Babaji

5693 Posts

Lamiɗo ya nemi a kafa kwamitin riƙo don tafiyar da harkokin PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Sule Lamido, ya bayar da wa'adin kwanaki goma ga jam'iyyar na ta magance magance rikicin cikin gida da ya dabaibaye ta kuma yake ƙoƙarin dagula al'amuran siyasarta. Ya kuma yi kira da a rusa zaɓen Ibadan da aka yi a babban taron jam'iyyar na kwanan nan tare da kafa kwamitin riƙo na ƙasa a nan take. Lamiɗo ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga magoya bayansa ciki har da tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi, tsoffin kwamishinoni, da sauran ƴan siyasa, wadanda suka kai masa…
Read More

Jonathan ya dawo Nijeriya bayan karɓe mulkin Guinea-Bissau ya rutsa da shi a ƙasar

A yammacin jiya Alhamis ne tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya koma Abuja bayan an ɗauko shi daga Guinea-Bissau sakamakon karɓe mulkin ƙasar da sojoji suka yi, inda ya sauka a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayya Abuja. Hotunan faifan bidiyo na isowarsa, wanda kafar yada labarai ta ARISE ta yada, ya nuna Jonathan yana saukowa daga matakalar jirgin gwamnatin Guinea-Bissau cikin dare, inda ya samu tarba daga dimbin magoya baya da jami'ai. Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban tawagar dattawan Afrika ta Yamma don sa ido kan zaben shugaban kasa da na 'yan…
Read More

Gwamnan Kano ya ci alwashin goyon bayan dokar ta-ɓacin tsaro ta Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cikakken goyon bayansa ga dokar ta-ɓaci akan lamuran tsaro da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a ƴan kwanakin bisa la'akari da ƙamarin taɓarɓarewar harkokin tsaro a sassan Nijeriya. Ya ce, lokaci ya yi da za a ƙara matsa ƙaimi wajen murƙushe ƴan fashi da masu garkuwa da mutane. Ya bayyana cewa Kano za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare al’umma, musamman yankunan iyaka da suka fuskanci hare-hare kwanan nan, inda aka sace mutane tare da tayar da hankulan jama’a. Gwamnan ya tabbatar…
Read More

EFCC ta gayyaci tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC), ta gayyaci tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami, (SAN). A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, Malami ya ce hukumar ta gayyace shi ne domin ya yi bayani akan wasu abubuwa da bai bayyana ba inda ya bada tabbacin girmama gayyatar. "A matsayina na ɗan ƙasa mai bin doka da oda kuma mai kishin ƙasa, na kuduri aniyar girmama wannan gayyata. Na yi imani da muhimmancin gaskiya, riƙon amana da kuma rike gaskiya a harkokin mulki — waɗannan ƙa’idoji ne da na dade ina goyon baya tare da tsayawa a kai,…
Read More

Gwamnonin Arewa sun jajenta rasuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana kaɗuwarsa bisa rashin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jagoran Ɗarikar Tijjaniya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda a ya rasu a ranar Laraba. Gwamnan a wata takarda daga mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Isma'ila Uba Misilli, ranar Alhamis, ya bayyana marigayin shehin malamin a matsayin magabaci na daban, wanda rayuwa da karantarwarsa ta yi tasiri akan miliyoyin al'umma. Ya ce, marigayin ya sadaukar da kansa wajen yaɗa addinin Musulunci musamman duba da yadda ya shahara da karantar da Alƙur'ani…
Read More

El-Rufa’i ya koma ADC a hukumance

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya koma jam’iyyar ADC a hukumance ta hanyar ansar katin jam’iyyar. Nasir El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC ne jim kaɗan bayan baban zaɓe na ƙasa na shekarar 2023, inda ya koma jam’iyyar SDP, wanda daga bisani kuma ya fice daga jam’iyyar. A yanzu a iya cewa sun haɗe da tsohon mataimakin ƙasa kuma kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar. Komawar El-Rufai ADC a hukumance wani mataki ne da ake ganin zai kawo sabon salo a siyasar adawa wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027.…
Read More

Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya bayyana kaɗuwarsa akan rasuwar babban malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a daren Laraba wayewar yau Alhamis. Tinubu ya ce, samun labarin ya sanya shi cikin kaɗuwa matuƙa, yana mai bayyana jagoran na Ɗarikar Tijjaniya a matsayin mutum mai daraja da ƙima. Haka kuma, ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa musamman Alƙur'ani mai girma. Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa rasuwar shehin malamin rashi ne ga Nijeriya baki ɗaya, ba ga iyalai da ɗalibai ko mabiyansa kaɗai ba.…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji sun yi wa Jonathan rakiya yayin fita Guinea-Bissau

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya samu rakiyar jami'an sojoji a lokacin da yake ficewa daga cikin ƙasar Guinea-Bissau, a yayin da ake cigaba da zaman ɗar-ɗar bayan sojoji sun karɓe mulkin ƙasar. Da fari an ruwaito cewa Jonathan yana ɗaya daga cikin jagororin Afirka da juyin mulkin ƙasar ya rutsa da su. An zaɓi tsohon shugaban ne domin ya shiga sahun mutane 36 masu sanya ido a zaɓen shugaban ƙasa a Guinea-Bissau ƙarƙashin haɗakar AU, ECOWAS da WAEF. Saidai, zuwa jiya Laraba rundunar sojoji ta sanar da karɓe iko da mulkin ƙasar…
Read More

Nan ba da jimawa ba za a sako ƴan makarantar Neja da aka sace, inji Shugaban APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawa Yiltwatda ya ce nan ba da jimawa ba za a sako ɗalibai da malaman makarantar St. Mary's Catholic Primary and Secondary School, Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara a Jihar Neja da aka yi awon-gaba da su a ranar Juma’ar da ta gabata. Yiltwatda ya bada tabbacin hakan ne a lokacin da ya jagoranci kwamitin ayyukan (NWC) jam'iyyar zuwa ziyarar ƙarfafa gwiwa ga Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) reshen jihar Neja a jiya Laraba. Ya ce, APC tana tare da iyalan waɗanda abin ya shafa, al'ummar Kiristoci da…
Read More

Yanzu-yanzu: Sheikh Ɗahiru Bauchi ya rasu bayan shafe shekaru 100 a duniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗaya daga cikin sanannun malaman addinin Musulunci a Nijeriya kuma jagoran Ɗarikar Tijjaniya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya rasu bayan shafe shekaru 100 a duniya. Rahotanni sun bayyana cewa, fitaccen malamin ya rasu ne a daren Laraba wayewar Alhamis, lamarin da ya kawo ƙarshen jagorancinsa na miliyoyin al'umma a Nijeriya da ma ƙasashen waje. A ranar 28 ga watan Junin 1927 aka haifi shehin malamin a Garin Nafaɗa da ke da tsohuwar jihar Bauchi, wanda a yanzu kuma yake cikin Jihar Gombe. Ya sadaukar da tsawon zangon rayuwarsa wajen karantarwa musamman Al-ƙur'ani, jagorancin ɓangarorin…
Read More