01
Dec
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su taimaka mata wajen sanya ido akan kiyaye umarnin Shugaba Bola Tinubu na janye ƴan sanda daga gadin manyan mutane. Mai ba Shugaban Ƙasa shawara akan harkar yaɗa labarai, Daniel Bwala ya yi wannan magiyar a wata hira da gidan talabijin na TVC a jiya Lahadi, inda ya bayyana ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya take yi wajen ganin an kiyaye umarnin Shugaban ƙasar, yana mai kira ga jama'a da su ruwaito duk wanda aka samu da saɓa wa hakan ta hanyar ɗaukar hoto ko bidiyon…
