Babaji

5693 Posts

Kebbi: MSSN ta yi jimamin rashin shugabanta na Yauri da ƴan bindiga suka halaka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hedikwatar Ɗalibai Musulmi ta Ƙasa (MSSN) ta nuna kaɗuwarta game da rashin Shugabanta na yankin Yauri a Jihar Kebbi, Ustaz Alqasim Usman Ibrahim, wanda ƴan bindiga suka halaka a makom da ya gabata. A cewar MSSN, an yi garkuwa da mamacin ne a gonarsa a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2025, inda bayan kwana guda da faruwar haka aka tabbatar da rasuwarsa. A wata sanarwa da Sakataren hulɗa da jama'arta, Moshood Abiola Olatunbi ya fitar, MSSN ta bayyana rashin a matsayin abin takaici da ke ƙarfafa ta'azzarar matsalar tsaro a yankunan Musulmi da…
Read More

Abin da ya sa ba mu halarci taron ACF na cikarta shekara 25 ba – Gwamnonin Arewa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma ta cigaba soka game da rashin halartar gwamnonin arewa taron bikin cikar Ƙungiyar Mashawartan Arewa (ACF) shekaru 25 da kafuwa, wanda aka gudanar a Kaduna, ranar Asabar. Hakan ya sa Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta fitar da saƙon ƙarin haske akan hukuncin duba da yadda wasu ke yi wa matakin kallon abinda bai dace ba. Bikin ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen arewa, tun daga ranar farko har zuwa ranar rufewa, waɗanda su ka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, hamshakin attajirin Afirka Aliko Ɗangote, Abdulsamad Isiyaka…
Read More

Don a tabbatar da zargin kisan Kiristoci ake sace ɗalibai, inji Sheikh Gumi

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce yawaitar sace-sacen ɗaliban makaranta da ake gani a ƴan kwanakin nan al'amari ne shiryayye. A wani rubutu da ya wallafa ta kafar Facebook, Shehin malamin ya ce an dawo an shirya garkuwa da ɗaliban ne don ƙarfafa zargin waɗansu da ke son ƙaƙaba wa Nijeriya kisan Kiristoci. Ya kuma ce halin da ake ciki yana shafar yaran addinai daban-daban, ba Kiristoci kaɗai ba. Sannan, duk da ta'azzarar matsalar tsaro, abu ne da zai zo ƙarshe "da yardar Allah" a Nijeriya. Sheikh Gumi na ɗaya…
Read More

Harin Kwara: Cocin CAC ta fitar da sunayen waɗanda aka sace har da yara takwas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Cocin Christ Apostlic (CAC) ta fitar da sunayen masu ibada guda 38 da aka yi garkuwa su a lokacin da ƴan bindiga suka kai farmaki a garin Eruku na Ƙaramar Hukumar Ekiti a Jihar Kwara. Hakan na zuwa ne bayan ƙasa da kwana biyu da ƴan bindigar sukanemi a biya su kimanin Naira biliyan 3.8 a matsayin kuɗin fansarsu, wanda hakan ke nuna za a biya miliyan N100 ga kowane mutum ɗaya daga cikinsu. Jaddawalin sunayen ya nuna cewa mai shekaru 64 daga cikin waɗanda aka sacen ita ce mafi tsufa yauinwata ƴar shekara…
Read More

Rashin tsaro: Shugaban DSS ya gana da Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa

Darakta Janar na hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) Adeola Ajayi, ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tnubu rahoton halin da ake ciki game da sace-sacen ɗalibai da ƴan bindiga bindiga suka yi a jihohin Kebbi da Neja da ke arewacin ƙasar. A sanarwar da Bayo Onanuga, Kakakin Shugaban ƙasa ya fitar, shugaban na DSS ya gana da Tinubu ne a jiya Juma'a da dare. A ranar Litinin ne ƴan bindiga suka sace ɗalibai mata 25 daga wata makarantar sakandare ta mata a garin Maga da ke ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi. Sai kuma ranar Juma'a, inda aka yi…
Read More

