Babaji

5693 Posts

Rashin tsaro: Gwamnatin Tarayya ta umarci a rufe makarantun haɗaka 41

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta sanar da umarnin rufe makarantunta na sakandare na kwalejojin tarayya da ake kira da 'Unity Colleges' da ke sassan arewacin Nijeriya. A sanarwar da Ma'aikatar Ilimi ta fitar a ranar Juma'a daga Daraktar makarantun sakandare, Binta Abdulqadir a madadin Ministan Ilimi, Tunji Alausa, gwamnatin ta sanar a rufe kwalejojin guda 41 a faɗin Nijeriya. Sanarwar ta ce, ma'aikatar ta ɗauki wannan matakin ne saboda barazanar tsaro da ake fuskanta a sassan ƙasar, da kuma yunƙurin daƙile afkawa cikin wata matsala. Sanarwar ta kuma umarci shugabannin makarantun su tabbatar an aiwatar da…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa jami’o’i bada digirin girmamawa ga jami’an gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta sanar da haramta bai wa dukkan wani jami’in gwamnati mai riƙe da muƙami digirin girmamawa a ƙoƙarinta na daƙile yawan saɓa wa ƙa’ida wajen bayar da irin shaidar. Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ce ta bayyana hakan, inda ta ce ta ɗauki matakin ne bayan samun rahotanni masu tayar da hankali game da yadda ake bayar da digirin girmamawa barkatai da amfani da su ta hanyoyin da ba su dace ba. Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu ne ya bayyana hakan a Abuja, jim kadan bayan karbar rahoton kwamitin bincike kan yadda ake bayarwa da…
Read More

‘Yan matan Kebbi: Gwamna Idris na ƙalubalantar dalilin sojoji na barin makarantar dab da garkuwar

Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya nuna damuwa kan janyewar jami’an tsaro mintuna kaɗan kafin ƴan bindiga su kai hari su sace ‘yan mata 25 a makarantar Maga ta Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu da ke jihar. Ya bayyana cewa gwamnati ta samu bayanan leƙen asiri daga hukumar tsaro ta DSS, lamarin da ya sa aka tura ƙarin jami'an tsaro zuwa makarantar. Gwamnan ya ce, sojoji sun janye da misalin 3:00am, sannan ’yan bindiga suka kai hari 45 mintuna bayan haka. Ya kuma yi kira ga rundunar sojoji da ta yi binciki akan musabbabin janye jami’an tare da ɗaukar matakan da…
Read More

Tinubu ya taya Ribaɗu murnar cika shekaru 65

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya taya murna ga Mai bada Shawara na Ƙasa akan Harkokin Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribaɗu bisa cikarsa shekaru 65 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan mutanen da suka samar da gyara a Nijeriya bisa la’akari da gagarumar gudumawarsa ga ci-gaban ƙasa. Ribaɗu, wanda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ne kuma shugaba na farko a Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC), a yau 21 ga watan Nuwamba, 2025 ya ke bikin zagayowar ranar haihuwarsa. A wani saƙon taya murna daga Kakakin Shugaban…
Read More

Pafaroma ya ƙaryata zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya ce ta’addanci na kan kowane addini

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Pafaroma Leo na 14 (XIV), ya yi watsi da ikirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a taɓarɓarewar harkokin tsaron Nijeriya, inda ya ce al'amarin ya shafi Kiristoci, Musulmai da yankuna da dama na ƙasar. Jagoran addinin ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da ya ke ganawa da ƴan jarida da yake barin gidansa na Castel Gandolfo da ke Vatican a ƙasar Italiya. Ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi amsa tambaya game da halin tsaron da al'ummar Kiristocin Nijeriya ke ciki, yana mai cewa al'amarin ta'addanci a ƙasar…
Read More

‘Yan matan Kebbi: Tinubu ya umarci Matawalle ya koma Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya gaggauta ƙaura zuwa Jihar Kebbi domin jagorantar yadda za a ceto ɗalibai ƴan mata guda 25 da aka yi garkuwa da su a farkon wannan makon. A safiyar ranar Litinin ne rahotanni suka bayyana cewa ƴan bindiga sun kutsa makarantar mata ta Government Girls' Secondary School, Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu na jihar da misalin ƙarfe 4, inda suka yi awon-gaba da ɗaliban. Tinubu ya bayar da umarnin ne ta bakin Kakakinsa Bayo Onanuga a ranar Alhamis. Ya ce, Ministan zai cigaba…
Read More

‘Yan matan Kebbi: Tinubu na tare da ku a halin jimami – Shettima ga iyayen ɗaliban

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya tabbatar wa iyaye da iyalan ɗalibai mata da aka yi awon-gaba da su a makarantar Government Girls' Comprehensive Secondary School, Maga, Jihar Kebbi cewa gwamnati za ta yi dukkan abinda ya dace wajen ganin an ceto ƴaƴansu. Haka kuma, ya ce Shugaba Bola Tinubu yana cikin jimami game da faruwar al'amarin mai ban takaici, lamarin da ya sa ya ɗage tafiyarsa ziyarar aiki zuwa ƙasashen waje. Shettima ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Birnin Kebbi bisa umarnin Shugaba Tinubu, yana mai cewa sace yaran bala'i ne…
Read More

Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi riƙa haɗa hannu wajen kare ƴancin yara a Nijeriya

Mai Kula da Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, ya yi kira da a yi aiki tare domin kare ‘yancin da makomar yaran Najeriya. Ya bayyana haka a yau, wajen bikin tunawa da Ranar Yara ta Duniya an Abuja. Ya fara da cewa: “Taron yau yana da muhimmanci a gare ni. Na shafe shekaru da dama a aikina a matsayin ma’aikacin UNICEF da kuma wakilin UNICEF a ƙasashe daban-daban, ina aiki tare da yara, iyalai, malamai, ma’aikatan lafiya, da al’umma. Na shaida yadda dama guda kaɗai za ta iya sauya gaba ɗaya tafiyar rayuwar yaro. Saboda…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai-da-rai

Mai Shari'a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan da masu gabatar da ƙara suka tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi masa. Tuhume-tuhumen da aka yi wa Kanu sun haɗa da ta'addanci da tunzura jama'a su kashe ƴan sanda da tayar da zaune-tsaye. Haka kuma, ya yanke masa hukuncin zaman gidan kurkuku na tsawon shekaru 20 da shekaru biyar na laifuka bakwai ba tare da zaɓin biyan tara ba. Hakan na zuwa ne bayan tsawon lokaci ana tsare da jagoran na ƴan ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafaran…
Read More

Sakacin jami’an tsaro na da nasaba da garkuwa da ƴan makarantar Maga, inji Gwamnan Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya ce awon-gaba da ɗaliban makarantar sakandaren mata ta Maga a jihar, yana da nasaba da sakacin jami'an tsaro bayan samun bayanin cewa akwai yiyuwar a kai farmaki a makarantar. Rahoton wata jaridar yanar gizo ta 'Pointblanknews' ta wallafa cewa gwamna Malam Nasir Idris bayan ya isa makarantar da yammacin ranar litinin, inda ya bayyana cewa akwai jami'an tsaro da ke yi wa gwamnatinsa zagon-ƙasa duk da irin ƙoƙarin da yake yi kan harkar tsaro. Ya ƙara da cewa bayan samun bayanan sirri daga hukumar jami'an tsaro na…
Read More