Babaji

5707 Posts

Babban jami’in rediyon Freedom da Dala FM, Shehu Ɗalhatu ya rasu

Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un! Cikin alhini mu ke sanar da rasuwar ɗaya daga cikin daraktocin Hukumar Gudanarwar Rukunin Tashoshin Freedom Rediyo da Dala FM, Alhaji Shehu Ɗalhatu. Marigayin ya rasu ne a yammacin Jumu'ar nan a birnin Madina na ƙasar Saudiyya, inda aka bada umarnin yin jana'izarsa. Ana karɓar gaisuwa a gidan Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Dalhatu da ke Hotoro Kwanar Maggi, a Kano. Mu na addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma ba mu haƙurin jure wannan rashi. Sanarwa daga Hukumar Gudanarwa ta Freedom Rediyo.
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ceto matar da aka yi safarar ta daga Iraƙi

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a, 3 ga watan Junairu, 2025 ne wata ƴar Nijeriya mai suna, Eniola Isaac za ta dawo ƙasar bayan wakilan Nijeriya a Jordan sun shiga tsakani da ƙasar Iraƙi. Hakan na zuwa ne bayan wani rahoto da ke zargin cewa an yaudari matar ne mai shekaru 28 da cewa za a kai ta Iraƙi don samun rayuwa mai daɗi. Bayan ta sha duka da wasu nau'ukan wulaƙanci, sai Eniola ta koka ga hukumomin Nijeriya don su dawo da ita ƙasarta. Cikin wani rahoto da NiDCOM ya fitar a ranar Alhamis ta kafar X, ya…
Read More

Gwamna Ƙaura ya shiga tsaka mai wuya bayan kasafin biliyan N3.4 ga fetur da tafiye-tafiye

Daga BELLO A. BABAJI Jami'iyyar PRP reshen Bauchi ta yi tir da shirin Gwamnatin jihar da Majalisar Dokoki na kashe sama da Naira biliyan 3.4 ga sanya fetur a ababen hawa, janaretoci da tafiye-tafiye a shekarar 2025 a matsayin abin kunya da rashin iya sarrafa dukiyar al'umma. A cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakatarenta, Hon. Wada Abdullahi, jami'yyar ta ce lokaci ya yi da za a riƙa bibiyar masu riƙe da muƙaman gwamnati don tabbatar da cewa sun yi adalci a kowane mataki musamman ganin yadda al'umma suke fuskantar matsin tattali a jihar. Ta ce yayin…
Read More

Gwamnan Nasarawa ya sallami sakataren gwamnati da kwamishinoninsa

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rushe Majalisar Zartarwar Gwamnatinsa inda ya tsige sakataren gwamnati da ilahirin tawagar kwamishinoninsa. A ranar Juma'a, 3 ga watan Junairu ne gwamnan ya gabatar da hukuncin a yayin zaman Majalisar Zartarwa inda ya yi godiya gare su bisa ayyukan da suka yi wa gwamnati da mutanen jihar tare da musu fatan alheri. An umarci tsigaggun kwamishinonin da su miƙa harkokin ma'aikatun da suka yi wa aiki da kayan gwamnati ga manyan sakatarorin ma'aikatun. Haka nan shi ma sakataren gwamnati mai barin gado, ya miƙa ragamar aiki ga babban sakataren gudanar…
Read More

Zargin badaƙala: El-Rufa’i ya ziyarci tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatinsa a kurkuku

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya ziyarci Kurkukun Kaduna don ganin tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatinsa, Bashir Sa'idu da aka tsare. A ranar Litinin ne aka kama shi tare da kai shi wata kotun shari'a dake Rigassa wadda ta umarci a tsare shi a gidan yarin bisa zargin sa da hannu a badaƙalar wasu kuɗaɗe da ma wasu tuhume-tuhume. Rahotanni sun ce El-Rufa'i ya je gidan yarin ne tare da wasu tsofaffin kwamishinoninsa da suka haɗa da; Kwamishinan Ilimi, Jafaru Sani; Kwamishinar Ci-gaban Al'umma, Hafsat Baba; da kuma Ibrahim Hussaini wanda shi ne tsohon…
Read More

