Babaji

5693 Posts

Turaki ya karɓi ragamar jagorancin PDP bayan rikici a sakatariyar jam’iyyar

A ranar Talata Kabiru Tanimu Turaki, ya karɓi ragamar jagorancin PDP a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja daga hannun ɓangaren da ke goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike. Da yake magana da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar, Turaki ya tabbatar da cewa ya shiga ofishinsa a hukumance, yana mai cewa wannan mataki ya kammala dukkan tsarin miƙa ragamar jagorancin jam’iyyar. Turaki ya soki matakan wasu mambobin jam’iyyar da suka bayyana cewa an kore su a taron jam’iyya na baya-bayan nan, inda ya zarge su da kawo ’yan daba domin tada hatsaniya a wajen wani taro da aka shirya bisa ka’ida…
Read More

‘Yan matan Kebbi: Shugaban sojoji ya kai ziyara, ya umarci dakarun tsaro su gaggauta ceto su

Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umarci dakarun rundunar 'Operation Fansan Yamma' da su ƙara himma wajen ganin sun ceto ɗaliban da aka sace a 'Government Girls Comprehensive Senior Secondary School (GGCSS), Maga', da ke karamar hukumar Danko-Wasagu ta Jihar Kebbi. Janar Shaibu ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin wata ziyarar aikin da ya kai jihar Kebbi domin duba yadda ake gudanar da ayyukan tsaro. Da yake jawabi ga kwamandoji da dakarun da ke kan gaba da aiki, Janar Shaibu ya buƙace su da su gudanar da ayyukan da suka dogara da sahihan bayanan leƙen…
Read More

Yadda Gwamna Makinde da Bala Mohammed suka yi gudun tsira yayin harbe-harben ƴan sanda da fesa hayaƙi a sakatariyar PDP

Rikici ya ɓarke a hedikwatar jam'iyyar PDP da ke Abuja, wanda ya tilasta wa ƴan sanda harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa magoya bayan jam'iyyar a daidai lokacin da ake cigaba da taƙaddama akan shugabancin jam'iyyar tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna. Rikicin ya ɓarke ne a Wadata Plaza yayin da Gwamna Seyi Makinde, Bala Mohammed, da shugabannin jam'iyyar da Turaki ke jagoranta suka isa. Al'amarin ya haifar da rikici da 'yan sanda da magoya bayan ɓangaren Sanata Anyanwu waɗanda suka yi ƙoƙarin hana shiga farfajiyar sakatariyar. Ministan Abuja, Nyesom Wike, shi ma ya isa Wadata Plaza amma…
Read More

Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin malamai don zama da Sheikh Yahaya Masussuka

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya zama tsakanin kwamitin malaman addini da Malam Yahaya Masussuka biyo bayan wasu zarge-zarge da ƙorafe-ƙorafe da wasu malamai a jihar suka yi cewa salon wa’azinsa ya saɓa wa ka’idojin shari’ar Musulunci. Bayanin haka na ƙunshe a wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar wanda daraktan Yaɗa Labarai, Ibrahim Alamu Gafai ya sanya wa hannu a yau Talata. A cewar sanarwar, Malam Yahaya a kwanakin baya ya kai korafi cewa wasu mambobin ƙungiyar Izala na zaginsa tare da yi masa barazana, inda gwamnati ta mika batun zuwa ga…
Read More

Ku gaggauta ceto ƴan matan Kebbi – Tinubu ga hukumomin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta ceto ɗalibai mata guda 25 da aka yi awon-gaba da su a makarantar Government Girls Comprehensive Senior Secondary School, Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu na Jihar Kebbi. Da fari, rundunar ƴan sandan jihar ta hannun kakakinta CSP Nafi'u Abubakar Kwatarkwashi, ta bayyana yadda aka yi garkuwa da ɗaliban a safiyar ranar Litinin. A yayin haka ne aka halaka mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku, da raunata mai gadinsu, Ali Shehu da harbin bindiga a hannunsa na dama. Da yake sanar da umarnin Fadar Shugaban…
Read More

