Babaji

5693 Posts

Rashin tsaro: ‘Yan Nijeriya na da ƴancin neman ɗauki daga ƙasashen waje, inji Obasanjo

Tsohon Shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce ƴan Nijeriya suna da cikakken ƴancin neman taimakon ƙasashen waje idan gwamnatin ƙasar ta gaza kare rayukansu. Obasanjo ya yi jawabin ne a wani taron Kirsimeti a Jos, inda ya ce bai kamata a ji kunyar neman taimako ba idan gwamnati ta kasa cika babban nauyinta na tsaro. Tashar talabijin ta Channels ta ruwaito cewa Obasanjo ya ce a zamanin da ake amfani da tauraron ɗan-adam da jiragen sintiri, bai kamata ƴan ta’adda su riƙa kashe mutane su bace ba. Ya zargi gwamnati da gazawa, inda ya ce hare-hare da kashe-kashe sun…
Read More

Karɓe mulki da sojoji suka yi a Guinea-Bissau ya tada min hankali, inji Jonathan

Tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana cewa abin da ya faru a Guinea-Bissau ba juyin mulki ba ne duk da cewa ya janyo ruɗani da tashin hankali a fadin ƙasar. Jonathan ya ce, al'amarin ya taɓa shi matuƙa fiye da ranar da ya kira marigayi Muhammadu Buhari domin taya shi murnar nasarar zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2015. Tsohon shugaban ƙasar ya kasance a Guinea-Bissau ne a lokacin a matsayin shugaban tawagar West African Elders Forum da ke sa ido kan zabukan kasar, lokacin da aka ruwaito juyin mulki. Saboda fargabar tsaro da tashin hankali, daga baya ya…
Read More

DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed bisa kalaman tunzura

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta gayyaci Yusuf Datti Baba-Ahmed, wanda tsohon abokin tafiyar Peter Obi ne a zaɓen 2023. Baba-Ahmed, wanda kuma shi ya samar da Jami'ar Baze da ke Abuja, a cewar wata majiyar tsaro, an gayyace shi ne a jiya Juma'a da dare bisa zargin sa da yin waɗansu kalamai na tunzura jama'a akan Nijeriya. An gano cewa DSS tana sanya ido akan kalaman Baba-Ahmed da aka baza su a kafafen watsa labarai musamman na ikirarin abinda ya kira da "rikicin dokokin ƙasa". Majiyar ta ce:…
Read More

Ya aka yanke wa Kanu ɗaurin rai da rai amma ɗan Ansaru shekara 20? – Bello El-Rufa’i

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa kuma ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, wato Bello El-Rufai, ya ƙalubalanci tsarin shari’a a Nijeriya inda ya yi kira da ƙara ƙaimi wajen tabbatar da kiyaye gaskiya da adalci a fannin. Bello ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar inda ya soki hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga Nnamdi Kanu yayin da kuma aka yanke hukuncin shekara 20 ga jagoran ƴan ta'addan Ansaru mai suna Husseini Ismail da ya jagoranci ayyukan ta'addanci daban-daban. Kalaman ɗan majalisar sun haddasa muhawara mai zafi a faɗin ƙasa bayan…
Read More

Zan yi murabus matuƙar Tinubu ya faɗi a zaɓen 2027, inji Gwamna Okpebholo na Edo

Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ce a shirye yake ya yi murabus daga muƙaminsa matuƙar Shugaba Bola Tinubu ya gaza lashe jiharsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Okpebholo ya lura cewa jam’iyyar APC a yanzu ta mamaye siyasar jihar Edo gaba ɗaya, kuma ba ta fuskantar wata adawa gabanin babban zaɓen mai zuwa, wanda ake sa rana gudanarwa nan da watanni 15. Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na AIT, Okpebholo ya ce Tinubu na da goyon baya mafi rinjaye a Edo don haka yake fatan shugaban ƙasar ya lashe zaɓen da ƙuri'a mai yawa.…
Read More

