26
Jun
Daga Adnan Muktar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya biya kuɗin hayar gida ga Zainab, ƴar marigayi tsohon Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da mahaifiyarta, biyo bayan barazanar korar su daga gidan da su ke da aka yi a Legas. Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya ziyarci wajen da su ke a rukunin gidajen 'Morning Side Suits' da ke Victoria Island a ranar Talata, 25 ga watan Yuni, 2024 which a ranar ƙudinsu zai ƙare da misalin ƙarfe 3 na rana inda har ta kai ga an basu takardar ficewa daga gidan, wato 'notice', sannan ya gana…
