Babaji

5698 Posts

DA Ɗumi-Ɗumi: ASUU ta janye yajin aikin mako biyu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Malaman jami’o’in Nijeriya ASUU, ta dakatar da yajin aikin sati biyu da ta shiga na gargaɗi a dukkanin jami'o'in ƙasar. ASUU ta sanar da haka ne a yau Laraba, yayin taron ganawa da manema labarai a hedikwatarta da ke Birnin Tarayya Abuja. Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna ya bayyana haka ga ƴan jarida, inda ya ce hakan ya samu ne a sakamakon shiga tsakanin ta da Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dattawa tare da wasu manyan ƙasa suka yi. Farfesan ya ƙara da cewa, majalisar zartarwar ƙungiyar ta cimma matsayar bai wa gwamnatin tarayyar…
Read More

Maryam Sanda za ta iya cigaba da zaman kurkuku bayan Antoni Janar ya nemi wasu hukumomi su binciki jaddawalin ɗaurarrun da Tinubu ya yafewa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Duk da cewa tana ɗaya daga cikin ɗaurarrun mutane 175 da Shugaban Bola Tinubu ya yi wa afuwa, wannan matar da aka yanke wa hukuncin kisa kan halaka mijinta, wato Maryam Sanda, ka iya cigaba da zama a gidan yari. Haka na zuwa ne a yayin da Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a, Frins Lateef Fagbemi ya umarci hukumomi da su yi nazari akan jaddawalin waɗanda aka yafewa gabanin aiwatarwa. A shekarar 2017 aka yanke wa Maryam Sanda hukunci bayan samun ta da laifin kisan mijinta, Bilyaminu Bello, inda a kwanan nan ta shiga…
Read More

Tinubu ya nemi majalisa ta tabbatar da Bernard Mohammed Doro a matsayin minista

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa sunan Dakta Bernard Mohammed Doro na jihar Filato domin ta tantancewa da tabbatar da shi a matsayin sabon minista a Majalisar Zartarwa ta ƙasa. Matakin ya zo ne watanni kaɗan da aka zaɓi tsohon Ministan Jinƙai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe shi ma daga jihar a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC. Dakta Doro, wanda aka haifa a yankin Kwall na Ƙaramar Hukumar Bassa ta jihar Filato a ranar 23 ga Janairun 1969, yana da gogewa ta fiye da shekaru 20 a fannoni da suka…
Read More

Tinubu ya amince da tallafin N250,000 ga ƙananan ƴan kasuwa a Katsina

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bada tallafin Naira 250,000 ga ƙananan ƴan kasuwa da matsakaitan masana’antu (MSME) da suka nuna bajinta a yayin Faɗaɗɗen Taron Ƙanana da Matsakaitan Masana’antu na Ƙasa (Expanded National MSME Clinic) da aka gudanar a Katsina. Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ya sanar da hakan yayin kaddamar da taron karo na tara na shirin, wanda aka shirya don tallafawa ƙanana da matsakaitan sana’o’i da kuma farfaɗo da tattalin arzikin al’umma. Ya bayyana cewa an samar da shirin ne domin kawo hukumomin gwamnati kusa da masu sana’a da kuma karfafa fasahar kirkire-kirkire, samar…
Read More

Yarinya ta zama Mataimakiyar Shugaban Nijeriya na lokaci ɗaya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gayyaci wata matashiya mai suna Joy Ogah, don ta zauna a kan kujerarsa ta Mataimakin Shugaban Ƙasa ta yi jawabi ga al’ummar ƙasa kan kudirin inganta hakkokin ƴaƴa mata. Shettima ya yi haka ne a lokacin da yake jawabi yayin ganawarsa da tawagar 'PLAN International' ƙarƙashin jagorancin Daraktar Inganta Fasahar kirkire-kirkire ta ƙungiyar, Helen Mfonobong Idiong a ranar Litinin. Mataimakin Shugaban Kasar ya tabbatar wa mahalarta taron cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sadaukar da kai wajen inganta ilimin 'ya mace a duk fadin Najeriya.Shettima ya ce, cikin…
Read More

