19
Oct
Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta bada umarnin hana Omoyele Sowore, mai gidan jaridar Sahara Reporters, da wasu masu fafutuka yin zanga-zanga a wasu wurare a Abuja, ciki har da Fadar Aso Rock, domin neman a sako Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar IPOB da aka haramta. Mai shari’a Mohammed Umar ne ya bayar da wannan umarni a ranar Juma’a bayan lauyan ‘yan sanda, Wisdom Madaki, ya gabatar da ƙarar gaggawa a madadin Gwamnatin Tarayya (FRN). A cewar kotun, an haramta yin zanga-zanga a wurare kamar Aso Rock Villa, Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Hedikwatar ‘Yan Sanda, Kotun Daukaka Kara,…
