Babaji

4778 Posts

Zafin rana ya sa an taƙaita huɗubar sallar juma’a a Saudiyya da Dubai

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙasashen Saudiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sun sanar da rage adadin lokacin gudanar da huɗubobin sallar jumma'a a masallatai saboda tsananin zafin rana da su ke fama da shi. Al'ummar musulmi a ƙasashe da dama na duniya kan gabatar da sallar jumma'a ne da rana wacce masallata ke zama domin sauraron ta ciki da wajen masallaci da wuraren da babun rumfuna, don haka ƙasashen biyu suka yanke hukuncin hakan domin sauƙaƙa mu su kamar yadda addinin Musulunci ya karantar. Shugaban ma'aikatar kula da harkokin addini na ƙasar Saudiyya ya ce, sun rage adadin lokacin huɗubar zuwa…
Read More

Wike zai tashi kasuwar ‘Mechanic Village’ zuwa Wassa

Daga KHADIJA ABUBAKAR Majalisar kula da ayyukan birnin tarayya, AMMC ƙarƙashin ofishin ministan Abuja, Nyesom Wike, ta ce za ta sauya wa makanikai da ƴan kasuwan kan hanya na 'Mechanic Village' dake yankin Apo wajen aiki zuwa Wassa. Sanarwar ta fito ne daga shugaban Majalisar, Felix Obuah a wata hira da manema labarai bayan ganawa da wikilan makanikan da na ƴan kasuwan da abin ya shafa, a ranar Talata. Obuah, ya ce Wike ya tabbatar da aikin wanda aka shirya shi musamman don ƴan kasusuwar kan hanya da makamantansu kuma ya ce za'a fara korar su nan da wata ɗaya…
Read More

El-Rufai ya karɓi baƙuncin Kwankwaso kwanaki bayan kai wa Buhari ziyara

Daga FAROUK ABBAS Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya karbi baƙuncin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a gidansa da ke Abuja a ranar Alhamis, kwanaki kaɗan bayan kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ziyara a Daura, Jihar Katsina. A ƴan kwanakin nan ne El-Rufa'i na jam'iyyar APC, ya yi ta ganawa abokanan hamayyarsu na siyasa ciki har da ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma ziyartar shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa a Abuja da ya yi. El-Rufa'i, wanda tsohon ministan Abuja ne, na ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa za a basu muƙaman…
Read More

Ƙananun ma’aikatan gidan yari sun koka kan dokar sabon kaya a jarrabawar ƙarin girma

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙananan jami'an hukumar gidajen yari ta NCS, sun koka kan yadda ta gagara raba musu sabon kayan sa wa na hukumar a kyauta bayan bai wa manyan jami'anta. Jami'an sun ce abun da ya ƙara dagula lamarin shi ne yadda hukumar ta sanya mallakar sabon kayan a matsayin ɗaya daga cikin rukunan jararbawar ƙarin girma da ta yi, wanda za'a gudanar daga ranar 1 zuwa 6 ga watan Yuli, 2024. Wani jami'i da bai yadda a faɗi sunansa ba, ya ce a ayyukan da ake sanya inifom, a kan bai wa manyan jami'ai kyauta, amma ƙananan…
Read More

Tinubu ya amince da bayar da tallafin 50,000 ga magidanta 100,000 na tsawon watanni uku

Daga KHADIJA ABUBAKAR Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da shirin gina ƙasa da tallafawa magidanta a yayin wani zama da Majilisar kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasa, NEC a Abuja. Wani jawabi da ya fito daga ofishin mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya ce manufar shirin su ne dan a inganta harkokin noma da tattalin arziƙi gami da bada tallafi domin rage raɗaɗin talauci ga ƴan Najeriya. Shirin wanda ya samu goyon bayan Majalisar ta NEC, ya ƙunshi rarraba kuɗaɗe da yin ayyukan more rayuwa a dukkan shiyyoyin ƙasarnan guda shida, inda za a bada tallafin Naira…
Read More

