Babaji

5693 Posts

An yi jana’izar ƴan sandan da ƴan bindiga suka halaka a Bauchi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin ne aka gudanar da janazar waɗannan ƴan sandan da ƴan ta'adda suka halaka a Jihar Bauchi bayn kai musu farmaki a bakin aiki. An ruwaito cewa, jami'an sun rasa ransu ne a wani ƙauye mai suna Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo yayin wani mummunan farmaki da ƴan bindiga suka kai musu a yankin. Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Sani Omolori Aliyu ne ya jagoranci taron binne mamatan. Saidai, babu ƙarin bayani game da yadda aka gudanar da jana'izar a lokacin haɗa wannan rahoton. A wani labarin kuwa, Gwamnan Jihar…
Read More

2027: Atiku ya koma ADC a hukumance

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya shiga jam'iyyar ADC a hukumance, lamarin da ke nuna ƙarfafa jam'iyyar yayin tunkarar babban zaɓen 2027. Atiku ya sanar da haka ne a jiya Litinin ta kafar X, inda ya wallafa hotonsa riƙe da katin zaman mamban jam'iyyar, wadda ke cigaba da maraba da gaggan ƴan siyasa. Hakan na zuwa ne watanni da sanar da yin murabus ɗinsa daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP tun a watan Yuli, yana mai bayyana rikici na tsawon lokaci da ya dabaibaye ta a matsayin dalilin ficewarsa. Haka kuma, wannan ci-gaban…
Read More

Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Dharmendra ya rasu

Fitaccen jarumin finafinan masana'antar Bollywood ta Indiya, Dharmendra wanda ake kira da Dharam ya rasu a birnin Mumbai na Indiya yana da shekara 89 a duniya. Firaministan India Narendra Modi ya bayyana jajensa ga iyalan mamacin da ƴan ƙasar baki ɗaya, sannan ya bayyana rasuwar jarumin da "ƙarshen zangon jaruman sinima a Indiya." Dharmendra, wanda ya kasance yana bayyana da "mutum mai sauƙin kai" ya daɗe yana jan zarensa a harkar fim, inda yake nishaɗantar da miliyoyin masoyansa a duniya. Ya yi fice da sunan Veeru saboda rawar da ya taka a fim ɗin Sholay a shekarar 1975, sannan ya…
Read More

Rashin tsaro: Gwamnatin Bauchi ta umarci a rufe dukkan makarantun jihar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da rufe dukkan makarantun da ke faɗin jihar bisa ƙamarin taɓarɓarewar tsaro a sassan Nijeriya musamman arewa. Umarnin ya shafi makarantun firamare, sakandare da da manyan makarantu da suka ƙunshi na Gwamnatin Tarayya da masu zaman kansu. A jiya Lahadi jami'in hulɗa da jama'a na ma'aikatar ilimi, Jalalideen Usman ya sanar hakan a wata takarda ga manema labarai. A cewarsa, an ɗauki matakin ne bayan shawarwari da masu ruwa da tsaki da kuma la'akari da rashin tsaro a ƴan kwanakin nan da musamman ya fi shafar ɗaliba, malamai da…
Read More

Gwamnatin Kaduna ta musanta biyan ƴan bindiga biliyan N1, ta ba El-Rufa’i mako guda ya tuba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Uba Sani, ta yi watsi da zarge-zargen da tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufa'i ya yi akanta cewa ta biya ƴan bindiga Naira biliyan 1. Ta bayyana kalaman, waɗanda aka yi su yayin hira da gidan talabijin na Channels a matsayin ƙarya da ake nufin siyasantarwa, kuma abin da babu hujja a kai. A wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida, Dakta Sule Shu'aibu (SAN) ya fitar, gwamnatin ta ce zarge-zargen El-Rufa'i babu ƙamshin gaskiya acikinsu, tana mai zargin sa da yunƙurin ruɗar da al'umma da kushe…
Read More

