Babaji

5700 Posts

Mayaƙan Lakurawa sun halaka ƴan sanda uku a Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yunƙuri na yin garkuwa da mutane a hanyar Zogirma zuwa Tilli dake Ƙaramar Hukumar Bunza ta Jihar Kebbi, mayaƙan ƙungiyar Lakurawa sun kashe jami'an ƴan sanda guda uku. Lamarin ya auku ne a lokacin da rundunar ƴan sanda a Zogirma ta samu labarin harin ƴan ta'addar, inda cikin hanzari ta tura jami'ai zuwa yankin tare da ƙarin dakaru daga babban ofishinsu dake Birnin Kebbi. Bayan musayar wuta da aka yi tsakanin ɓangarori biyun ne, ƴan sanda uku suka rasa rayukansu. A sanarwar da Kakakin ƴan sandan jihar, Nafi'u Abubakar ya fitar, ya…
Read More

Dukiyar Ronaldo ta ƙara hawa bayan samun mafi yawan mabiya a YouTube

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tashar YouTube ta shahararren ɗan wasa Cristiano Ronaldo, wato UR Cristiano, ta kere ta wasu manyan taurari irin su Justin Bieber da Taylor Swift wajen samun mabiya. Tun bayan buɗe ta a watan Agustan 2024, tashar ta karya tarihin da dama daga cikin tashoshi a kafar inda ta samu sama da mabiya miliyan 60 a ƙasa da wata guda da buɗe ta. A watan Yulin 2025 ne tashar ta tara mabiya sama da miliyan 75, lamarin da ya mayar da ita ɗaya daga cikin tashohi mafi samun yawan mabiya a duniya. Ana ganin hakan…
Read More

A Santiago Bernabeu za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030 – Rahoto

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta cimma yarjejeniya da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) bisa zama mai masauƙin baƙi wajen jagorantar wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na 2030. Marca ta ruwaito cewa an cimma yarjejeniyar tsakanin ɓangarori biyun ne a yayin ganawa da Shugaban ƙungiyar Florentino Perez da Shugaban FIFA Gianni Infantino a Amurka, inda ake gudanar da Kofin Duniya na ƙungiyoyi. Za a gudanar da wasannin Kofin Duniyar ne a ƙasashen Sifaniya, Portugal da Moroko, lamarin da ya zama na farko a tarihi da ƙasashe uku za su jagoranci gasar.…
Read More

Tinubu ba shi da ikon cire zaɓaɓɓen gwamna kamar yadda Shettima ya faɗa – Jam’iyyar ADC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar adawa ta ADC, ta yi tir da abinda ta kira da saɓa wa doka wajen tsoma baki a harkar siyasar Jihar Ribas, inda ta ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da iko a hukumance na cire zaɓaɓɓen gwamna. A sanarwar da ke ɗauke da sa hannun Sakataren yaɗa labaranta, Mallam Bolaji Abdullahi, ADC ta goyi bayan kalaman Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima na cewa Shugaban ƙasar ba shi da ikon cire ko da zaɓaɓɓen kansila ne daga muƙaminsa balle a ce gwamna. Duk da cewa Faɗar Shugaban Ƙasa ta yi ƙoƙarin fito da…
Read More

Majalisar Malmai ta shirya sallar roƙon ruwa a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta kirayi al'ummar jihar da su halarci taron gudanar da sallar roƙon ruwa da aka shirya, wanda za a yi a ranar Asabar. Za a yi sallar ne da nufin neman agajin ubangiji bisa rashin wadataccen ruwan sama a jihar kasancewar damina ta yi nisa. Shugaban Majalisar, Shaikh Ibrahim Khalil ya sanar da hakan a wata takarda, inda ya ce sun ɗauki matakin ne a sakamakon ƙarancin ruwan sama a wannan shekarar duk da ce yanayin damina ya yi nisa. Da misalin ƙarfe 9:00 na safe ne za a…
Read More

Jawabina ba shi da alaƙa da abinda ya faru a Ribas, tsohon tarihi na bayar – Shettima

Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana damuwa kan yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka juya maganganun Sanata Kashim Shettima da ya gabatar a lokacin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da littafin “OPL 245: The Inside Story of the $1.3 Billion Oil Block” a Abuja, ranar Alhamis. Sanarwar, wadda mai ba shi shawara kan harkokin labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, ta bayyana cewa jawabin Shettima na nuni ne zuwa ga tsohon tarihin matsalolin da ya fuskanta a lokacin yana gwamna a Borno sakamakon rikicin Boko Haram, ba wai yana tsokaci ne kan abubuwan da ke faruwa a Jihar Ribas ba.…
Read More

Gyaran matatun Nijeriya kamar sabunta mota ƴar shekara 40 ne, inji Ɗangote

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hamshaƙin Attajirin Ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Ɗangote ya koka game da makomar matatun gwamnatin Nijeriya, inda ya ce duk da Dala biliyan 18 da aka kashe wajen gyara su, ba lallai su koma aiki kamar yadda su ke a baya ba. Ɗangote a yayin ganawa da wata tawaga daga shirin 'Global CEO Africa Programme' naMakarantar Kasuwanci dake Legas, ya ce zai yi wahala matatun Fatakwal, Warri da Kaduna da ke ƙarƙashin kamfanin NNPCL su sake koma wa aiki yadda dace. Ya ce, an ɗauki shekaru ana ɓarnatar da kuɗaɗe domin dawo da martabarsu duk…
Read More

Boss Mustapha ya yi kuskure, Tinubu ya taimaka wa nasarar Buhari a 2015, inji Adamu Aliyu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗaya daga cikin daɗaɗɗun na hannun daman tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Farouk Adamu Aliyu, ya bayyana ƙin amincewarsa game da kalaman tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, kan matsayin Shugaba Bola Tinubu a nasarar Buhari ta 2015. A lokacin da ya ke magana yayin ƙaddamar da wani littafi a Abuja, Boss Mustapha ya ce lallai Tinubu ba shi ne silar zaman Buhari shugaban ƙasa ba. Ya ce, Buhari ya ci zaɓe ne bisa gudanarwa da ya samu na ƙuri'u miliyan 12, inda jam'iyyun da suka yi haɗaka suka samar da APC suka samar…
Read More

Rasha za ta ƙara adadin ɗaukar ƴan Nijeriya karatu kyauta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tarayyar Ƙasar Rasha ta amince da ƙara adadin bada gurbin karatu ga ɗalibai daga Nijeriya a kyauta daga guda 220 da ta saba zuwa sama a yayin da ta ke shirin cimma yarjejeniyar haɗin-gwiwa da Ma'aikatar Ilimi ta Ƙasa. An samu ci-gaban ne a yayin zama da wakilan ofishin jakadancin Rasha da Ma'aikatar Al'adu a Abuja, ranar Alhamis. Daga cikin ababen da aka tattauna akwai batun inganta matasa ta masana'antum ƙirƙira, musayar al'adu da haɗin-gwiwa ta fuskar tattali. Da ta ke jawabi, Ministar Al'adu, Walwala da Ƙirƙirarren Tattali, Hannatu Musa Musawa ta alaƙanta yawan…
Read More

Neja: An yanke wa ƴar aikatau hukuncin kisa bisa laifin kashe malamai jami’a

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotu a Minna, Babban Binta Jihar Neja, ta yanke wa wata yarinya mai suna Joy Afekafe hukuncin kisa bisa kashe Dakta Funkilayo Sherifat Adefolalu, wadda babbar lakcara ce a Jami'ar Fasaha (FUT) dake Minna. Mai Shari'a Mohammed Adishetu ta gabatar da hukuncin a ranar Laraba, bisa samun yarinyar da laifukan fashi da makami da kisa, waɗanda suna saɓa wa sashe na 221 da na 298 na kundin doka. Ta ce, a ranar 28 ga watan Oktoban 2023 ne aka halaka Dakta Adefolau a gidanta dake Gbaiko a Minna. Kotun ta ce, yarinyar…
Read More