Babaji

5701 Posts

Neja: An yanke wa ƴar aikatau hukuncin kisa bisa laifin kashe malamai jami’a

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotu a Minna, Babban Binta Jihar Neja, ta yanke wa wata yarinya mai suna Joy Afekafe hukuncin kisa bisa kashe Dakta Funkilayo Sherifat Adefolalu, wadda babbar lakcara ce a Jami'ar Fasaha (FUT) dake Minna. Mai Shari'a Mohammed Adishetu ta gabatar da hukuncin a ranar Laraba, bisa samun yarinyar da laifukan fashi da makami da kisa, waɗanda suna saɓa wa sashe na 221 da na 298 na kundin doka. Ta ce, a ranar 28 ga watan Oktoban 2023 ne aka halaka Dakta Adefolau a gidanta dake Gbaiko a Minna. Kotun ta ce, yarinyar…
Read More

Darakta-Janar na NITDA ya jagoranci shirin ‘Infinite Game’ na bunƙasa ci-gaban dijital a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Darakta Janar na Hukumar Ci-gaban Fasahar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NITDA) Kashifu Inuwa ya yi kira ga ƴan Nijeriya da masu-ruwa-da-tsaki da su kalli sauyin dijital da idon basira a madadin abinda taƙaice shi na ƙaramin lokaci. A lokacin da ya ke magana a taron Ranar Jagororin Kasuwanci karo na 13 da aka yi take da "Nigeria: From Reform to Recovery', Daraktan ya bayyana cewa kowace nasara da aka samu a yayin sauyi aba ce za a yi amfani da ita wajen samar da ci-gaban hark-ar tattali. Ya ce, tun daga samar da NITDA…
Read More

Yadda Adoke ya dakatar da Jonathan tsige ni a gwamnan Borno – Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa, saura ƙiris a cire shi a matsayin gwamnan Jihar Borno a zamanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Johnathan, inda ya yi nasarar tsira daga hakan ta hannun Antoni Janar na Ƙasa na lokacin, Mohammed Bello Adoke. Shettima, wanda ya yi gwamna a Jihar daga 2011 zuwa 2019 ya faɗi haka ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin taron gabatar da jawabin wata takarda da tsohon antonin ya rubuta mai suna 'OPL 245: Inside Story of the $1.3 Billion Nigerian Oil Block'. Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce,…
Read More

Ɓatar tiriliyan N200: Shugaban NNPCL ya sake ƙin amsa kiran Majalisar Dattawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da Majalisar Dokoki ta matsa wa Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) game da lamarin wasu maƙudan kuɗaɗe, a ranar Alhamis ne Shugaban kamfanin, Bayo Ojulari ya sake gaza amsa gayyatar Kwamitin Asusun Ƙasa na Majalisar Dattawa. Wannan shi ne karo na biyu da Ojulari ya ƙi zuwa zauren majalisar domin amsa tambayoyi akan Naira tiriliyan 200 da aka gaza bada gamsassun bayanai akansu acikin rahoton kuɗaɗe da kamfanin ya fitar. A madadin zuwa da kansa, Ojulari ya naɗa wata tawaga domin ta wakilce shi, inda Majalisar Dattawan ta ƙi sauraron su…
Read More

Tinubu ya aiki Shettima zuwa dubiyar Buhari a London

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana karɓar magani a wani asibiti dake London a Ingila, kamar yadda rahotanni da dama suka bayyana. Akan haka ne Shugaba Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima da ya je ya duba halin da tsohon shugaban ƙasar ya ke ciki. Muryoyi sun shaida cewa, an shirya tafiyar Shettima zuwa duba Buhari mai shekaru 81 ne a ƙarƙashin umarnin Shugaba Tinubu. Lamarin rashin lafiyar, wanda ba a bayyana asalin abinda ke damunsa ba, ya janyo hankulam al'ummar Nijeriya, lamari da ya sa ake cecekuce a kai. Saidai, makusantanasa sun…
Read More

