Babaji

5707 Posts

Ƙungiyoyin Arewa da na ƴan gwangwan sun roƙi Wike ya dakata da rusau a kasuwar Fanteka

Daga BELLO A. BABAJI An bayyana rushe kasuwannin Fanteka a wasu yankunan birnin tarayya Abuja da Minista Nyesom Wike ke yi a matsayin amfani da laifin wani wajen ƙuntata wa wasu. Kodinetan ƙungiyar Arewa ta 'Arewa Renaissance Group', Umar Abba ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci wasu kasuwannin gwan-gwan da aka rushe su a unguwannin Deidei, Karmo, Kabusa da wasu wurare a babbar birnin. Ya yi magiya ga Minista Wike da ya dakatar da rusau da ya ke yi wa kasuwannin, inda ya ce hakan zai taimaka wajen samun ƙaruwar marasa aikin yi tare da ƙarfafa ayyukan sata…
Read More

‘Yan sanda sun fake da barazanar tsaro ne don su hana maulidi a Kano, inji Kwamishinan Labarai

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta zargi ƴan sanda da ƙoƙarin hana taron addini na ɗariƙar Tijjaniyya na shekara-shekara da ta saba yi, inda suka yi ƙaryar cewa akwai barazanar tsaro a jihar. Da ya ke jawabi ga manema labarai a Fadar Sarkin Kano a ranar Juma’ah, Kwamishinan yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya kuma musanta gargaɗin da ƴan sanda suka fitar tun da fari. Waiya ya ce rundunar ƴan sanda kawai ta fake da barazanar tsaro ne don ta hana gudanar da taron mauludin. Kwamishinan, wanda ya ce an kwashe kusan shekaru 40…
Read More

Tsofaffin janar na soji ke da hannu a haramtattun haƙar ma’adanai a Nijeriya, inji Majalisar Dattijawa

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattijawa ta yi zargin cewa wasu daga cikin jagororin sojojin da suka yi ritaya sune ke da hannu a gudanar da haramtattun haƙar ma'adanai a Nijeriya wanda hakan ke haifar da koma-baya ga faɗaɗa tattalin arziƙi a ƙasar. Shugaban kwamitin majalisar akan harkokin cikin gida, Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana hakan a lokacin da Shugaban kwamitin ci-gaban albarkatu na majalisar, Sanata Samson Ekong yake gabatar da kasafi ga kwamitin kasaftawa. Oshiomhole ya bayyana takaicinsa kan yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza ɗaukar mataki a kai, ya na mai cewa lallai sai gwamnatin Shugaba Tinubu ta yaƙi…
Read More

Sanarwar mummunar hari: ‘Yan sanda sun ankarar da mazauna Kano

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sandan Kano ta aika da saƙon ankarar da al'umma bayan samun wasu rahotonnin sirri game da wani shirin ta'addanci da ake zargin wasu ɓata-gari sun shirya don farmakar wuraren haɗuwar mutane a jihar. A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, an yi kira ga al'umma da su ƙaurace wa wuraren taruka da kuma kula da abubuwan da ke kai-kawo a yankunansu. Hakan wani salo ne da zai taimaka wa jami'an ƴan sandan wajen daƙile shirin ƴan ta'addar. Ya kuma ce an baza jami'ain kula da…
Read More

Abinda ya sa Asusun Tarayya zai raba kuɗin ƙananan hukumomi na Janairu ga jihohi

Daga BELLO A. BABAJI A halin yanzu Kwamitin Asusun Tarayya (FAAC) bai kai ga biyan kuɗin wata-wata kai-tsaye ga ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya ba, tun bayan ƴancin cin gashin kai da Kotun Ƙoli ta ba su a shekarar 2024. A jiya Alhamis ne aka gano cewa wa'adin da aka bai wa ƙananan hukumomin na su bada bayanan asusun bankuna ya cika. Wata majiya ta ce za a bai wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu ne ta hannun gwamnatocin jihohinsu. Majiyar ta ce za a bai wa Hukumar Ilimi na bai-ɗaya (UBEC) da rassan Cibiyar Kiwon lafiya (PHC) kuɗaɗensu kai-tsaye daga Asusun…
Read More

