyara mai dorar da hadin-kai. Mai Shariar wanda ya yaba wa ƙungiyar bisa ƙoƙarinta na daƙile dukkan wata ɓarna acikin kasuwar ya hore su da su zama masu sa ido game da abubuwan da ake sayarwa acikin kasuwar. Tun da fari shugaban 'yan kasuwar, Alhaji Abubakar Mazahimu Sale,…
Read More

An yaba wa Kwankwaso bisa zama ginshiƙin NNPP a Kano

An jinjina wa jagoran Kwankasiyya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso kan zama tushe na samar da gwamnatin alheri ga jama'ar Kano. A wata sanarwar da Jami'ar Yada Labarai ta Ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, Mataimakin Shugaban Hukumar Yawon Bude Idanu ta Jihar Kano, Alhaji Tijjani Aliyu ne ya yi jinjinar da godiya a yayin gudanar da taron zaɓen shugabanin Jam'iyyar NNPP na Bichi a Cibiyar Musulunci dake yankin. A jawabinsa, Alhaji Tijjani Aliyu, ya nuna jin daɗi game da zaman lafiya da haɗin kai da jam’iyyar tasu ta NNPP ta ciri tuta a kai, duba da irin…
Read More

Kano: An kwaɗaitar da ƴan kasuwar Bichi sanya dabarun zamani a harkokinsu

Shugaban Hukumar Raya Kogin Hadejia da Jama'are, Alhaji Rabi'u Sulaiman Bichi ya yi kira ga 'yan kasuwar Bichi a kan mai da hankali wajen shigo da dabarun kasuwancin zamani cikin harkokin kasuwancinsu. Ya bayyana haka, a yayin da kungiyar ƴan kasuwa ta (Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited) ta kai masa ziyara a ofishinsa dake jihar Kano. Da ya ke jawabi, Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi, ya nuna farin ciki da jin dadin wannan ziyara, inda ya bayyana hakan a matsayin hadin kan da zai samar da cigaba mai dorewa, ya kuma kara da shawartar su game da koyon hanyoyin lissafi…
Read More

Kano: Cibiyar Musulunci a Bichi ta jagoranci musabaƙar Alƙur’ani

Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, ta ƙaddamar da karatun musabaƙa na yara da matasa a Cibiyar Musulunci dake yankin. A sanarwar da Jami'ar Yada Labarai ta karamar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai, an ƙaddamar da kwamitin gasar ne domin zaburar da al'umma koyo da karatun musabakar karkashin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na jihar, don kwadaituwa da karanta Al-Kur'ani mai girma tare da aiki da shi a kodayaushe. Shugaban Kwamitin Musabakar na yankin, Malam Ibrahim Muhammad, ya bayyana Bichi tana cikin kananan hukumomin da aka fara gudanar da wannan gasa ta musabakar Kur'ani da…
Read More

Sama da mutane miliyan 1.4 sun amfana da shirin sufurin motocin kyauta na Kaduna a wata biyar – Kwamishina

Shirin sufuri na kyauta da gwamnatin Jihar Kaduna ke gudanarwa na amfani da motocin masu amfani da iskar Gas (CNG ) ya ɗauki fiye da fasinjoji miliyan 1.4 akan manyan hanyoyi guda huɗu tsakanin watan Yuli zuwa Nuwambar 2025, wanda ya adana wa mazauna jihar fiye da Naira biliyan 1.39 na kuɗin mota, kamar yadda rahotanni suka ruwaito. Yayin gabatar da bayanan ga manema labarai a Kaduna ranar Alhamis, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Ahmed Maiyaƙi, ya ce an gudanar da wannan tantancewar ne domin gano ainihin tasirin tsarin sufuri kyauta da Gwamna Uba Sani ya ƙaddamar, inda alkaluman suka nuna…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kakakin Majalisar Dokokin Ribas da wasu 15 sun koma APC

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas, Martin Amaewhule ya sauya sheƙa tare da wasu ƙarin mambobi 15 na Majalisar Dokokin jihar a yau Juma’a. Ana ganin hakan a matsayin abinda ya ƙara dagula harkokin siyasar jihar wadda ke fama da rikice-rikicen cikin gida tun watanni da dama da suka gabata. Rahotanni sun nuna cewa sauya sheƙar na da alaƙa da rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar. Wannan mataki ya mayar da adadin mambobin majalisar da suka koma jam’iyyar APC zuwa 16 gaba ɗaya. Sauya sheƙar ya faru ne a wani zama na musamman da majalisar ta yi inda mambobin suka bayyana…
Read More