Babaji

4782 Posts

Bishiyun shekara 100 sun faɗo sun kashe ƴan kasuwa huɗu a Edo

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu bishiyu uku a kasuwar Jattu dake ƙaramar hukumar Etsako ta yamma a jihar Edo, sun yi sanadiyar mutuwar mutum huɗu bayan da suka faɗo a kan ƴan shan inuwa da masu shaguna. Wani adadi da ba a tantance ba na mutane sun samu raunuka a yayin aukuwar ibtila'in. Blueprint ta ruwaito cewa yayinda ake ruwan sama da misalin ƙarfe takwas na safe, masu saye da sayarwa sun fake a ƙarƙashin rumfunan bishiyun inda aka yi wani tsawa da ya yi sanadiyar faɗuwarsu wanda a sakamakon haka ne aka rasa rayukan. Wani mai suna Sule, ya…
Read More

Gwamnan Zamfara ya yi shiru kan rahoton damfarar sa jirgin Dala miliyan 6.3

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A jiya Litinin ne, wata jarida mai suna 'People's Gazette' ta ruwaito cewa wasu ma'aurata sun damfari gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawan kuɗi da adadinsu ya kai Dala miliyan 6.3 kan cinikin jirgi mai tashin angulu. Kasancewar labarin na cigaba da yaɗuwa musamman a kafafen sada zumunta, kawo yanzu ba'a samu wani jawabi daga gwamnatin jihar kan batun wanda idan ƙarya ce, wakilan jaridar gwamnatin za su gaggauta yin gamsashshen bayani a kai domin kiyaye suka daga suka daga ƴan adawa. Sannan, shuru da gwamnatin ta yi, mai yiwuwa akwai ƙamshin gaskiya a cikin rahoton wanda…
Read More

A dakatar da Yarjejeniyar Samoa har sai hankali ya kwanta – Majalisar Wakilai

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Majalisar Wakilai ta buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da batun zartar da yarjejeniyar Samoa har sai abubuwa sun lafa. Majalisar ta yanke hukuncin ne sakamakon kiran gaggawa kan lamarin wanda ya shafi ƙasa da wasu ƴan majalisu 88 suka yi. A lokacin da yake magana kan batun, ɗan majalisa Aliyu Madaki ya yi ƙarin haske kan sakin layin da ke magana a kan 'gender equality', wato 'a samu daidaiton jinsi' inda ya ce wannan ka iya cin karo da al'adun ƴan Nijeriya. Majalisar ta kuma yi kira ga kwamitin da ke da alhakin shiga batun da…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Ƙungiyar lauyoyi ta ce babu maganar amince wa auren jinsi a Yarjejeniyar Samoa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA), ta ƙaryata rahotannin da ke cewa Nijeriya ta rattaɓa hannu kan ciyo bashin Dala biliyan 150 wanda ya ƙunshi amince wa tare da halasta auren jinsi a ƙasar. Wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun shugaban ƙungiyar, Yakubu Maikyau, ta ce ba a samu daidaito tsakanin yarjejeniyar da dokokin Nijeriya ba wanda akwai batun haramcin auren jinsi a cikin kundi na 2023. Maikyau, ya ce ƙungiyar da ta shawarci Nijeriya kan sanya hannun matuƙar akwai dokar da ta ci karo da dokokin Nijeriya. Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta…
Read More

‘Yan sanda sun kama wanda ya yi yunƙurin kashe kansa a Abuja saboda tsadar rayuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar 'Yan sanda a Abuja, ta kama wani mai suna Shuaibu Yusuf sakamakon hawa hasumiyar gidan radiyon Aso da nufin faɗowa ƙasa saboda tsadar rayuwa. A ranar Litinin ne mutumin wanda ɗan Maiduguri ne a jihar Borno, ya kwashi ƴan kallo a lokacin da ya hawu ƙolin hasumiyar da ke dutsen Katampe inda ya sha alwashin faɗowa ƙasa matuƙar gwamnatin tarayya ta ƙi dawowa da tallafin da ta cire. Sanadiyar haka, 'Yan sanda na tsare da shi bayan da ya karɓi rarrashin Darakta Janar ta offishin bada agaji ta gaggawa (FEMD), Florence Dawon Wenegieme inda ta…
Read More