Zargin juyin mulki: Ku faɗa wa ƴan Nijeriya haƙiƙanin abinda ya faru – ADC ga Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar adawa ta ADC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta fayyace haƙiƙanin abinda ke faruwa akan rahotannin da ke yawo cewa an yi yunƙurin juyin mulki ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Ta yi gargaɗin kada a riƙa amfani da jita-jita wajen rufe bakin ƴan adawa ko kuma karkatar da tunanin al'umma game da gazawar gwamnati. A wata takarda daga Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Bolaji Abdullahi a ranar Litinin, jam'iyyar ta ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu akan kada ya yi amfani da zargin juyin mulki wajen rufe bakin ƴan adawa ko jagororinsu da sunan…
Read More

Barazanar ƙasashen waje na neman durƙushe haɗin kan ƴan Nijeriya, inji Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ta koka game da barazanar da ƴan ƙasashen waje ke yi akan Nijeriya da al'ummarta wanda ke neman hargitsa al'amura da durƙusar da haɗin kan al'umma a ƙasar. Akan haka ne ta kirayi ƙwararru akan harkokin yaɗa labarai da su riƙa amfani da dabaru wajen daƙile zantukan ƙarya da ake yaɗawa akan ƙasar musamman kan batun kisan kiyashin Kiristocin ƙasar da wasu ƴan waje suka ƙirƙira. Ministan Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris ya bayyana haka a Abuja yayin taron 'World Public Relations Forum' (WPRF Abuja 2026),…
Read More

ASUU: NLC ta gargaɗi Gwamnatin Tarayya kan rikici da manyan makarantu

Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta ba gwamnatin tarayya wa’adin mako huɗu domin ta kammala tattaunawa da ƙungiyoyin ma’aikata na manyan makarantu ko kuma ta fuskanci yajin aikin ƙasa baki ɗaya daga dukkan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta. Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero, ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, inda ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ƙungiyoyin ilimi don tabbatar da biyan haƙƙoƙin da aka amince da su, da kuma inganta kuɗin gudanarwa da albashi a jami’o’i, kwalejoji da sauran cibiyoyin ilimi. Ajaero ya ce, NLC ba za ta sake amincewa da…
Read More

Zargin kitsa juyin mulki: Ana binciken ƴan siyasa da sojoji a Kudu da Arewa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A sakamakon zargin juyin mulki ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, an sanya wasu ƴan siyasa da jami'an sojoji a yankin Kudanci da Arewacin Nijeriya a sahun waɗanda zargi ya yi ƙarfi akansu. Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu ana gudanar da bincike akan wasu sojoji da ƴan siyasa bisa zargin su da hannu a kitsa juyin mulkin. A kwanan nan ne Hedikwatar Tsaro DHQ, ta sanar da kama jami'an soji su guda 16 akan abinda ta kira da rashin biyayya ga tsarin aiki. Saidai, wasu na ganin an kama su ne sakamakon…
Read More

Hajjin 2026: NAHCON ta ƙaddamar da kwamitin jiragen sama don inganta zirga-zirga

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ƙaddamar da kwamitin sanya ido akan harkokin jiragen sama domin aikin Hajjin 2026. An ƙaddamar da kwamitin ne a wani taro da aka gudanar a Hajj House da ke Birnin Tarayya Abuja. Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya kirayi mambobin kwamitin da su yi aiki bisa gaskiya da kishin al’umma, tare da tabbatar da cewa dukkan shirye-shiryen jiragen sama na tafiya da dawowar alhazai sun kasance akan tsari da kuma aminci. Ya bayyana cewa, gwani Shugaba Bola Tinubu na ɗaukar aikin Hajji a matsayin amana ta addini saboda haka wajibi ne a tabbatar…
Read More