01
Jul
Daga FAROUK ABBAS Kwamishinan lafiya na Jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya ce sun samu rahoton mutane 25 da ake zargin suna ɗauke da cutar ƙwalara daga gidan yarin Kirikiri. Hakan na zuwa ne bayan da hukumar kula da gidajen yari (NCS) ta fitar da bayanin cewa babu mai ɗauke da cutar a gidan kurkukun a makon da ya gabata. Mai magana da yawun hukumar, Abubakar Umar ya ce sun ɗauki matakan kariya wajen ganin ba a samu ɓullar kwalara a gidan yarin ba. Sai dai, ma'aikatar lafiya ta jihar Lagos ta offishin jami'in hulɗa da jama'a, Tunbosun Ogunbawo ta…