Matsaya ta kan cecekucen karrama Rarara – Farfesa Abdalla

Ana ta cecekuce kan matsayata game da zuwa taron nazarin waƙoƙin Rarara.Na ga yadda na yamutsa hazo a kan ƙudirin ƙaddamar da gagarumin taro na nazarce-nazarcen waƙoƙin Dauda Kahutu Rarara. A sanarwar farko, cewa aka yi ni ne Baƙo Mai Babban Jawabi. Na ce ni ban san da maganar ba – hasali ma mutane ne suka riƙa aiko min da sanarwar domin tabbatar da ita. Da ya ke ba wani sahihin bayani da zan bayar, na ƙaryata shigata cikin lamarin. Daga baya Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, Katsina (FUDMA) inda aka ce za a yi taron, ta fito ta ce yadda…
Read More

Kotun Ƙoli ta tabbatar da Okpebholo a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Edo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis ne Kotun Ƙoli ta tabbatar da Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamna a Jihar Edo, lamarin da ya kawo ƙarshen shari'ar da aka ɗauki watannin a kai tun bayan zaɓen da aka gudanar a Satumban 2024. A wani hukunci na tawagar alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Mohammed Garba, kotun ta yi watsi da ƙarar da babbar jam'iyyar adawa (PDP) mai ɗan takara Asue Ighodhalo ta ɗaukaka a wajenta, tana mai cewa ta ɗauki matakin ne duba da cewa ƙarar ba ta da nagarta. Mai Shari'a Garba ya…
Read More

Ambaliya: Gwamnatin Jigawa ta ware biliyan N4.2 don agajin gaggawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta warware Naira biliyan 4.2 domin amfani da su wajen daƙile aukuwar ambaliyar ruwan sama da ayyukan bada agajin gaggawa ga iftila'in. Shugaban kwamitocin kula da lamuran agajin gaggawa a jihar, Dakta Abdullahi Sa'id ya faɗi hakan a yayin zama da masu-ruwa-da-tsaki game da lamarin a ranar Laraba, a garin Ringim dake Ƙaramar Hukumar Ringim a jihar. An gudanar da zaman ne a ƙarƙashin Hukumomin kula da muhalli da Bada Agajin Gaggawa na jihar duba da cewa jihar tana ɗaya daga cikin jihohin da ka iya fuskantar ambaliya, kamar…
Read More

Ƙungiyar Bura-Pabir ta buƙaci a kafa Jihar Savanna a Kudu maso Gabas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar al'ummar Bura-Pabir ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta fara aiki akan takardar buƙatar kafa Jihar Savanna kamar yadda al'ummar yankin tsohuwar Jihar Arewa maso Gabas suka buƙata. Masu neman a samar da jihar suna ganin yin hakan zai taimaka wajen haɗe mutanen yankin da ƴan uwansu barebari, waɗanda a shirye suke su ba su goyon baya a siyasance da ci-gaba. Dakta Yawutama Emmanuel Amaza shi ne wanda ya samar da ƙungiyar ta 'Bura-Pabir Network' da nufin fafutukar samar wa al'ummrsu jiha. A lokacin da ya ke magana game da…
Read More

‘Yan sanda sun kama mutum huɗu da hannu a harin Fadar Sarkin Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano, ta ce ta kama mutane huɗu da ake zargin su da hannu a tada rikicin da aka yi a Fadar Sarkin Kano a ranar Lahadi. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna ya tabbatar da hakan a wani saƙo da ya aika wa manema labarai, inda ya ce a halin da ake ciki jami'ai suna gudanar da bincike akan su. Ya bayyana cewa, Kwamishinan ƴan sandan, Ibrahim Adamu Bakori ya kafa tawagar bincike game da lamarin, wanda ya auku tsakanin magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da Sarkin Kano na…
Read More