Nijeriya ta musanta rufe makarantu a duka faɗin ƙasar

Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotonnin da ake yaɗawa cewa ta umarci a rufe makarantu a faɗin ƙasar daga ranar Litinin mai zuwa. A wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta fitar, ta ce rahoton ba gaskiya ba ne. "Rahoton ba daga gwamnatin tarayya yake ba, ko ma'aikatar ilimi, ko wata ma'aikatar ilimi ta jiha, ko wata hukumar tsaro." A ranar Juma'a gwamnati ta sanar da rufe makarantun sakandare na kwana su guda 41 mallakarta da ake kira da Unity Schools a faɗin ƙasar. Wannan umarni na zuwa ne bayan sace ɗalibai mata 25 a jihar Kebbi da kuma wasu 315 a…
Read More

Yana nuna Hausawa ƴan bindiga ne – Musulmi sun nemi a dakatar da Netflix kan fim ɗin The Herd

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata tawagar al'ummar Musulmin Nijeriya ta ƙaddamar da kiran neman a dakatar da manhajar Netflix da ayyukanta bisa yaɗa fim ɗin 'The Herd'. Fim ɗin, wanda ke nuna yadda ake garkuwa da ƴan Nijeriya a yau da kullum daga Fulani makiyaya da ƴan bindiga, ya haifar da cecekuce acikin masu kallo musamman a kafar X inda ake ta kiraye-kirayen al'umma da su goge Netflix daga wayoyinsu. Hakan yana nuni da yadda ake cigaba da fargaba game da yadda ake nuna ababen da ke faruwa musamman akan ƴancin yaɗa ayyukan fasaha da nauyin zamantakewa acikin…
Read More

Wajibi ne ka yaƙi ƴan bindigar Fulani – Ɗan majalisar Amurka ga Tinubu bayan garkuwa da ɗalibai

Ɗan Majalisar Dokokin Amurka, Riley Moore, ya kirayi Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta fuskantar ƙungiyoyin ƴan bindiga a yankin Arewa ta tsakiya. Moore ya faɗi haka ne kwanaki kaɗan da sace yara sama da 300 da malamai 12 daga Makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke Jihar Neja a ranar Juma’a. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, Moore ya bayyana ɓacin ransa kan harin da aka ruwaito, yana cewa: "A matsayina na uba, ganin irin waɗannan hare-hare yana tada min hankali ƙwarai." Ya kuma yi kira ga hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen yaƙar…
Read More

Ba na tunanin kansa ƙalau yake – Soyinka ya caccaki Trump kan barazanar kai wa Nijeriya hari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Farfesa Wole Soyinka ya caccaki Shugaban Amurka Donald Trump bisa barazanar da ya yi na ɗaukar matakin soja akan Nijeriya, yana mai bayyana kalamansa a matsayin abinda ke nuna rashin sanin tsauraran ƙalubalen tsaro da Nijeriya ke fuskanta. Gogaggen tauraron marubucin ya bayyana haka ne a ranar Jumma'a bayan ganawa da Gwamnan Jihar Benuwai, Hyacinth Alia a Makurɗi. A cewar Soyinka, babu wani shugaba na wata ƙasa da zai tsoma baki a matsalolin tsaron Nijeriya ba tare yin fahimtar da ta dace ba game da sarƙaƙiyar da ke cikin al'amarin ba. Ya soki Shugaba…
Read More

Lewandowski ya zura ƙwallon farko a Camp Nou cikin shekara biyu bayan Barca ta lallasa Bilbao

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wasan farko da ta buga a filin wasa na Camp Nou tun bayan gyara shi, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta yi nasarar lallasa Athletic Bilbao da ci 4 da 0. Hakan ya nuna Barca ta yi wasa 12 a gasar Laliga ba tare da an doke ta a ko ɗaya ba, inda ta yi nasarar a goma da yin canjaras a biyu. Wannan shi ne wasa na farko a filin wasan da ƙungiyar ta yi nasara a tsawon sama da shekarq biyu. Bayan minti huɗu da fara wasan ne ɗan wasan gaba…
Read More