Babaji

5698 Posts

An sace wayar kwamishinan tsaro a taron tsaro na Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An zargi wani ɓarawo da sace wayar salular Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Barista Sule Shu'aibu (SAN). Al'amarin ya faru ne a yayin wani taro da ke da alaƙa da harkar tsaro a Kaduna, ranar Alhamis. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya auku ne a yayin da jama'a suka taru a wajen, lamarin da ya jefa alamar tambaya duk da matakan tsaro masu tsauri da aka ɗauka wajen ba taron kariya. Zuwa lokacin kammala haɗa rahoton, ba a samu bayani akan wanda ake zargin ba. Haka kuma, hukumomin jihar ba…
Read More

Za a riƙa yin sahihan zaɓuka a jagorancina, inji sabon Shugaban INEC, Amupitan

Sabon Shugaban Hukumar Zaɓe, Farfesa Joash Amupitan (SAN) ya yi alkawarin cewa a ƙarƙashin jagorancinsa za a riƙa shirya sahihi kuma karɓaɓen zaɓe a sassan ƙasar. Da yake jawabi bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi, Farfesa Amupitan ya kuma ce a wa'adin jagorancinsa zai tabbatar da cewa wanda ya faɗi zaɓe ya taya wanda ya yi nasara murna, saboda ingancin zaɓen. Ya ƙara da cewa zai yi aiki tare da sauran hukumomi, kamar hukumar bayar da katin ɗanƙasa (NIN), domin tabbatar da komai ya fi daidai. “Babban burinmu shi ne yin sahihai kuma ingantattun zaɓuka da kowa zai amince…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta musanta cire JAMB a sharuɗɗan shiga jami’a da wasu makarantu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ma’aikatar Ilimi ta fitar da sanarwar da ke musanta rahotannin da ke cewa gwamnati ta cire JAMB daga cikin sharuɗɗan samun gurbin karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu. Ma'aikatar ta bayyana cewa rahoton da ke yawo cewa daga yanzu ɗalibai za su riƙa samun gurbi a jami’a ba tare da JAMB ba ƙarya ne da aka ƙirƙira. Hukumar JAMB a ɗaya ɓangaren, ta nanata cewa tana nan a matsayin hukumar da ke da hurumin gudanar da jarrabawar shiga makarantu, kuma har yanzu ɗalibai suna buƙatar shaidar UTME domin neman gurbi a manyan makarantu.…
Read More

Miyetti Allah ta dakatar da jagororinta na Taraba, Bauchi da Adamawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Miyetti Allah ta dakatar da shugabanninta na jihohin Bauchi, Taraba da Adamawa bisa zargin su da gazawa wajen wakiltar makiyaya da rashin kula da walwalar mambobinta. A sanarwar da Kakakin ƙungiyar na ƙasa, Ambasada Mohammed Tasiu Suleiman ya fitar, dakatarwar ta biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da aka samu daga mambobin ƙungiyar a jihohin da lamarin ya shafa. Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Muhammad Hussaini Buzaye na Jihar Bauchi, Bammi Bello Jane na Jihar Taraba, da kuma Usman Abubakar Yirilabe na Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Abdullahi Bello Boɗejo, ya ce…
Read More

Kano: An yi taron inganta sana’o’in gargajiya a Ƙaramar Hukumar Bichi

Himma da hoɓɓasa ta Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na jihar Kano na cigaba da gudana a kowane fanni na bunkasa cigaban al'umma. Akan haka ne Karamar Hukumar Bichi ta yi gangamin taron zaburar da ma'abota sana'o'In gargajiya na ɗaukacin karamar hukumar. A wata sanarwa da Jami'ar Yada Labarai ta karamar hukumar, Jamila Abdullahi R/Lemo ta fitar, ta ce taron ya ƙunshi masu sana'o'i daban-daban da suka haɗa da; abinci, saka, rini, ƙira da kaɗe-kaɗen gargajiya da ake kira da Kalankuwa. Bisa wannan gagarumin biki na farfado da al'adu da sana'o'in gargajiya na faɗin jihar da gwamati ke ƙoƙarin yi, karkashin…
Read More