Yadda ƴata ta tsira bayan ƴan bindiga sun halaka mijina – Matar mataimakin shugaban makarantar Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Matar mataimakin shugaban makarantar Government Girls Comprehensive Senior Secondary School, Maga na Jihar Kebbi da aka kashe, ta bayyana yadda ƴarta ta tsira yayin harin ƴan bindiga da ya yi sanadin awon-gaba da ɗalibai 25. Rahotanni sun bayyana cewa, matar, mai suna Amina Hassan ta ce maharan sun kutsa gidansu ne da misalin ƙarfe 3:30 na asuba a lokacin da ƴan gidan suke barci. Ta ce, da fari sun yi zaton hayaniya ce ta wasu dabbobi ne, inda ta faɗa wa marigayi mijin nata cewa sun fara lalata kayayyakin gida. A lokacin da ya…
Read More

ISWAP ta kashe Janar Uba a Borno

A cikin wata sanarwa da ta rubuta da harshen Larabci, wacce ta wallafa a mujallar farfajiyarta mai suna Amaq, ƙungiyar ISWAP ta bayyana cewa ta kama Janar Uba kuma ta kashe shi bayan ta gudanar da bincike a kansa. Shugaban Rundunar sojojin, M. Uba, wanda tun da farko rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa yana cikin ƙoshin lafiya bayan mayakan ISWAP sun yi wa tawagarsa kwanton-bauna a hanyar Damboa zuwa Biu a Jihar Borno, yanzu an tabbatar da mutuwarsa. Ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP ta sanar da cewa ta kama Janar Uba kuma ta kashe shi, tare da sakin hotunan da…
Read More

Mutum miliyan 2.3 sun yi rajistar zaɓe yayin da jihohin Osun, Imo da Kano suka fi yawan adadi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Lahadi Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fitar da sabon ƙididdiga na waɗanda suka yi rajistar zaɓe a faɗin Nijeriya waɗanda adadinsu ya kai 2,316,232, sannan kuma hakan ya nuna Jihar Osun ita ce akan gaba da mafi yawan mutane. INEC ta ce hakan wani ɓangare ne na kula da tsare gaskiya da adalci a yayin gudanar da al'amarin, wanda yanzu an kammala mako na 12 da farawa. A cewar hukumar, Osun tana da jimillar mutane 185,089 da suka kammala rajista, sai Imo mai mutane 143,386. Ita kuwa Jihar Kano, wadda ke…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da ɗaliban sakandare da halaka ma’aikaci a Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Da asubahin yau Litinin da misalin ƙarfe 5:52 ne wasu ƴan bindiga a Jihar Kebbi suka farmaki makarantar sakandare ta Maga Comprehensive Girls' Secondary School, inda suka yi garkuwa da ɗalibai masu yawa. A cewar rahoton Humangle, harin ya yi sanadiyyar rasa ran ɗaya daga cikin ma'aikatan makarantar da raunata mai gadi. Rahoton ya ƙara da cewa, mazauna yankin sun ce maharan suna cigaba da zama a wajen inda suke shelanta wa hukumomin tsaro cewa su kai wa ɗaliban ɗauki. Saidai har zuwa lokacin kammala haɗa rahoton, ba a samu saƙo na musamman akan…
Read More

Batun kai wa Laftanal Yarima hari ba gaskiya ba ne, inji ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Abuja, ta yi watsi da rahotannin da ke cewa Laftanal Ahmed Yerima na Rundunar Sojin Ruwa ya tsallake rijiya da baya bayan wani hari da aka kai masa a Birnin Tarayyar, tana mai bayyana rahoton a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al'umma. Rahotannin, waɗanda aka baza su ta kafafen sadarwa a ƙarshen mako, sun yi zargin cewa wasu motocin Hilux biyu marasa lambobi sun bi diddiginsa a yammacin ranar Asabar. A cewar rahoton wanda ba a tabbatar da ingancinsa ba, al'amarin ya faro ne tun da…
Read More