Ganduje da Gawuna sun samu muƙamai a sabbin naɗe-naɗe da Tinubu ya yi

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tawagar shugabancin hukumomin gwamnati na mutane 42 da kuma sakatare na rundunonin Civil Defense, Shige-da-fice da kuma Hukumar kula da Gidajen Yari. Shugaban ya kuma naɗa darakta-manaja a hukumar kula da Tashoshin Jiragen ƙasa da darakta-janar a Hukumar kula da Ci-gaban Fasaha (NBTI). Haka kuma Shugaba Tinubu ya umarci mambobin tawagar da kada su tsoma baki a harkokin gudanarwar hukumomin, ya na mai cewa muƙamansu ba na zartarwa bane. Ya kuma ce naɗe-naɗen zasu fara aiki a nan take. Blueprint ta ruwaito yadda shugaban ƙasar ya yi naɗe-naɗen da kuma guraben…
Read More

Gwamna Raɗɗa ya jaddada manufarsa ta tafiyar da gwamnati bisa gaskiya da amana

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya yi alƙawarin cigaba da tafiyar da gwamnatinsa bisa gaskiya da riƙon amana ga al'ummar jihar. Gwamnan ya faɗi haka ne a taron da ya yi da shugabannin ƴaƴan jam'iyyar APC daga matakin ƙananan hukumomi 34 da na jiha wanda ya wakana a gidan Gwamnatin jihar. Dangane da zaɓe mai zuwa na ciyamomi da kansiloli na ƙananan hukumomin jihar, Gwamna Raɗɗa ya umurce su da su wayar da kan al'ummar jihar akan su zaɓi APC. Ya kuma yi kira da waɗanda suka mallaki katin zaɓe da su yi amfani…
Read More

Ribaɗu ya ƙaddamar da kwamitin yaƙi da miyagun ƙwayoyi

Daga BELLO A. BABAJI Mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribaɗu ya ƙaddamar da shirin yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya. Hakan na zuwa ne bayan an kama fiye da kwantena 250 na haramtattun ƙwayoyi a wasu tashoshin jiragen ruwa na Najeriya. Kwantena 250 na ƙwayar Tramadol da wasu abubuwa masu haɗari aka kama a tashoshin ruwan Nijeriya, kamar yadda Blueprint Manhaja ta ruwaito. Lamarin da ya sa Mallam Ribaɗu ya ayyana yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar a matsayin barazana ga kwanciyar hankali da zaman lafiyar al'umma. An kafa kwamiti ne, wanda…
Read More

Tsohon Ministan Abuja, Janar Jeremiah Useni ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI A daren ranar Alhamis ne Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya tabbatar da rasuwar Laftanal Janar Jeremiah Tumbut Useni, mai shekaru 82 da haihuwa, bayan fama da wata jinya ta tsawon lokaci. A wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Gyang Bere ya fitar, Gwamna Mutfwang ya ce ba iya iyalan babban jami'in aka yi wa rashi ba, har da rundunar sojoji da ma ƙasa baki ɗaya. Gwamnan ya kuma ce irin jagorancin marigayin na jajircewa wajen yi wa ƙasa hidima abin koyi ne acikin al'umma, ya na mai cewa mutuwarsa ta bar giɓi a harkokin tsaro…
Read More

Zamfara za ta ƙaddamar da dokar kariya ga nakasassu da marasa galihu – Gwamna Dauda ga UNICEF

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, ya bayyana aniyar gwamantinsa ta ƙaddamar da dokar shirin bada kariya a jihar. A ranar Laraba ne gwamnan ya karɓi baƙoncin tawagar wakilan Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, (UNICEF) a Fadar gwamnatin jihar. A wata sanarwa da Kakakinsa Sulaiman Bala Idris ya fitar, wakilin UNICEF a Nijeriya, Cristian Munduate ya bayyana gamsuwarsa ga yadda jihar ta samu ci-gaba a ɓangaren bunƙasa harkokin kiwon lafiya. Sanarwar ta ƙara da cewa UNICEF, GAVI, WHO da wakilan ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) sun halarci zaman tattaunawa game da batun sanya dokar a…
Read More