Babaji

5698 Posts

MOPPAN ta yaba wa Abdul Amart bisa kai Jaruma Halisa umrah

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa MOPPAN, ta yaba wa sanannen furodusa a masana'antar Kannywood, Abdul Amart kan daukar nauyin jaruma Halisa Mohammed zuwa aikin umara. Sakataren MOPPAN, Dakta Mohd I. Gumel a wata takarda, ya miƙa godiya da jinjina ga furodusan a madadin mambobin ƙungiyar, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tausayi da kulawa ga abokan aiki da ma al'umma baki ɗaya. Ya ce, "wannan taimakon nasa ba shine na farko ba", abu ne da ya saba yi wa kowane ɗan masana'antar da ke cikin halin buƙatar a tallafa masa. Sakatare…
Read More

Zanga-zangar Nnamdi Kanu: Yadda hargitsi ya tashi bayan jami’an tsaro sun yi kwanton ɓauna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An samu ƙarin adadin jami'an tsaro a Birnin Tarayya Abuja a yayin da zanga-zangar lumana ta neman sako Nnamdi Kanu ta rikiɗe zuwa hargitsi a wasu sassa. Rahotanni sun bayyana cewa, al'amarin ya faro ne a lokacin da jami'an tsaro suka yi yunƙurin dakatar da zanga-zangar ta '#FreeNnamdiKanu', wadda ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Omoyele Sowore ya shirya. An ruwaito cewa, jami'an sun watsa barkonon tsohuwa daga yankin Maitama har zuwa Transcorp, inda aka gargaɗi al'umma da su ƙaurace wa wuraren. Haka kuma, an datse babbar hanyar da ke kaiwa zuwa…
Read More

Zanga-zanga: ‘Yan sanda sun kama lauyan Nnamdi Kanu da wasu a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an ƴan sanda sun cika hannu da Aloy Ejimkor, wanda shi ne lauyan da ke kare tsararren jagoran Ƙungiyar masu fafatukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), wato Nnamdi Kanu a yayin da ake zanga-zanga a Abuja. Lauyan ne ya bayyana kamen ta shafinsa na kafar X a yau Litinin, 20 ga watan Oktoba, 2025. Ejimakor ya bayyana cewa an kama shi ne da wasu da dama a lokacin da ake gangamin kiran a sako Nnamdi Kanu a Birnin Tarayyar. Da fari lauyan ya zargi ƴan sanda da fesa wa dandazon ƴan zanga-zangar hayaƙi mai sa…
Read More

DA Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan sanda sun watsa barkonon tsohuwa ga ƴan zanga-zangar sako Nnamdi Kanu a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar AAC kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowere da wasu ƴan gangamin neman sako Nnamdi Kanu, wato mai fafutukar kafa ƙasar Biafara, sun tsira a yayin da jami'an tsaro suka yi harbe-harbe ana tsaka da zanga-zanga. A cewar DAILY POST, jami'an, waɗanda suka haɗa da ƴan sanda da sojoji sun fara sa ido ne akan zanga-zangar, wadda aka fara a safiyar yau Litinin. An ga wani faifan bidiyo da ke nuna yadda ɗan gwagwarmayar tare da wasu masu zanga-zanga ke ƙoƙarin neman tsira daga harbe-harben jami'an tsaron. Da fari…
Read More

Har yanzu darussan Lissafi da Turanci wajibi ne ga masu neman manyan makarantu, inji Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce har yanzu darussan Lissafi da Turanci suna daga cikin muhimman darussan da ɗaliban sakandare ke buƙata a yayin rubuta a jarabawar kammala karatu a zangon. Hakan na nufin duk da sabuwar manufar da aka fito da ita kan tsarin karɓar ɗalibai a jami’o’i da wasu manyan makarantu. A wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta fitar a ranar Lahadi, ta ce sabuwar dokar da aka yi ta bai wa jami’o’i sassauci ne wajen shigar da ɗalibai wai za a cire wajabcin rubuta Lissafi ba. Daraktar yaɗa labarai Misis Boriowo Folasade, fitar…
Read More