Lakurawa sun halaka jami’an shige da fice uku a Kebbi

Rahotanni daga Jihar Kebbi sun tabbatar da mutuwar jami'an hukumar shige-da-fice su guda uku sakamakon wani hari da mayaƙan Lakurawa suka kai kan gidajen kwanansu da ke yankin shingen bincike. A jiya Alhamis da dare aka kai harin a ƙauyen Bakin ruwa na Ƙaramar Hukumar Bagudo da ke da iyaka da Jamhuriyar Benin. Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin gida na jihar, Haliru Aliyu Wasagu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ƴan bindigar sun cinna wa gidajen ma'aikatan wuta ne cikin daren, sannan bayan sun fito daga gidan kuma suka harbe su har aka kashe 3 tare da jikkata…
Read More

‘Yan sanda sun musanta janye jami’an tsaron Atiku, Wike da wasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda ta musanta rahoton da ake yaɗawa akan janye jami'an tsaron wasu manyan mutane a Nijeriya. A wani saƙo da ta wallafa ta kafar X a yau Juma'a, rundunar, ta baki kakakinta Benjamin Hundeyin, ta ce rahoton, wanda aka yi zargin CSP Abdullahi Sulaiman da aka bayyana daga sashen gudanarwa ne yake ya sanya wa hannu, ba gaskiya ba ne kuma abu ne da ake yaɗawa da nufin ruɗar da al'umma. Waɗanda aka lissafo sun haɗa da : Atiku Abubakar, Namadi Sambo, Nyesom Wike, Aisha Buhari, Justice Kudirat Olatokunbo Kekere-Ekun, HRM Ogiame…
Read More

Gwamnatin Kaduna ta ayyana Asabar ta ƙarshen kowane wata a matsayin ranar tsaftar muhalli

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana Asabar ta ƙarshen kowane wata a matsayin ranar Tsaftar muhalli a jihar a wani mataki da ta ce za a yi amfani da shi wajen ƙarfafa tsafta, kare lafiyar jama’a da kuma rage barazanar da ke fitowa daga rashin tsafta a faɗin jihar. A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya fitar, an bayyana cewa aikin tsaftar na farko zai gudana ne a Asabar, 29 ga Nuwamba, 2025, daga ƙarfe 7:00 na safe zuwa 10:00 na safe. Da yake jawabi, Kwamishinan Muhalli na jihar, Abubakar Buba, ya bayyana wannan shiri a…
Read More

Mikel Obi na harin aikin shugabancin NFF

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Bayan da Super Eagles ta gaza nasarar shiga gasar Kofin Duniya na 2026 karo biyu a jere, tsohon wasan tsakiya ma Nijeriya da ƙungiyar Chelsea, John Obi Mikel ya bayyana aniyarsa ta karɓar jagorancin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta ƙasa (NFF). Tsohon kyaftin ɗin na Super Eagles ya ce shigarsa harkokin ƙwallon Nijeriyar za ta taimaka wajen tabbatar da gaskiya da adalci tare da kauce wa dukkan ayyukan da suka shafi rashawa a hukumar. Ya bayyana cewa, wajibi ne a sanya koma a gurbinsa tare da yaƙar duk wata hanya da za ra bada damar…
Read More

A rage ayyukan Majalisar Dokoki don ƙarfafa tsaro – Ndume ga Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya nemi a rage wasu ayyukan gwamnati ciki har da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin wata hanya ta rage adadin kuɗaɗen da gwamnati take kashewa domin ƙarfafa ayyana fannin daƙile ta'addanci ta fuskar kuɗi a Nijeriya. A wata hira da Channels Television da ya yi ranar Alhamis, Ndume ya ce nauyin kuɗin gudanar da Majalisar Dattawa a tsarin cikakken lokaci ba zai ɗore ba, musamman a wannan lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin kuɗi da tsaro. Ya ce, “kudin gudanar da gwamnati…
Read More