Babaji

4782 Posts

EFCC ta tsaurara tsaro a Abuja, Legas da Ibadan bisa shirin yi wa hukumar zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), ta ɗauki matakin tsaurara tsaro a ofisoshinta da ke Abuja, Lagas da Ibadan, babban birnin jihar Oyo, biyo bayan raɗe-raɗin cewa an shirya za a yi mata zanga-zanga a ranar juma'a 5 ga watan Yuli. Jaridar 'The Nation' ta ruwaito cewa, a jihar Legas, an sanya wasu jami'an hukumar tare da 'Yan sandan farin kaya na DSS a dukkan hanyoyin da za su kai zuwa ofishinta da ke hanyar Awolowo a ƙaramar hukumar Ikoyi. Haka nan a jihar Oyo, wani mai suna Steve ya sanya a shafinsa…
Read More

Sarki Sanusi ya yaba wa Gwamnan Kano bisa bai wa ‘yan fansho da ilimin yara mata muhimmanci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya jinjina wa gwamna Abba Kabir Yusuf kan warware matsalolin biyan ƙuɗaden fansho da kuma bada muhimmanci ga ilimin yara mata. Sanusi ya yi hakan ne la'akari da yadda mutane da dama suka shiga matsanancin rayuwa da talauci wanda rashin biyan su kuɗaɗensu na fansho da giratuti ya zama dalilin samun kansu a wannan hali. A kwanakin baya ne, gwamnan ya sa a ka ware Naira biliyan 11 domin biyan waɗanda ke karɓar kuɗin fansho ciki har da waɗanda aka riƙe mu su na tsawon lokaci, inda Sarkin ya yaba…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta dakatar jirage masu zaman kansu 10

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da harkokin jirage masu zaman kansu (NCAA), ta dakatar da zirga-zirga da ayyukan wasu jirage guda 10 biyo bayan da su ka gaza sabonta tantancewarsu daga gare ta. Wata sanarwa da NCAA ta saka a shafinta na 'Twitter' wanda ke ɗauke da sa hannun daraktanta kan hulɗa da jama'a da kula da abokan hulɗa, Micheal Achimugu, ta ce ta bayar da umarni ga waɗanda ke mallakan jirage domin amfanin kansu da su sake zuwa a tantance su wanda wa'adin hakan ya kamata a ce ya ƙare tun ranar 19 ga watan Afrilu, 2024. Achimugu…
Read More

Tinubu da wasu manyan ƙasashe sun taya Starmer murnar lashe zaɓen Birtaniya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da wasu shugabannin ƙasashe sun taya Sir Keir Starmer na jam'iyyar Labour murna, biyo bayan nasarar da ya samu a babban zaɓen da aka gudanar a ƙasar Birtaniya. Nasarar da Starmer ya samu, ta sa zai zama sabon firaministan ƙasar bayan da Rishi Sunak ya shafe shekaru 14 a kan kujerar. Tuni dai Rishi ya amince da faɗuwa a zaɓen bayan shan kaye da ya yi da rinjaye mai yawa. A lokacin da ya ke jawabi cikin wata sanarwa, mai taimaka wa shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya…
Read More

Bulalar malamar makaranta ta yi sanadiyyar mutuwar wani ɗalibi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukuma ta tsare wata malamar makaranta a jihar Anambara sakamakon mutuwar wani ɗalibinta ɗan kimanin shekara 8. Malamar mai suna Faith Nwoye, ta kasance mai koyarwa ce a Landmark International School da ke Mbakwu a ƙaramar hukumar Akwa ta Arewa a jihar, wacce ta zane Henry Okonkwo da bulala wanda daga bisani ya mutu. Ganin haka ke da wuya, sai a ka shigar da ita ƙara a wata kotu da ke aiki kan lumuran da suka shafi mata da yara inda a nan a ka yanke hukuncin tsare ta a gidan gyaran hali. An shigar da…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Ban taɓa kwana a gidanki ba – Martanin Alƙali Ɗandago ga Sadiya Haruna

