Babaji

5707 Posts

Tsofaffin ɗaliban Pilot Daura ajin 2010 sun gudanar da taron sada zumunci da taimakon juna

Daga RABIU SANUSI Tsoffin ɗaliban makarantar sakandire ta Pilot dake Daura a Jihar Katsina, ajin shekarar 2010 sun gudanar da taron ɗabbaƙa zumunci da taimakon juna. Taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na farfajiyar makarantar dake Ganga a Garin Daura, ya samu halartar da yawa daga cikin mambobin ɗaliban. Da yake jawabi, ɗaya daga cikin shugabannin riƙon ƙwarya, Yusuf Muhammad Sadau ya bayyana irin jin daɗinsa bisa yadda aka samu amsa wannan katin gayyata cikin ƙanƙanin lokaci da aka bayar. Sadau ya ce sanin kowa ne cewa babu al'ummar dake samun cigaba sai sun samu haɗin kai. Ya ce…
Read More

Gwamnan Kano ya rattaɓa hannu a kasafin kuɗin 2025

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rattaɓa hannu kan Kasafin kudinshekarar 2025 dan inganta rayukan Al'ummar Jihar Kano. Gwamna Abba Kabir ya ce wannan kasafin kuɗi zai taimaka matuka wajen cimma Muradun da za su kawo ma jihar Kano cigaba matuka dan samun saukin rayuwa ga musamman Al'umma matasa masu tasowa. Haka kuma Gwamnan yana fatan wannan kasafin kuɗi zai ƙara bunƙasa hanyoyin samun damar bijiro da ayyuka kamar a bunƙasa harkokin Ilimi da Noma. ''Haka kuma muna fatan wannan Kasafin kudi zai taimaka wajen samar da Ayukan yi ga jama'ar Jihar Kano…
Read More

Zubairu Balannaji ya lashe gasar gajerun labarai ta Gwamnatin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta Jihar Kano ta ayyana Zubairu Musa Balannaji a matsayin wanda yazo na farko a gasar gajerun labarai ta shekarar 2024 Da ya ke bayyana sakamakon gasar a ɗakin taro na Malam Aminu Kano da ke Mumbayya a Birnin Kano, shugaban kwamitin alƙalan gasar, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, ya bayyana labarin 'Bahaushiyar Al'ada', wanda Marubuci Zubairu Musa Balannaji ya rubuta a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya zama na farko cikin labarai 50 da suka fafata a cikin gasar. Kazalika, ya bayyana labarin 'Gadon gida saida Horo' wanda…
Read More

Mun hallaka ƴan bindiga 40 da kama masu aikata manyan laifuka 916 a 2024 – Kwamishinan ƴan sandan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Kwamishinan ƴan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Musa, ya ce jami'an rundunarsu sun kashe ƴan bindiga 40 acikin shekara guda. Kwamishinan ya kuma bayyana cewar, an kama masu aikata laifuka 916 tare da ceto mutane 319 da aka yi garkuwa da su a cikin lokacin. Kwamishinan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da ya ke bayyana irin nasarorin da rundunar ta samu shekarar 2024. “Ina so in tabbatar da jajircewar da aka yi na yaƙi da laifuka da rundunarmu ta yi cikin wannnan shekara, jajircewar da muka yi ta haifar da raguwar…
Read More

Masarautar Fika da ke Potiskum ta yi naɗe-naɗen sarautu

Daga BELLO A. BABAJI Mai martaba Sarkin Fika kuma Shugaban Majalisar Sarakunan gargajiya ta Jihar Yobe, Alhaji Dakta Muhammad Ibn Abali Muhammad (CON, CFR), ya umarci a sanar da ƙarin girma da naɗin wasu daga cikin muƙarrabansa. Mutanen sune; Air Komodo Ibrahim Alƙali (rtd) daga Galadima zuwa Madakin Fika; sai Ali Adamu Fika wanda aka naɗa a matsayin Wazirin Fika; sannan Alhaji Ali Gimba Fika daga Sakataren riƙon ƙwarya zuwa Sakataren Majalisar Masarautar Fika. Wata takarda da Sakataren masarautar, Ali Gimba Fika ya fitar a ranar 30 ga watan Disamba, 2024, ta ce tuni mutanen da aka naɗa suka kama…
Read More

