Babaji

5693 Posts

Newcastle ta hana Haaland zura ƙwallon Premier League na 100 bayan doke City

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙoƙarin Erling Haaland na zura ƙwallon Premier League a Manchester City na 100 ya ci tura bayan da Newcastle United ta doke su da ci 2 da 1. Haian ya sa City ta gaza rage adadin makin ratar da ke tsakanin ta da ta ɗaya a teburin, wato ƙungiyar Arsenal. Da fari, Newcastle ce ta fara zura ƙwallo a ranar City ta ɗan wasa Harvey Barnes a minti na 63. Saidai, nasarar ta samu ne na tsawon mintina biyar a lokacin da City ta farke ta hannun ɗan wasa Rúben Dias a minti na…
Read More

An rufe makarantun kwana a Yobe kan rashin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ƙoƙarinta na ɗaukar matakan kariya game da al'amarin taɓarɓarewar tsaro, Gwamnatin Yobe ta umarci a rufe dukkan makarantun sakandare na kwana da ke sassan jihar. Darakta Janar na harkokin yaɗa labaran Gwamna Mai Mala Buni, wato Mamman Mohammed ya sanar da haka a wata takarda, jiya Asabar. Ya ce, gwamnati ta ɗauki matakin ne bayan ganawa tsakanin gwamnan da jagororin hukumomin tsaro a jihar. A cewar sanarwar, Gwamna Buni shi ya jagoranci zaman, wanda aka yi nazari akan matsalolin tsaro da suka shafi sassan ƙasar a ƴan kwanakin nan. Ya bayyana cewa, gwamnatin…
Read More

Yadda Gwamnatin Kano ke tallafa wa mata a Ƙaramar Hukumar Bichi

Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da shirin bai wa mata jari a sakatariyar ƙaramar hukumar. Manufar shirin dai ita ce, taimaka wa mata marasa karfi akan don tsayawa bisa gwadaben neman na kansu ta hanyar rage barace-barace a cikin al'umma da kuma bunƙasa tattalin arziƙinsu. Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata tare da mata kimanin dari da suka amfana da jarin dubu hamsin-hamsin a yankin, sun gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kokarinsa na hidimtawa al'umar Kano ta kowane fanni. "Mun gode, an ba…
Read More

Kano: Salon da Bichi ta ɗauka wajen rajistar haihuwa a ƙaramar hukumar

A ƙoƙarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ganin al'ummar jihar Kano sun mayar da hankali wajen yin rijistar haihuwa, musamman ga yara kasa da shekara ɗaya da ake ci gaba da yi a fadin kasar nan, Karamar Hukumar Bichi ta duƙufa don tabbatar da wannan ƙudirin. A Mazabar Fagolo, Bashir Abdullahi Usman, ya ce, bayan kammala bita da aka yi musu, aikin ya tafi yadda yakamata inda suka samu damar yi wa yara talatin rijistar ta hanyar bi gida-gida, amma sakamakon matsalar rashin network ya kawo tsaikon aikin a yanzu, sun kuma sanar da na gaba a gyara domin cigaba…
Read More

Hajiya Rahmatu: Matar sanannen sarki ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hajiya Rahmatu Awwal Ibrahim, matar Mai Martaba Sarkin Suleja, Malam Muhammad Awwal Ibrahim, ta rasu bayan fama da wani dogo rashin lafiya. Sakataren Gwamnatin jihar Neja (SSG), Alhaji Abubakar Usman ya sanar da rasuwarta a wata takarda, ranar Alhamis. Ya bayyana rashin marigayiyar a matsayin abin baƙin ciki ga Masarautar Suleja da ma jihar Neja baki ɗaya. Ya kuma yaba mata bisa sadaukarwarta a matsayinta na uwa kuma jigon al'umma wadda hidimarta ta inganta rayukan jama'a da dama. Haka kuma ya jinjina wa ƙoƙarinta ga fannin ilimi musamman wajen zama shugabar makarantar Rahama School,…
Read More

NDLEA ta kama hodar iblis da mutane 20 a jirgin ruwan Brazil

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), ta yi nasarar kama kilogram 20 na hodar iblis da aka yi jigilarta daga ƙasar Brazil inda ta kuma tsare ma'aikatan jirgin ruwa guda 20 na Filipino. Jami'an NDLEA sun sake kama wani jirgin ruwa da ke ɗauke da kayayyaki - MV Nord Bosporus mai lamba 9760110 daga tashar jiragen ruwa ta Santos da ke Brazil a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas tare da aƙalla kilogiram 20 na maganin Class A da aka binne a ƙarƙashin kayansa. Sun gano haramtaccen maganin a cikin jirgin a ranar Lahadi 16 ga…
Read More

‘Yan matan Kebbi: MOPPAN ta jajenta wa gwamnati da al’ummar jihar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gamayyar Ƙungiyar masu Shirya Fina-finai ta ƙasa (MOPPAN) ta miƙa saƙon jajentawa ga gwamnati da al'ummar jihar Kebbi, bisa awon-gaba da ƴan bindiga suka yi da ɗalibai mata guda 25 a makarantar Government Comprehensive Girls' Secondary School, Maga da ke jihar a farkon makon da ya gabata. Shugaban ƙungiyar, Shehu Hassan Kano ya sanar da haka a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakataren MOPPAN, Dakta Mohammed Ibrahim Gumel, ranar Juma'a. Ya ce, "Masana'antar Kannywood ta shiga ɗimuwa da tadhin hankali bisa wannan mummunan iftila'i da ya faru. Allah ya kiyaye, Allah…
Read More

CAN ta tabbatar da garkuwa da ɗalibai 215 da ma’aikata 12 a harin makarantar Neja

Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), ta ce kimamin mutune 227 da suka ƙunshi ɗalibai 215 da malamai 12 ƴan bindiga suka yi awon-gaba da su a lokacin da suka kai hari makarantar St. Mary da ke garin Papiri a Jihar Neja. A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar reshen jihar, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya fitar, ya ce harin ya jefa al'ummar yankin cikin ɗimuwa da firgici. Da tsakar daren ranar Alhamis ne wasu mahara ɗauke da muggan makamai suka far wa makarantar wadda ta kwana ce, da ta ƙunshi firamare da sakandire, inda suka sace ɗaliban, bayan sun harbi maigadi.…
Read More

DSS ta mayar da Nnamdi Kanu kurkukun Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Bisa la'akari da hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS), ta kai tsararren jagoran ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), Nnamdi Kanu zuwa gidan gyaran hali a Jihar Sakkwato. Wata majiya daga hukumar ta shaida wa manema labarai cewa an ɗauki matakin ne bayan yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai da kotu ta yi bisa samunsa da hannu a laifuka bakwai masu alaƙa da ta'addanci. Da yake gabatar da shari'ar a ranar Alhamis a Abuja, Alƙali James Omotosho ya umarci DSS ta mayar da Kanu zuwa kowane kurkuku a ƙasar…
Read More

Shettima zai wakilci Tinubu a taron G20

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Juma'a Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a babban taron shugabannin ƙasashe na G20, wanda za a yi Johannesburg na ƙasar Afirka ta Kudu. Da fari Shugaba Tinubu ya tsayar da tafiyarsa ta Johannesburg ne domin jin ba'asin lamuran tsaro da ya shafi jihohin Kebbi da Kwara, inda aka yi garkuwa da ɗalibai da masu ibada. Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu, wanda shi ne shugaban G20, ya gayyaci takwaran nasa na Nijeriya domin halartar taron na wannan shekarar. A yau 22 ga Nuwamba…
Read More