Mutum biyu sun kamu da kwalara a Katsina, 118 kuma na karɓar kulawa

  Daga Naziru Adam Ibrahim Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina, ta ce an tabbatar da cutar kwalara ta kama mutum biyu a ƙaramar hukumar Kusada, da ke jihar tare da wasu 118 da a ke binciken lafiyarsu. A cewar hukumar, tuni an ɗauki matakan fara amfani da tsarin kula da al’amuran da ke faruwa domin hana yaɗuwar cutar da sauran cutukan da za a iya rigakafinsu a jihar. Daraktan kula da cutuka na hukumar, Dakta Kabir Sulaiman, a wani taron manema labarai a cibiyar bayar da agajin gaggawa ta hukumar, ya bayyana cewa gwamnatin…
Read More

Rikicin Masarauta: Aminu Ado ya ɗaga tuta a fadar Nasarawa

Daga Sadiq Yayin da ake tsaka da rikicin masarautar Kano, Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya ɗaga tutar mulki a ƙaramar fadar da ke Nassarawa inda hakan ke nuna iko da Sarkin yake da shi a yanzu. A bisa al’ada, tutar na zama ne a matsayin alamar iko, kuma ɗaga ta na alamta cewa sarki yana cikin fada. Hakan kuwa na zuwa ne duk da umarnin gwamnatin Kano ga Sarki Aminu na ya fice daga fadar a yayin da ake cigaba da dambarwar sarautar Kano. Akan ɗaga tutar ce da misalin karfe 6 na safe a kuma sauke…
Read More

Majalisar Wakilai ta umarci a kama daraktan kwalejin koyon tuƙin jirgi kan sayar da helikwaftan Dala 1.2

Daga Farouk Abbas Kwamitin kadarorin ƙasa na Majalisar wakilai ya buƙaci hukumomin tsaro da su gaggauta kama daraktan kwalejin koyon tuƙin jirgin sama da ke Zariya kan sayar da helikwafta guda biyu a dala miliyan 1.2. Kwamitin ya yi kira ga sufeta Janar na Rundunar Ƴan sanda, Kayode Egbetokun da ya yi bincike kan sayar da helikwaftocin da aka yi ba bisa ƙa'ida ba. Shugaban kwamitin, Ademorin Koye, yayin wani dogon zama da wakilan hukumar kwalejin, ya nuna damuwa kan lamarin inda ya bukaci a yi bincike. An sayo jiragen kan dala miliyan 2.4 yayinda aka ce an sayar da…
Read More

El-Rufa’i ya shigar da Majalisar Dokokin Kaduna ƙara kan badaƙalar Naira biliyan 432

Daga BALA MUHAMMAD Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya shigar da Majalisar Dokokin Jihar ƙara kan kuɗi da adadinsu ya kai naira biliyan 432 da suka zargi gwamnatinsa da sauya akalansu. El-Rufa'i ya shigar da ƙarar takardar nuna ƴancinsa da ke ƙalubalantar zargin shi da cin hanci da kwamitin Majalisar ta yi a babbar kotun tarayya da ke Kaduna. Lauyansa Abdulhakeem Mustafa (SAN) shi ya jagoranci shigar da ƙarar inda a ciki El-Rufa'i ya buƙaci kotun da ta yi watsi da rahoton kwamitin majalisar da ke tuhumarsa da gwamnatinsa da cin hanci, ganin cewa ba a bashi damar…
Read More

Zamfara: ’Yan bindiga sun sake kai hari masallaci, sun kashe mutum biyu da yin garkuwa da wasu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A safiyar ranar talata ne ƴan bindiga suka kai hari wani masallaci a ƙauyen Tazame da ke ƙaramar Bungudu a Jihar Zamfara. Jaridar 'PRNigeria' ta ruwaito cewa an kai harin ne a lokacin da mutane ke ƙoƙarin gudanar da sallar asuba yayinda ƴan bindigar suka buɗe wuta wa masallata inda suka kashe Ladanin masallacin da ɗan uwansa tare da raunata Limamin. Baya ga haka ne, sun kuma yi garkuwa da wasu da dama daga cikin masallatan. A ƴan kwanakinnan, ƴan bindiga sun kai hare-hare da dama wa masallatai da yin fashi a shaguna gami da garkuwa…
Read More