‘Yan sanda sun gano makamai masu linzami uku, sun hana fashewar bom a Borno

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an ƴan sanda a Borno sun gano wasu makamai masu linzami guda uku da kuma dakatar da fashewar bom a jihar. Kakakin ƴan sandan, Nahum Daso ya ce an gano makaman ne a yankin Dala Kafanti na Maiduguri, babban birnin jihar a ranar 2 ga watan Janairu, 2025. A ranar Alhamis ne wata mai suna Asabe James ta ruwaito wa hukumar ƴan sanda cewa ta ga wani buhu dake ɗauke da wasu ababen zargi a bayan gidanta inda rundunar ta aika da jami'an kula da ababan fashewa (EOD) zuwa yankin. Daga nan ne jami'an suka garzaya…
Read More

Kamfanonin waya sun nemi Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin kaso 100 na farashi

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanonin waya na Telecoms sun miƙa takardar buƙatar ƙara farashi ga Gwamnatin Tarayya da kaso 100. An miƙa kundin ne ga Hukumar Sadarwa ta NCC don warware matsalolin tashin farashin gudanarwa da hauhawar farashi da ƙarin adadin kashe-kashe. Shugaban Kamfanin MTN a Nijeriya, Karl Toriola ya faɗi hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, inda ya ce babu tabbas kan cewa ko NCC za ta amince da buƙatar. Ya ce yana da muhimmanci su ƙara farashin kasancewar kamfanonin suna fuskantar matsalolin hauhawar farashin gudanarwa yayin ayyukansu. Ya kuma ce duk da…
Read More

‘Yan Sanda a Katsina sun kuɓutar da mutane 361 daga komar ƴan ta’adda

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda a Jihar Katsina sun yi nasarar kuɓutar da mutum 361 daga hannun yan ta'adda a shekarar 2024. Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da hakan a lokacin da ya ke wa manema labarai bayanin nasarorin da rundunar ta samu acikin shekarar. Ya ce mutanen tuni aka miƙa su ga iyalan su yayin da suka kashe ƴan bindiga 40 a wurare daban-daban a faɗin jihar. "Mun kuma samu nasarar kama ɓarayin shanu guda 81 da gano shanu da suka sata guda 2081." Har'ilayau, jami'an ƴan sandan sun kama yan fashi da makami…
Read More

Tsohon ɗan majalisa daga Zamfara, Ahmad Bakura ya koma APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon ɗan Majalisar Wakilai wanda ya wakilci ƙananan hukumomin Bakura da Maradun na Jihar Zamfara, Hon. Ahmad Muhammad AA Bakura tare da ɗaruruwan magoya bayansa sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC. Da ya ke jawabi ga magoya bayansa, Hon. Bakura ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda rashin gaskiya da adalci wajen gudanar da mulki a Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal. Hon. Bakura ya bayyana rashin tsaro da ya addabi jihar sakamakon hareharen ƴan ta'adda a matsayin abin da ya shafi gwamnatin jihar, yana mai kokawa da halin ko in…
Read More

Gwamnatin Katsina za ta kashe biliyan N1 a gyaran KTTV

Dakta Bala Salisu Zango Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Bayanin ya fito ne daga bakin kwamishinan yaɗa labarai da aladu na jihar, Dakta Bala Salisu zango a yayin bikin ƙarshen shekara da gidan talabijin na KTTV ya shirya wa ma'aikatansa. Bala zango ya ce gwamnati ta sanya kuɗin ne a kasafin kuɗinta na shekarar 2025 da Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya sanya hannu. Kwamishinan ya yaba da jagorancin babban Manajan gidan talabijin ɗin, Abba Zayyan kan gagarumin ci-gaba da aka samu a wajan shirye-shirye da kula da jin daɗin ma'aikatan KTTV. Ya kuma yi kira ga ma'aikatan da su tashi…
Read More