Babaji

5707 Posts

Atiku ya zargi Tinubu da ƙaddamar da yaƙi kan ƴan adawa

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jami'yyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da ƙarfin mulki wajen ƙaddamar da yaƙi kan ƴan ɓangaren adawa. A wani saƙo da aka wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya yi alla-wadai da kama Farfesa Usman Yusuf, mai sharhi akan al'amuran yau da kullum, ya na mai cewa an siyaysantar da kama shi duk da cewa akwai zargi akansa da ya samo asali daga gwamnatin da ta gabata. Ya ce gwamantin Tinubu tana tafiya ne da waɗanda akwai zarge-zarge akansu daga hukumomin cikin gida da na…
Read More

Daga Fabrairu ƴan hidimar ƙasa za su riƙa karɓar N77,000 – Darakta-Janar na NYSC

Daga BELLO A. BABAJI Darakta-Janar na Hukumar kula da ɗaliban da ke yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Yusha'u Ahmed ya sanar da cewa a watan Fabrairu, 2025 ne ƴan hidimar ƙasa za su fara karɓar alawus ɗin N77,000 a madadin N33,000 da aka saba biyan su. A ranar Alhamis ne Daraktan ya bayyana hakan a Katsina, a lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga ƴan zangon 'C' 2024, ɗiba na biyu. Ya ce an sanya karin kuɗaɗen ne a kasafin kuɗin 2025 na Gwamnatin Tarayya waɗanda za a fara biya da zarar an tabbatar da shi. Ya…
Read More

Harin jirgin ƙasa: Na biya N80m ta hannun Tukur Mamu don sako mahaifiyata da ƴan uwana – Shaida

Daga BELLO A. BABAJI Wani shaida da iftila'in harin jirgin ƙasa na shekarar 2022 a hanyar Abuja-Kaduna ya rutsa da shi, ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya dake Abuja cewa Naira miliyan 80 ya bai wa ƴan ta'adda a matsayin kuɗin fansa ga mahaifiyarsa da ƴar uwarsa. A ranar Alhamis, Mai Shari'a Inyang Ekwo ya gabatar da sauraron ƙarar da aka shigar akan Tukur Mamu, wanda shi ne mai magana da yawun waɗanda suka yi garkuwa da mutanen inda ake tuhumar sa da laifuka 10. Shaidar ya ce an sako mahaifiyarsa da ƴar uwar tasa ne tare da wasu mutum…
Read More

Sarkin Yaƙin Zazzau ya yanke jiki ya faɗi, ya rasu ana tsaka da taro

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Alhamis ne lamarin ya auku da ɗaya daga cikin mambobin Majalisar Masarautar Zazzau mai suna Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, wanda ya rasu a yayin da aka garzaya da shi asibitin Gambo Sawaba dake Zaria, Jihar Kaduna. A wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ofishin jami'in hulɗa da jama'arta, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ta koka game da rashin Sarkin Yaƙin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate. Marigayin, wanda ya kuma taɓa riƙe muƙamin Mai kula da lamuran da suka shafi kiwon lafiya, ya rasu a yayin da ake tsaka da gudanar da wani taro a kusa…
Read More

Mu na godiya ga Ƙungiyar Gwamnonin Arewa bisa kwaskwarima da suka yi wa ƙudirin gyaran haraji – Dakta Lajada

Daga BELLO A. BABAJI Wani ɗan kishin ƙasa mai suna Dakta Ibrahim Abubakar Lajada, ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya na goyon bayan yin kwaskwarima ga ƙudirin gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya samar. Dakta Lajada, wanda ya yi watsi da matakin da gwamnonin suka ɗauka a baya, ya bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na ciyar da harkokin kuɗin, daidaito da kuma ci-gaban tattalin arziƙin ƙasar. Ya yi tsokaci kan amincewar da gwamnonin Gyaran Haraji suka yi a baya-bayan nan, inda ya yaba da hasashen da ƙungiyar ta yi na amincewa da tsarin rabon harajin…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi adana ababen fashewa don haramtaccen haƙar ma’adanai

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Yaɗa Labarai da Wayar kai, Alhaji Mohammed Idris ya gargaɗi mutanen da ke ajiye ababen fashewa a gidajensu domin yin ayyukan haƙar ma'adanai ta haramtattun hanyoyi. A wata sanarwa da Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rabi'u Ibrahim ya fitar, Ministan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, a yankin Sabon Pegi na Jihar Neja a lokacin ya je gaisuwar ta'aziyyar waɗanda suka rasa rayukansu a yayin fashewar wani abin fashewa a ranar Litinin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane da dameji ga wasu ababe. Ministan ya ce ajiye ababen fashewa don haƙar…
Read More

Dokar Haraji: CNG ta nemi mahukunta su kiyayi masu son zuciya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Ƙungiyar Gamayyar Al'ummar Arewacin Najeriya (CNG) ta ƙalubalanci ƴaƴan majalisun dokoki na tarayya da cewa duk waɗanda suka ƙi bayar da gudunmawar da ta dace wajen yin fatali da tanaɗe-tanaɗen son zuciya da ke cikin dokoki na sauya fasalin haraji da Shugaban ƙasa ya ƙiƙira, su kwana da sanin sun zalunci ƙasa. Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi a wata ganawa da manema labarai a garin Bauchi, ya ce babu wani dalili a yanzu da al'umma ta ke ɗanɗana wahalhalun rayuwa ace za a ƙara kuɗaɗen haraji, yana mai cewa wannan ƙudirorin na…
Read More

APC ta kori tsohon gwamnan Osun, Aregbesola kan zagon-ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Jam'iyyar APC ta tabbatar da korar tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola daga jami'yyar bayan zargin sa da yi mata zagon-ƙasa. Aregbesola tsohon ministan harkokin cikin gida kuma jagoran ƙungiyar ƴaƴan jam'iyyar mai suna Omoluabi Caucus a jihar, wadda aka zarge ta da taimaka wa rashin nasarar da jam'iyyar ta yi a zaɓen gwamnan Osun a shekarar 2022. A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar a mataki na ƙasa, ta tabbatar da kokar ɗan siyasar bayan saɓa wa dokar jam'iyyar ta matakan ladabi ga mambobi. Tuni dai jami'yyar NNPP ta nemi Aregbesola da ya shigo cikinta…
Read More

Jami’an tsaro sun karɓe Sakatariyar PDP bayan rikici ya ɓarke a zaman Hukumar Amintattu

Daga BELLO A. BABAJI A sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin Samuel Anyanwu da Ude-Okoyes kan tabbatar da sahihin Sakataren PDP na ƙasa, jami'an tsaro sun karɓe ragamar kula da Sakatariyar jami'yyar. Jami'an sun haɗa da sojoji, ƴan sanda, jami'an tsaro na ƙasa da na Civil Defense. Rikicin ya soma ne a lokacin da Anyanwu da Ude-Okoyes suka halarci zaman Hukumar Amintattun (BoT) ta jami'yyar, inda wani mataimakin Samuel Anyanwu ya Ude-Okoyes da ƙarfi daga wajen taron jim-kaɗan bayan wata ganawar sirri. Lamarin da ya haifar da hatsaniya tsakanin ɓangarorin biyu, wanda har ya kai ga jami'an tsaro sun shiga…
Read More