Tsawa da walƙiya ne suka haifar da ƙarancin fetur, inji NNPC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC), ya ce layukan gidajen mai da al'umma ke fuskanta musamman a jihohin Legas da Abuja na faruwa ne sakamakon sauyin yanayi da ake ciki. Wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun babban jami'in hulɗa da jama'a na kamfanin, Olufemi Soneye da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, ta ce shiga sauyin yanayi ya haifar da matsalar layin mai domin hakan ya shafi shirya manyan motocin da ke raba man da kuma safararsu wanda hakan ya sa aka samu ragowar samar da isasshen man fetur ga jihohin. Sanarwar ta…
Read More

Ahmad Musa ya yi tsokaci kan ajiye aiki da Super Eagles

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ya warware batun cewa ya yi murabus daga buga wa ƙungiyar wasan. Musa bai buga wasa ko ɗaya ba ciki wasannin 7 da Super Eagles ta yi a gasar kofin Nahiyar Afirka da aka buga na wannan shekarar inda ta ƙare a ta biyu. Ahmed Musa, wanda tsohon ɗan wasan gaba na Leicester City ne, ya buga wasa na ƙarshe daga farkonsa ne wa Super Eagles tun a shekarar 2021, a wani wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya da Nijeriya ta yi da ƙasar Cape Vade wanda ta yi…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori ƙarar shuwagabannin ƙananan hukumomi na ɓangaren Wike

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kotun ɗaukaka ƙara reshen jihar Ribas, ta kori ƙararraki biyu da shuwagabannin ƙananan hukumomi da ke ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike suka shigar bayan da ta ce ba su cika ƙa'idojin sauronsu ba. Hon. Enyiada Cookey-Gam da wasu mutum shida suka shigar da su masu ɗuake da lambobi kamar haka; CA/PH/137M/2024 da kuma CA/PH/145M/2024 inda a ciki su ke ƙalubalantar karamar kotu kan hukuncinta na ƙara wa'adin shugabancin majalisar da suka nema. Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce ƙalubalen nasu basu gamsar da tsare-tsaren doka ba don haka, ta yi watsi da su. Ɗaya daga cikin…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Yadda ƴan majalisa na ɓangaren Fubara da na Wike ke mabambantan zama a Ribas

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ana cigaba da dambarwar siyasa jihar Ribas yayinda ɓangarori biyu na majalisar dokokin jihar ke gudanar da mabanbantan zama a ranar Litinin. A ranar Lahadi ne ƴan ɓangaren gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ƙarƙashin jagorancin Victor Oko-Jumbo na majalisar, suka gayyaci Emmanuel Frank Fubara domin tantance shi a matsayin wanda za bai wa muƙamin kwamishina kuma ɗaya daga cikin mamba majalisar zartarwa ta jihar. Sai dai, a gefe guda, ƴan majalisu da ke ɓangaren tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, ƙarƙashin jagoranci Martin Amaewhule za su yi nasu zaman a rana ɗaya da ƴan Fubara.…
Read More

Badaƙalar biliyan N80.2: EFCC ta gano shirin Yahaya Bello na ficewa daga Nijeriya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), ta ce gano shirin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello na ficewa zuwa ƙasar Maroko daga Kamaru sakamakon zargin badaƙalar biliyan N80.2 a kan sa. Tsohon gwamnan wanda akwai batutuwa 19 na laifuka da ake zargin sa da aikatawa cikin har da badaƙalar kuɗi, zamba cikin aminci da kuma sauya akalan waɗansu kuɗaɗe da adadin su ya kai kimanin Naira biliyan 80.2. Duk da cewa ya musanta aikata laifukan, gwamnan ya ƙi amincewa a lokuta mabanbanta ya bayyana a gaban Alƙali Emeka Nwite. A ranar 27 ga…
Read More