20
Nov
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta tabbatar da aikata laifukan ta'addanci akan tsararren jagoran ƙungiyar ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), Nnamdi Kanu, wanda aka shigar da tuhume-tuhumensu akansa a gabanta. Da yake gabatar da hukunci akan shari'ar, Alƙali James Omotosho ya tabbatar da tuhuma guda uku da masu ƙara suka shigar akan Kanu tun farkon lokacin da aka maka shi a kotu. Ya ce, barazanar tashin-tashina da Kanu ya yi a wani faifan bidiyo ya haddasa fargaba da shiga ƙunci ga al'umma a yankin Kudu maso Gabas, lamarin da ya ƙarfafa zarge-zargen…