Ɗan jaridar Kano, Ibrahim Ɗan Uwa Rano ya shaƙi iskar ƴanci bayan hadimin gwamnan Kano ya sa an kama shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda ta sako ɗan jarida mazaunin Kano, wato Ibrahim Ɗan Uwa Rano bayan alla-wadai daga Cibiyar Fasahar Labarai da Ci-gaba, ƙungiyar Amnesty International da wasu ƙungiyoyin al'umma. Ɓangarorin sun bayyana kamawa da tsare ɗan jaridar a matsayin abinda aka yi ba bisa doka ba da nufin rufe bakin gidajen jaridu. An tsare Rano ne bisa zargin sa da laifin ɓatanci a ofishin ƴan sanda na Zone 1 Police Headquarters da ke Kano. Da fari CITAD da Amnesty International sun nemi a gaggauta sako shi ba tare da sharaɗi ba, lamarin da suka…
Read More

Zargin badaƙalar N6.5bn: ‘Yan sanda sun kama ɗan jaridar Kano bisa ƙorafin mataimaki ga Gwamna Abba

A ranar Asabar Rundunar ƴan sanda reshen Zone 1 Kano, ta kama tare da tsare ɗan jarida Ibrahim Ishaq, wanda aka fi sani da Ɗan'uwa Rano. Jami'an sun kama sanannen ɗan jaridar mai gabatar da shirye-shirye kuma shugaban sashin shirye shirye na musamman na Hikima Radio Ibrahim Ishaq ne inda suka yi masa tambayoyi bisa zargin ɓatanci. Hakan ya biyo bayan ƙorafin da Daraktan Al’amuran Fadar gwamnatin jihar, Abdullahi Ibrahim Rogo ya shigar, inda ya zargi ɗan jaridar da ɓatanci da ɓata masa suna ta cikin rahotannin da ake yaɗawa a Dan'uwa Rano TV, wata kafar yaɗa shirye-shirye ta yanar…
Read More

Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da tattaunawa da kamfanin ƙasar Chana don yaƙar Lakurawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Kebbi ta jaddada aniyarta ta cigaba da aiki tare da dakarun sojoji, ƴan sanda da wasu hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa ga al'umma a sassan jihar. A baya ne Gwamna Dakta Nasir Idris na jihar ya karɓi baƙoncin tawagar tsaro ta G-Safety domin haɗa hannu da ita wajen ganin ta faɗaɗa ayyukanta na daƙile matsalolin ta'addanci a jihar. A ranar Laraba gwamnan ya karɓi tawagar ta ƴan Chana da nufin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi dabarun daƙile ta'addanci da ƙarfafa wa hukumomin tsaro a jihar. Gwamnan, wanda…
Read More

2027: Ba sai ka zo kamfen ba, ba abokin hamayya a Kogi – Yahaya Bello ga Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai buƙaci yin kamfen don zaɓen 2027 a jihar Kogi ba. Da yake magana a ranar Asabar yayin taron jam’iyyar APC a Kogi, Bello ya ce jam’iyyar ba ta da kowace irin hamayya a jihar, wadda ke Arewa ta Tsakiya. Tsohon gwamnan ya bayyana jihar Kogi a matsayin garkuwa ga jam’iyyar mai mulki, yana mai cewa Shugaba Tinubu yana da gagarumin goyon baya daga jama’a a dukkanin sassan jihar. "Mai girma Shugaban ƙasa, ba ma sai ka zo jihar Kogi don yin…
Read More

Sanata Wamakko ya ba NABTEB kyautar babban ofishi a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Sakkwato ta Arewa a Majalisar Dattawa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bada kyautar ginin ofis ga Hukumar shirya jarabawar NABTEB, domin ƙarfafa ci-gaban ilimi da bunƙasa matasa a jihar. Sanata Wamakko, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙetare, ya miƙa ginin na bene ga Sakataren NABTEB, Dakta Aminu Muhammad, a yayin bikin ƙaddamarwa da aka gudanar a Birnin Sakkwato a jihar. Ƙaramin Ministan Ayyuka, Alhaji Bello Muhammad Goronyo ne ya wakilci Sanatan a wajen bikin, inda ya bayyana cewa…
Read More