Kwara: Mutane 38 da aka sace a cocin Eruku sun shaƙi iskar ƴanci bayan Tinubu ya ƙarfafa jami’ai

Dags BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Kwara Abdulrahman AbdulRazaq ya sanar da sako baki ɗaya mutane 38 da aka yi garkuwa da su a Cocin Christ Apostlic (CAC) na Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti cikin aminci. A yau Lahadi mutanen suka shaƙi iskar ƴanci bayan atisayen da ya ƙunshi ɓangarorin hukumomin tsaro na manyan matakan gwamnati. A sanarwar da Sakataren yaɗa labaransa, Rafiu Ajakaye ya fitar, Gwamna AbdulRazaq ya danganta nasarar ceto mutanen da shiga tsakani na Shugaba Bola Tinubu. A cewar gwamnan, Tinubu bai tsaya a sanya ido wajen ceton ba, hat ma da sadaukar da bulaguronsa…
Read More

‘Yan bindiga na shirya wa harin Amurka wajen amfani da yara a matsayin kariya, inji Jerry Gana

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana ya koka game da al'amarin garkuwa da mutane da ya yi ƙamari a arewacin Nijeriya, yana mai gargaɗin ta yiwu ƴan bindiga suna yin haka ne domin amfani da ƴan makaranta da ƙauyawa a matsayin kariya ga harin da Amurka ka iya kawo wa Nijeriya. A jiya Asabar Farfesan ya bayyana haka a wani taro na musamman don karrama shugaban Hukumar Kwastom (NCS) Bashir Adewal Adeniyi, wanda ya zama sabon shugaban ƙungiyar jami'an Kwastom ta Duniya (WCO). A cewar Gana bayanan sirri da salon hare-haren ƴan kwanakin nan…
Read More

Maga 25: Rundunar Sojoji ta fara binciken janyewar dakaru gabanin garkuwa da ɗaliban Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojojin ƙasa ta ce ta fara gudanar da binciken cikin gida game da zargin cewa sojojin da aka tura aiki a makarantar mata da aka sace ɗalibai 25 sun janye gabannin ƴan bindiga su isa garin, wato Maga a jihar Kebbi. A yau Lahadi Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta sanar da matakin binciken biyo bayan cecekucen al'umma game da al'amarin duk da cewa bayanan sirri sun nuna cewa makarantu sune abin hari ga ƴan ta'adda. A sanarwar da Daraktan Hulɗa da jama'a na DHQ, Manjo Janar Michael Onoja ya fitar, Hedikwatar ta ce matakin…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: 50 daga cikin ƴan makarantar Neja da aka sace sun tsira

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin ɗaliban St Mary's Catholic School, Papiri a Jihar Neja su guda 50 da aka yi garkuwa da su ne suka yi nasarar kuɓuta daga hannun ƴan bindiga tare koma wa cikin iyalansu. Hakan na nufin har yanzu akwai sauran ɗaliba 253 da malamai 12 da ke hannun waɗanda suak yi garkuwa da su. Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) a jihar kuma shugaban makarantar, Reberen Bulus Dauwa Yohanna ya sanar da haka ga manema labarai a yau Lahadi. Wannan shi ne nasara na farko da aka sami akan al'amarin tun bayan faruwarsa a rare…
Read More

Yanzu-yanzu: Mayaƙan ISWAP sun yi garkuwa ƴan mata 13 a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi garkuwa da wasu ƴan mata guda 13 a yankunan manoma da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya faru ne a Gundumar Mussa yayin da ƴan matan suke tsaka da aiki a gonaki, inda kwatsam sai mayaƙan zagaye su tare da yin awon-gaba da su. Maitaimakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Rt. Hon. Abdullahi Askira ya tabbatar da aukuwar lamarin a yau Lahadi. Askira, wanda shi ke wakiltar mazaɓar Askira-Uba ya ce ƴan matan ƴan shekaru 15 ne zuwa 20, waɗanda suak je gona…
Read More