02
Dec
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa Gwabin a matsayin sabon Ministan Tsaro. Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a yau Talata. Onanuga ya ce, a wata wasiƙa zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya miƙa sunan tsohon Babban Hafsan Tsaron na Nijeriya (CDS) a matsayin wanda zai gaji Alhaji Mohammed Badaru a muƙamin, wanda ya yi murabus a jiya Litinin. Janar Musa mai shekaru 58, ya riƙe muƙamin CDS daga shekarar 2023 zuwa watan Oktoban 2025. Ya kuma taɓa samun…
