28
Jan
Daga BELLO A. BABAJI Kwamishinan ƴan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya ce sun kama wani da ake zargi da kuma ƙwato wasu ababen fashewa, biyo bayan sanarwar mummunan hari da ka iya shafar al'ummar jihar. A yayin taron manema labarai, Kwamishinan ya zayyano matakan da ƴan sanda suka ɗauka don tabbatar da zaman lafiyar al'umma da kuma ba su kariya daga hare-hare. A ƴan kwanakin nan ne ƴan sandan suka fitar da sanarwar yiwuwar samun mummunan hari a lokacin gudanar da Maulidin Tijjaniyya da ya gabata a jihar da kuma ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan al'amarin.…
