23
Oct
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ƙaryata rahoton wata jarida da ke ikirarin Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh ya sa an tsare editanta bisa wallafa labarin rashawa da aka danganta wa hukumar. A wata takarda daga mai taimaka wa Shugaban na NAHCON akan al'amuran gudanarwa, Ahmad Mu'azu, hukumar ta ce ta samu labarin na ƙarya da ake yaɗawa da nufin ɓatanci a gare ta da jagorancinta, lamarin da acewarsa, ba za su lamunta ba. An wallafa rahoton ne a ranar 21 ga watan Oktoba, 2025, wanda aka yi wa laƙabi da 'How NAHCON Chairman…
