23
Jan
Daga BELLO A. BABAJI Wasu ɗaliban makarantar Ebira Muslim Community College Okengwe (EMCCO) dake ƙaramar hukumar Okene a Jihar Kogi, sun farmaki wani malami mai suna Mista Muktar Salihu inda suka lakaɗa masa dukan kawo-wuƙa da ya kai ga an kai shi asibiti tare da kwantar da shi a ɗakin jinya na musamman. Ana zargin cewa ɗaliban ƴan ƙungiyar asiri ne kuma ƴan aji biyu a babbar sekandire. Lamarin, wanda ya haifar da damuwa acikin al'umma, ya faru ne a ƙoƙarin shirin ƙungiyar na mamaye kwalejin. Jaridar PeoplesPen ta ruwaito cewa an yi zargin wani mai suna Abdulbatin, wanda ɗa…