Tinubu ya amince da gina jami’ar tarayya a Kudancin Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya amince da buƙatar samar da jami'ar tarayya a Kudancin Jihar Kaduna, kamar yadda Mataimakinsa, Kashim Shettima ya faɗa. Shettima ya bayyana hakan a lokacin da ya je gaisuwar ta'aziyyar rasuwar Agwom Akulu na Masarautar Ikulu wanda kuma ɗan uwa ne ga Bishop Matthew Hassan Kuka. Ya kuma ce ana tattaunawa game da samar da asibitin tarayya (Federal Medical Center) a Kafanchan dake Kudancin jihar. Ya jaddada ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Tinubu na samar da ci-gaba ga yankin, yana mai bada misali da naɗa Janar Christopher Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaron Nijeriya la'akari…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Matatar Warri ta fara aiki

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanin tace dangogin mai na Warri (WRPC) dake Jihar Delta ya fara aiki. Shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari ya bayyana hakan a yau Litinin, a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a matatar. Ya ce duk da cewa ba a kai ga kammala aikin 100 bisa 100 ba, amma an fara ayyukan tace mai. Ya kuma tabbatar wa masu kokwanto game da aikin matatar kan cewa tabbasa abu ne mai yiwuwa ba kamar yadda su ke ɗauka ba na rashin yiwuwar sa. Hakan na zuwa ne makonni kaɗan bayan matatar…
Read More

Shugaban Amurka na 39, Jimmy Carter ya rasu

Daga BELLO A BABAJI Tsohon Shugaban Amurka, Jimmy Carter, wanda ya shahara da ayyukan jin-ƙai ya rasu bayan shafe shekaru 100 a duniya. Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi, a jihar Georgia bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci. Gabannin mutuwarsa, Charter ya ƙudirin aniyar kaɗa wa ƴar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2024 Kamala Harris ƙuri'a. Carter ya shugabanci Amurka ne daga shekarar 1977 zuwa 1981 inda ya rasa damar komawa zango na biyu bayan ya sha kaye a hannun Ronald Reagan. Ya kuma samu kyautar 'Nobel Prize' a shekarar 2002.
Read More

An tsaurara tsaro akan iyakar Najeriya da Nijar kan ƙishin-ƙishin ɗin harin Lakurawa

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an tsaro sun tsaurara matakan kariya akan iyakar Najeriya da Nijar kan samun labarin harin mayaƙan Lakurawa musamman a yankin Sakkwato. Jami'an Hukumar shige da fice (NIS) sun tabbatar wa al'umma cewa kada su ɗaga hankulansu domin sun ɗauki matakan kariya ga shigowa Najeriya ta haramtattun hanyoyi da nufin haddasa fitina. Wani jami'in hukumar ya tabbatar wa manema labarai cewa NIS da haɗin-gwiwar wasu hukumomi suna aiki tare don shawo kan kowacce matsala da za ta gitta ta kan iyakar. Haka kuma hedikwatar hukumar dake Abuja, kamar yadda wata majiya ta nuna, ta tabbatar da cewa…
Read More

Sojoji sun kama masinjan harsasan ƴan bindiga a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Dakarun Birget ta ɗaya, tawaga ta 2 a atisayen 'Fansan Yamma', sun kama wata ‘yar shekara 25 mai suna Shamsiyya Ahadu ɗauke da harsashi na musamman samfurin 764mm 7.62mm da kuma kenson harsasai Gida shida (Magazine 6) a yunƙurin ta na kaiwa sansanin ‘yan ta’addan Bello Turji. Kodinetan Joint Media Coordinating Center Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Gusau, inda ya ce an kama Shamsiyya ne a ranar 28 ga watan Disamba, 2024 tare da abokinta, wani direban babur mai suna…
Read More