15
Oct
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban ƙungiyar jagororin matasan Arewa ta NNYLF, Kwamared Murtala Muhammed Gamji tare da sauran membobin ƙungiyar, sun yi gargaɗi da kuma bayyana rashin goyon bayansu ga yunƙurin neman a sako shugaban ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara, Nmadi Kanu daga wasu jagororin al'umma Nijeriya. A cewar Kwamared Gamji, tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jigo a jam'iyyar adawa, Alhaji Atiku Abubakar da ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ne suke shirya zanga-zangar neman sako jagoran Biafaran. Ƙungiyar matasan ta kuma yi watsi da masu kiran a sake shugaban ƴan tawaren na IPOB, Nnamdi Kanu. A yayin ganawa da…
