08
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI 'Yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da sace wasu ƴan jarida biyu tare da iyalansu da aka yi a ranar Asabar da misalin ƙarfe 10:30 na dare. Mai magana da yawun rundunar Mansir Hassan ya faɗi hakan a yayain wata hira da 'News Agency of Nigeria' inda ya ce jami'ansu na ƙoƙari wajen ganin an ceto su daga waɗanda suka yi garkuwa dasu wanda a yanzu haka an watsa tawagar ƴan sandan a yankunan da ake tsammanin suna nan. Mansir ya ce, ɗaya da cikin su shi ne Abdulgafar Alabelewa, shugaban wakilan 'Chapel' na ƙungiyar ƴan…
