Babaji

5707 Posts

Ƙungiyar ɗalibai ta bai wa Gwamnatin Tarayya kwana 14 ta gyara hanyar Numan-Jalingo

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS), ta bayyana hanyar Numan zuwa Jalingo a matsayin turken mutuwa, inda ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin mako biyu ta sake gina titin. Shugaban NANS na ƙasa, Mista Lucky Emonefe ya bayyana hakan a ranar Asabar a Jalingo yayin ƙaddamar da Majalisar Zartarwar ƙungiyar reshen Arewa maso Gabas, ya na mai gargaɗin matuƙar gwamnati ta gaza yin aikin hanyar, to za su gudanar da zanga-zanga. Ya kuma ce matuƙar gwamnati ta ƙi fara aikin hanyar har wa'adin da suka bayar ya ƙare, za su sauya sakatariyar ƙungiyar daga Abuja zuwa Arewa maso…
Read More

Ambaliya ce sababin koma-bayan ilimi a wasu jihohin Nijeriya – UNICEF

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Kamar yadda binciken UNICEF ya nuna, daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi sakamakon ambaliyar ruwan sama ta raba da muhallansu a ƙasashe 85 a duniya a shekarar 2024, ɗalibai miliyan 2.2 ne a Nijeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin karatukansu a shekarar da ta gabata kamar yadda rahoton ƙungiyar Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF ya bayyana. Da ya ke gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista…
Read More

Turji matsoraci ne, ya fito a yi gaba da gaba idan ya isa, inji Birgediya Janar Timothy

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Babban Kwamandan Runduna ta 1 ta sojojin Najeriya dake Gusau, Burgediya Janar Opurum Timothy, ya bayyana fitaccen shugaban ‘yan ta'addan nan Bello Turji a matsayin matsoracin da a kodayaushe ya ke ɓoyewa don tsoron hare-haren da sojoji ke kai wa a sansanin ƴan ta'addan da suka addabi yankunan Jihar Zamfara. Burgediya Janar Timothy ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai jim-kaɗan bayan kammala bikin ƙungiyar Sojojin Nijeriya ta West African Social Activities (WASA) na 2024 da aka gudanar a Gusau ranar Asabar. Burgediyan ya kuma ƙalubalanci jiga-jigan ƴan ta'adda musamman Bello Turji…
Read More

Cikin ƴan Nijeriya dake Amurka ya ɗuri ruwa bisa umarnin Trump na korar baƙin haure

Daga BELLO A. BABAJI Rahotanni sun nuna cewa baƙin haure a Amurka daga Nijeriya da wasu ƙasashen Afirka sune waɗanda gwamnatin ƙasar za ta kora nan ba da jimawa ba. Hakan ya haifar da tsoro acikin ƴan Nijeriyan da ke zaune a ƙasar, bayan da zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar, Donald Trump ya shelanta yaƙar baƙin haure da ke zama a Amurka ba bisa ƙa'ida ba. A ranar rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar na 47 ne Trump ya sanya hannu akan dokokin da ke tsawwala matakan zama a ƙasar, waɗanda daga ciki akwai batun hana zama ƴan ƙasa ga yaran…
Read More

Ku horar da matasan Igbo don yaƙar IPOB – Sheikh Gumi ga gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI Babban Malamin Addinin Islama a Nijeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya shawarci gwamnati da ta bai wa matasan Kudu-maso-Gabas horo ta yadda za su magance rikici Mutanen Biafra na IPOB. A wata hira da Blueprint, Sheikh Gumi ya ce mafi dacewar hanyar magance matsalolin ta'addanci a shiyyar ita ce bai wa matasan da suka san yadda yanayin ta'addanci ya ke a yankin horon da za su iya tunkararsa. Ya bada misali da Asari Dokubo da Tompolo a yankin Neja-Delta, waɗanda suka sauya daga ubannin daba zuwa masu kare harkokin gwamnati da yaƙar manyan ƴan ta'adda. Ya ce…
Read More

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya ƙi amincewa da buƙatar Bello Turji ta miƙa wuya

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya ce shahararren jagoran ƴan ta'adda, Bello Turji ya bayyana ƙudirinsa na son ya miƙa wuya sakamakon ƙarfin dakarun tsaro. Ya ce jami'an sojoji ba za su amince da buƙatar ba, ya na mai cewa za su cigaba da farautarsa har sai sun cim masa a maɓoyarsa. Janar Musa ya bayyana hakan ne a yayin hira da gidan talabijin ɗin channels a ranar Juma'a, inda ya ƙara da cewa tuni ɗan ta'addar ya sallami da dama daga cikin waɗanda ke ƙarƙashinsa. Rahotanni sun bayyana cewa sojoji sun yi…
Read More

Kwangilar Mambilla: Abubuwan da Obasanjo da Buhari suka faɗa a kotun Paris

Daga BELLO A. BABAJI A makon da ya gabata ne tsofaffin shugabannin Nijeriya, Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari suka faɗa wa Kotun Sasanci ta 'International Chamber of Commerce Court of Arbitration' dake Paris a Faransa cewa Gwamnatin Tarayya ta bada kwangilar Dala biliyan 6 ga Kamfanin Sunrise Power a Jihar Taraba don gudanar da aikin Wutar lantarkin Mambilla. Obasanjo da Buhari sun kare Nijeriya ne a ƙarar sasancin, wanda kamfanin da wanda ya samar da shi, Cif Leno Adesanya sukai shigar bisa zargin Gwamnatin Nijeriya da karya dokar kwangila. Kamfanin Sunrise ya ce ya na neman a biya shi kuɗaɗen…
Read More

Yadda Wike da Fubara suka basar da juna yayin ganawa da Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI An zargi manyan abokanan hamayya a rikicin siyasar Ribas, wato Ministan Abuja Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar da ƙin gaisawa da juna a lokacin da suka gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata. Jagororin biyu suna daga cikin tawagar Ogoni, wadda ta ziyarci Shugaban ƙasar don tattauna batun yiwuwar dawo da samar da mai a yankin 'Ogoniland'. Wata majiya daga zaman ta ce duk da cewa an hango sun ɗauki hoto da Shugaba Tinubu, amma ba su yi musabaha ko rungumar juna ba, kaɗai sun yi abinda ya kai su ne,…
Read More

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 79 da kwamandansu, Abu Mosaje

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Asabar ne Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce jami'anta a sassa daban-daban na ƙasar sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda guda 79 da kuma kama wasu 224. Ta kuma ce jami'ai a Rundunar Atisayen Arewa ta Tsakiya sun kashe sanannen Kwamandan ƴan bindiga mai suna Abu Mosaje a ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato. Daraktan Yaɗa Labarai na hedikwatar, Manjo-Janar Edward Buba ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jami'an sun kama wani shahararren mai garkuwa da mutane da ake kira Babangida Gora Usman a ƙaramar hukumar Sanga,…
Read More