Babaji

5692 Posts

Mallakar makami da sunan kare kai ba mafita ba ne ga rashin tsaro, inji Bishop Matthew Kukah

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban jagoran Kiristocin Sakkwato, Bishop Matthew Hassan Kukah, ya ce cigaba da mallakar makami ga al'ummar da ke rayuwa a wurare masu fama da rashin tsaro ba mafita ba ne ga matsalar rashin tsaro a Nijeriya. Bishop Kukah ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a Abuja yayin zaman tattauna muhimman al'amuran ƙasa da aka yi wa take da 'A Whole-of-Society Approach to Prevention of Violence and Conflict in Northern Nigeria'. Cibiyar kwamitin zaman lafiya ta Kukah da Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA) ne suka shirya zaman. Kalaman babban…
Read More

Kyaftin ɗin Super Eagles, Troost-Ekong ya yi murabus a hukumance

Kyaftin ɗin tawagar Super Eagles, William Troost-Ekong, ya sanar da yin ritaya daga taka wa Nijeriya tamola. Ekong mai shekara 32 ya sanar da matakin ne acikin wata sanarwa a shafukansa na sada zumunta kwana ɗaya bayan mai horarwa Eric Chelle ya zaɓe shi cikin tawagar farko ta ƴan wasan da za su wakilci Nijeriya a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2026. "Lokaci ya yi da zan miƙa damar, na miƙa ƙyallen kyaftin ɗin," inji shi. "A yau, ina sanar da yin ritaya daga taka leda a matakin ƙasa da ƙasa." Ekong bayan ya buga wa Super Eagles wasa 83…
Read More

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jaddada hukuncin haramta wa VIO ƙwacewa da sanya tara ga ababen hawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta jaddada hukuncin wata Babbar Kotun Tarayya da ke birnin tarayya, wanda ya haramta ta wa Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa da aka fi sani da VIO, dakatarwa, karɓewa ko ƙaƙaba tara ga masu motoci. A wani hukunci na tawagar alƙalai uku, kotun ta yanke hukuncin haramta ababe ukun da aka lissafo ga hukumar. Da yake gabatar da shari'ar, Mai Shari'a Oyejoju Oyewumi ya ce ɗaukaka ƙara akan batun ba shi da nagarta. Don haka ya yanke hukuncin tara ga ɓangaren da ya shigar da ƙarar (VIO) na…
Read More

Babu rikici tsakanina da Akpabio, aiki na kaɗai nake yi, inji Sanata Ɗanjuma Goje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Nijeriya, Ɗanjuma Goje ya bayyana cewa babu wani rikici a tsakaninsa da Shugaban majalisar, Godswill Akpabio bisa abinda ya faru a yayin zamansu na ranar Talata, yana mai bayyana al'amarin a matsayin wani ɓangare na ayyukansu. Goje ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar na ranar Laraba, wato kwana ɗaya bayan ya ƙalubalanci Akpabio bisa abin da ya kira da 'saɓa aikin majalisa'. Sanatan ya ce abinda ya yi yana kan doka, saidai wani sashi na ƴan jarida bai fahimci abinda yake nufi…
Read More

Rashin tsaro: NEC ta amince da biliyan N100 don gyaran cibiyoyin horon hukumomin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa (NEC) ta amince da ware Naira biliyan 100 a matsayin kuɗin gyaran cibiyoyin horon ƴan sanda da wasu hukumomin tsaro a Nijeriya. Hakan na na nufin har zuwa hukuncin da Shugaba Bola Tinubu zai yi a kai bisa la'akari da shawarwarin da kwamitin majalisar ya bayar na duba matakin wuraren horon aikin ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro a faɗin Nijeriya. A zamanta na 154 da aka gudanar a ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin Maitaimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, NEC ta kuma amince da Naira biliyan 2.6 na hidindimun shawarwari game…
Read More

Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta tabbatar da Janar Musa a matsayin Ministan Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa a matsayin sabon Babban Ministan Tsaron Nijeriya bayan shafe sa'o'i biyar a gaban ƴaƴanta a yau Laraba. Da fari, Sanata Sani Musa (Neja ta Gabas) ya roƙi majalisar da ta ƙyale Janar Musa ya yi gaisuwar ban girma sannan ya tafi bayan sun masa wasu ƴan tambayoyi. Saidai, wannan magiyar bata samu wuri ba domin kuwa waɗanda suka ƙi amincewa sun ce wajibi ne duk wanda aka bada sunansa a muƙamin minista, sai ya amsa karin wasu tambayoyi, lamarin…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: CBN ya ƙara adadin cirar kuɗi ga kwastomomin bankuna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sanar da wasu sauye-sauye ga tsarin cirar kuɗaɗe a bankuna, inda ya soke tsarin iyakance adadin waɗanda za a zuba da faɗaɗa adadin cirar kuɗi a kowane mako zuwa N500,000 daga N100,000 da ake bi a baya. An samu wannan jawabi ne a saƙon umarni da Daraktar tsare-tsaren kuɗaɗe da gudanarwa ta CBN, Dakta Rita Sike ta aike wa cibiyoyin kuɗi a Nijeriya, inda aka yi wa takardar taken 'Rivised Cash-Related Policies'. Ta bayyana cewa, CBN ya ɗauki matakin ne domin rage tsadar gudanar da tsabar kuɗi, daƙile barazanar…
Read More

Yau Majalisar Dattawa za ta tantance Janar Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Laraba ne Majalisar Dattawa za ta tantance tsohon Babban Hafsan Tsaron (CDS), wato Janar Christopher Musa Gwabin domin tabbatar da naɗinsa a matsayin ministan tsaro, bayan Shugaba Tinubu ya bada sunansa a jiya Talata. Shugaban mafiya rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya sanar da haka a wata takarda, inda ya bayyana matakin a matsayin abinda za a yi da nufin inganta harkokin tsaro da kariya ga rashin ɗorewa al'amuran ƙasa. An bada sunan Janar Musa ne ƙasa kwana ɗaya da tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus. Rahotanni sun…
Read More

Kungiyar masana zane-zane ta koka kan gobarar da ta lanƙwume Herwa Heart of Art Gallery

Sanannan wajen koyar da fasaha na Herwa Heart of Art Gallery, wacce ta shahara a matsayin babban cibiyar ƙirƙira kuma ta samu lambar yabo ta Outstanding Gallery Award daga Ƙungiyar Ɗaliban Zane-Zane ta Nijeriya (SNA), ta ƙone kurmus a ranar Juma’ar da ta gabata sakamakon abin da shaidun gani da ido suka bayyana a matsayin fashewar hasken rana kwatsam. Wannan lamari ya tayar da hankulan maƙota da ke yankin. Akan haka ne ƙungiyar SNA ta bayyana al'amarin a matsayin babban rashi ba ga ƴan ƙungiyar ba kaɗai har ma ga ɗalibai masu tasowa, asarar a matsayin babbar rashi ga masu…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu na ganawar sirri da jagororin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu yana halin ganawa da jagororin hukumomin tsaron Nijeriya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Olufemi Oluyede ne ya jagoranci tawagar a fadar. Sauran waɗanda suka samu halartar zaman sun haɗa da Shugaban sojojin ƙasa (COAS), Lt. Janar W. Shaibu; Shugaban Sojin Sama, CAS, Air Marshal Sunday Aneke; da Shugaban Sojin Ruwa, CNS, Vice Admiral I. Abbas. Haka kuma, akwai shugaban sashen leƙen asiri, CDI, Lt. Janar Emmanuel Undiandeye; Shugaban DSS, Adeola Ajayi, da Sufeto Janar na ƴan sanda, IGP, Kayode Egbetokun. Amma ba a samu…
Read More