Babaji

5693 Posts

An yi garkuwa da mutane da dama yayin farmakin ƴan bindiga a Kogi

Dafa BELLO A. BABAJI a Abuja Mutane da dama ne aka yi awon-gaba da su a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a yankin Isanlu Makutu zuwa Idofin da ke Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas a Jihar Kogi. A cewar ShaharaReporters, shaidu sun ce maharan sun kutsa yankin ne da tsakar rana a yau Asabar, lamarin da ya sa mutane firgita tare da gudun tsira domin neman mafaka. Saidai har ƴan bindigar suka tafi, ba a san iya adadin mutanen da suka kwashe ba. Majiyoyi daga yankin sun ce al'amarin ya tayar da hankalin al’umma domin hatta a…
Read More

Pafaroma ya cire takalmi yayin shiga masallaci a Turkiyya

Shugaban Fadar Vatican, Pafaroma Leo na 14 ya ziyarci Masallacin Sultanahmet da ke ƙasar Turkiyya a yau Asabar, inda shiga babu takalmi a ƙafarsa. Sultanahmet masallaci ne mai tarihi da ke birnin Istanbul a matsayin wani ɓangare na ziyararsa a hukumance zuwa Turkiyya. Fafaroman ya iso Turkiyyar ne tun a ranar 27 ga Nuwamba a ziyararsa ta farko zuwa ƙasar waje bayan Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya gayyace shi. Hakan na nufin Pafaroman ya cire takalmansa kamar yadda Musulmai ke yi kafin shiga masallaci domin yin salla. Aƙalla ya shafe mintina 15 aciki tare da jagororin musulmi inda suka kewaya…
Read More

Femi Fani-Kayode, tsohon Shugaban INEC Yakubu, Reno Omokri da wasu 29 sun shiga jaddawalin jakadun Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya miƙa sabon jaddawalin mutane 32 da za a ba su muƙaman jakadanci ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da kuma tabbatarwa. An ruwaito cewa shugaban ƙasar ya yi aiken buƙatar ne a takardu guda biyu zuwa ga Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio. A sanarwar da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya nemi majalisar da ta yi nazarin tabbatarwa akan wasu ƙwararru a fannin guda 15 da waɗanda basu da ƙwarewa su 17 domin wakiltar Nijeriya a manyan ofisoshin jakadancin a ƙasashen duniya. Sunayen manyan ƴan siyasa da tsofaffin jami'an…
Read More

MOPPAN ta jajenta rasuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa MOPPAN, ta yi alhinin rashin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis. A wata takarda daga Shugabanta, Shehu Hassan Kano, MOPPAN ta ce a madadin mambobinta, tana miƙa ta'aziyyarta ga iyalai, ƴan uwa, ɗalibansa da ɗaukacin al'ummar Musulmi bisa rashin marigayin. MOPPAN ta bayyana cewa, rashin shehin malamin ya haifar da babban giɓi ga al'ummar musulmi musamman ƴan Ɗarikar Tijjaniya duba da hidimarsa ta koyar da addinin Musulunci da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya acikin al'umma. Ƙungiyar ta kuma ce,…
Read More

EFCC ta sallami Malami bayan gudanar da bincike akansa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta sallami tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami sa'o'i kaɗan bayan amsa gayyatar ta yi masa. Malami (SAN), ya bayyana haka ta kafar Facebook inda ya ce, EFCC ta sallame shi, bayan ya amsa wasu tambayoyi da take neman amsarsu daga gare shi. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jim kaɗan bayan fitowa daga ofishin hukumar, Malami ya ce, yana gode wa Allah da ya ba shi ikon kammala amsa tambayoyin hukumar lafiya. Ya kuma ce, ganawar tasa da jami'an EFCC ta…
Read More

Za a rataye ɗalibin Jami’ar UNIPORT kan halaka budurwarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Jihar Ribas da ke zaune a Fatakwal, ta yanke wa wani ɗan ajin ƙarshe na Jami'ar jihar (UNIPORT) mai suna Damian Okoligwe, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifin halaka budurwarsa, Justina Otuene. An samu Okoligwe ne da laifin kisan Otuene a ranar 20 ga watan Oktoban 2023 a gidansa da ke Mgbuoba a Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor da ke jihar. Bayan haka ne sai kuma ya daddatsa gangar jikinta, sannan ya zuba ta a baro da nufin zubarwa a matsayin shara, inda a yayin haka ne aka cafke shi.…
Read More

Haihata-haihata ni da makaranta – Ɗalibin da ya kuɓuta bayan garkuwa da ƴan makarantar Neja ya faɗi halin da ya tsinci kansa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani ɗalibi mai suna Stephen Samuel mai shekaru 13, wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a makarantar St Mary's Catholic School, Papiri ta Karamar Hukumar Agwaran Jihar Neja, ya bayyana halin da ya tsinci kansa a ciki bayan ya samu tsira, inda ya ce yana ganin shi da makaranta har abada. Da yake magana yayin hira da jaridar Reuters, Samuel ya bayyana cewa ƴan bindigar sun far musu da tsakar dare a lokacin da suke barci, inda suka tashe su tare da umartar su da su kwanta. A lokacin…
Read More

ECOWAS ta dakatar da Guinea-Bissau kan juyin mulki

Ƙungiyar Tattalin Arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, ta dakatar da ƙasar Guinea-Bissau daga dukkan fannonin aiwatar da shawararta bayan juyin mulkin da ya hambarar da Shugaba Umaro Sissoco Embaló. Sanarwar ta fito ne bayan taron gaggawa da shugabannin ƙasashen suka gudanar, inda suka yi Allah-wadai da juyin mulkin tare da bukatar a mayar da mulki kan tsarin dimokuraɗiyya ba tare da wani sharadi ba. Kungiyar ta yi kira da a saki Shugaba Embaló da sauran jami’an zaɓe da ke tsare, sannan ta dage cewa dole ne a ba Hukumar Zaɓe damar bayyana sakamakon zaɓen 23 ga Nuwamba ba tare…
Read More

Ƙungiyar AU ta dakatar da Guinea-Bissau kan juyin mulki

Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), ta dakatar da ƙasar Guinea-Bissau daga zama memba, sakamakon kifar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissico-Embalo da dakarun sojoji suka yi a makon da ya gabata. Shugaban ƙungiyar, Mahamoud Youssouf, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Juma’a. Wannan matakin na AU ya biyo bayan ƙararrawar da ECOWAS ta ɗauka a sa’o’i kafin haka, inda ita ma ta sanar da dakatar da Guinea-Bissau daga yalwar ayyukanta, bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar. An gudanar da juyin mulkin ne yayin da ake cigaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, wanda manyan ƴan takarar kujerar…
Read More

Katsina: Kwamandan ƴan bindiga ya sako mutane 37 da aka yi garkuwa da su

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen jagoran ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa ya sako mutane 37 da aka yi garkuwa da su, waɗanda ke komarsa a Ƙaramar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina. A cewar rahoton Zagazola Makama, ƙwararre mai sharhi kan lamuran tsaro, mutanen, waɗanda galibinsu maza da mata ne, an yi awon-gaba da su a hare-hare da aka ƙaddamar a wasu ƙauyuka, inda aka sako su a ranar Laraba bayan kwanaki da dama a hannun ƴan bindiga. Hakan na zuwa ne bayan makonni ana tattaunawa wanda ya kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya, kamar yadda ɗan majalisa…
Read More