29
Jan
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu a shirye take wajen haɗe kai da gwamnonin ƙungiyar yankin Tafkin Chadi da wasu masu-ruwa-da-tsaki wajen kawo zaman lafiya mai ɗorewa a yankin wanda mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka jima suna addabar sa tsawon shekaru. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana hakan a yayin taron ƙungiyar karo na 5 da Gwamnatin Jihar Yobe ta jagoranta a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. An gudanar da taron ne musamman don tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, haɗin kai tsakanin yankunan iyakoki da ci-gaba da aka samu da kuma rashin daidaito da…