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wani tsohon Alƙali a Kano mai suna Muntari Ɗandago, ya musanta kalaman wata sananniyar mai harkar kayan mata kuma tsohuwar tauraruwa, Sadiya Haruna inda ta ce ya kan ziyarci gidanta akai-akai domin cin abinci da kuma kwana. Ya ce, kalaman nata yunƙuri ne na masa sharri da kuma ɓata masa suna bayan ko shi mutumin kirki ne a idon jama'a. A watan Fabrairun 2022 ne Ɗandago a matsayinsa na Alƙali a wata Shari'a da ya jagoranta, ya yanke wa Sadiya hukunci zaman gidan yari na wata shida kan samun ta da laifin ɓata wa tsohon mijinta,…
Read More

‘Yan bindiga sun ƙi sakin ƴaƴan alƙalin da aka sace a Kaduna bayan sun sako ta

Daga BALA MUHAMMAD An sako Alƙalin da aka yi garkuwa da ita tare da 'ya'yanta huɗu a Kaduna, Janet Gimba a watan da ya gabata. Sai dai ƴaƴanta uku har yanzu ba su dawo gida ba kamar yadda mijinta, Musa Gimba ya tabbatar. Ya ce, ƴan bindigar suna gargaɗin cewa a biya Naira miliyan 150 nan da kwana uku ko kuma su kashe su. A ranar 24 ga watan Yuni, 2024 ne aka yi garkuwa da matar wacce ke aiki a reshen Sabon Tasha na babbar kotun jiha tare da ƴaƴanta huɗu a gidansu da ke yankin Mahuta a ƙaramar…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta hana lauyoyi hira da ‘Yan jarida kan rikicin Masarautar Kano

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata babbar kotun Jiha a Kano ta fitar da umarni da ke hana lauyoyi amsa tambayoyin Ƴan jarida kan rikicin Masarautar Kano. Mai Shari'a, Amina Adamu Aliyu ce ta faɗi haka a yayin wani zaman kotu da ta jagoranta kan batun a ranar Alhamis. A ranar 25 ga watan Mayu, 2024 ne Antoni Janar na Kano da Kakakn majalisar jihar da kuma majalisar dokokin Jihar suka shigar da wata takarda da ke ƙunshe da ƙwance rawanin Sarki Aminu Ado Bayero da sarakunan Bichi, Rano, Gaya da kuma na Ƙaraye Kano. Mai Shari'ar, ta ce umarnin zai…
Read More

Naira 400,000 ne albashina lokacin Ina Kakakin Majalisa – Dogara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon Kakakin Majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya ce Naira dubu ɗari huɗu a ke biyan sa duk wata a lokacin da ya ke shugabantar majalisar, saɓanin yadda a ke ta yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa maƙudan kuɗaɗe ƴan majalisu ke ɗauka a matsayin albashi. Dogara, wanda shi ne Kakakin a majalisa ta takwas (daga 2015, zuwa 2019), ya faɗi haka ne a zauren Majalisar da ke Abuja yayin jawabin fatan alkhairi ga ƴan majalisu a bikin satin majalisar ƙasa. Ya ce, kuɗin albashi da alawus ɗin da ya ke karɓa sun kai jimillar Naira miliyan…
Read More

Harin Gwoza: Red Cross za ta taimaka wa asibitin Maiduguri

Daga EDITA Tawagar Likitoci daga ƙungiyar agaji ta 'International Committee of the Red Cross' (ICRC), za ta tallafa wa likitocin asibitin Maidugiri wajen yi wa mutanen da harin ƙunar baƙin wake a Gwoza ya afka mu su magani. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce tawagar ƙwararrun likitocin nata za ta yi aiki da likitocin asibitin koyarwa na birnin Maiduguri wajen ceto rayukan mutanen da harin ya yi musu mummunar illa. Mutane da dama ne suka samu munanan raunuka a lokacin harin da wasu ƴan ƙunar baƙin wake suka kai garin Gwoza a ƙarshen makon da ya gabata.…
Read More