13
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata ƙungiya mai suna 'Birnin-Gwari Vanguard for Security and Good Governance' da ke jihar Kaduna ta yi kira ga gwamnatin jihar da sauran masu-ruwa-da-tsaki da a rushe kwamitin riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Birnin-Gwari tare da ɗora zaɓaɓɓen ɗan takara. Ƙungiyar ta yi hakan ne bayan da kotun ƙoli ta yanke hukuncin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi inda ta ce naɗa kwamitin riƙon ƙwarya da gwamnatin Kaduna ta yi a Birnin-Gwari ya ci karo da sakin layi na 7 a kundin shekarar 1999 na dokar ƙasa kamar yadda kotun ƙoli ta tabbatar. Wata takarda da…
