16
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin ƙirƙirar Majalisar Masarautu da zai bada damar samar da wasu Masarautun bayan da ƙudirin ya tsallake dubiya ta uku a ranar Talata. Ƙudirin, wanda mataimakin kakakin majalisar, Muhammad Bututu Bello da ke wakiltar Rimin Gado/Tofa ya jagoranta ya bayyana samar da Masarautar Kano a matsayin mai daraja ta ɗaya, sai Masarautun ƙananan hukumomin Rano, Gaya da Ƙaraye a matsayin masu darajoji na biyu-biyu. Sarakunan Masarautun masu daraja ta biyu za su ke biyayya ga Sarkin Kano sannan suna da ikon bashi shawara kan kula da zaman lafiyar al'umma…
