03
Jul
Daga EDITA Majalisar wakilan Nijeriya ta gabatar da ƙudurin ƙirƙiro ƙarin jiha guda da za a kira jihar Etiti a yankin kudu maso gabashin ƙasar. Ƙudirin, wanda Amobi Godwin Ogah tare da wasu ƴan majalisa huɗu suka gabatar, ya tsallake karatu na farko a majalisar ranar Talata. Ƙudurin na buƙatar yin gyara a sashe na uku na kundin tsarin mulkin ƙasa, domin goge lamba ta 36 tare da maye gurbinta da lamba 37 don bai wa sabuwar jihar damar shiga jerin jihohin ƙasar, sannan a saka Etiti bayan Enugu cikin jerin sunayen jihohin ƙasar. Sabuwar jihar da za a yanka…