AU ta dakatar da Madagascar bayan juyin mulki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙasashen Afirka (AU) ta sanar da dakatar da Madagascar biyo bayan juyin mulki da sojojin ƙasar suka yi wanda ya hamɓarar da Shugaba Andry Rajoelina. Shugaban AU, Mahamoud Ali Youssouf ya tabbatar da haka ga kafar labarai ta AFP a jiya Laraba, inda ya ce hukuncin zai fara aiki ne a nan take. An ɗauki matakin ne bayan da wata tawagar manyan sojoji ta karɓe mulki jim-kaɗan da majalisar dokokin ƙasar ta tsige shugaban ƙasar. Babbar Kotun Madagascar tuni ta tabbatar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaba, lamarin da ya sauya…
Read More

NNPP ta yi wa siyasata ƙanƙanta, inji Farouk Lawan

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon ɗan Majalisar Wakilai kuma wanda ya samu yafiyar shugaban ƙasa a kwanan nan, Farouk Lawan, ya bayyana jam'iyyar NNPP a matsayin wadda ta yi wa siyasarsa ƙanƙanta, inda ya ce an fi saninsa da tafiyar siyasar da ta shahara a mataki na ƙasa. A wata hira da shi da BBC Hausa ranar Talata, Farouk Lawan ya ce ya fi ra'ayin haɗa hannu da jam'iyyu masu ƙarfi a mataki na ƙasa, a cewarsa, NNPP a Kano ma ba ta gama samun karɓuwa a wajen al'umma ba duk da cewa ita ke mulki a jihar.…
Read More

Matsin rayuwa ya kusa zama tarihi a Nijeriya, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya tabbatar wa al'ummar Nijeriya cewa ƙuncin tattalin da suka samu kansu a ciki na gab da zama tarihi yayin da ƙasar ke shiga sabon shafi na nasarorin harkar tattali da bunƙasarsa a ƙasar. Da yake jawabi a taron ƙungiyar harkar makamashi ta 'Renewable Energy Innovation Forum' (NREIF) a Abuja ranar Talata, Shettima ya ce zuciyar Shugaba Bola Tinubu tana tare ƴan Nijeriya da halin raɗaɗin da suke fuskanta sakamakon tsare-tsaren gwamnati. Mataimakin Shugaban ƙasar ya bayyana cewa, taron dama ce ta mayar da Nijeriya a matsayin fage na…
Read More

Abinda ya sa muka mayar da Sheikh Abduljabbar kurkukun Kuje – NCoS

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) reshen Jihar Kano, ta ce ta mayar da fursuna, Sheikh Abduljabbar Kabara gidan yarin da ke ƙarƙashin ikon tarayya ne saboda la'akari da tsare-tsarenta na gudanarwa. Jami'in hulɗa da jama'arta, CSC Musbahu Lawan Ƙofar Nassarawa ya faɗi haka a wata takarda, ranar Laraba. Ya bayyana cewa, sauya wa fursuna sheƙa daga wannan kurkukun zuwa wani ya danganta ne da matakin tsaro a wajen da aka ajiye shi, wanda kuma hakan yana ƙarƙashin dokokin hukumar gyaran 2019, kamar yadda ya shar'anta. Ya kuma ce, akan ɗauki…
Read More

Tinubu ya jajenta rasuwar Raila Odinga na Kenya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya miƙa gaisuwar ta'aziyyarsa ga gwamnati da al'ummar Kenya bisa rasuwar tsohon Fraministan ƙasar, Raila Odinga. A takardar da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a yau Laraba, Tinubu ya bayyana Odinga a matsayin ginshiƙi a siyasar Afirka. Ya kuma yaba da sadaukarwarsa ta tsawon lokaci ga harkar dimukraɗiyya, shari'a da haɗin kai, yana mai cewa ya bar tarin alkhairai a ƙasarsa Kenya da ma Afirka baki ɗaya. Haka kuma, ya jinjina masa bisa ƙoƙarinsa wajen kawo sauyi a harkar zaɓe musamman wajen shugabancin da ya bai wa al'umma muryar…
Read More