19
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Babbar kotun tarayya da ke jihar Legas ta kori ƙarar da cibiyar tabbatar da ƴanci da adalci (SERAP), ta shigar wanda ke ƙalubalantar umarnin ofishin shugaban ƙasa na cewa a rufe layukan da ba a sadar da su da lambobin katin ɗan ƙasa ba (NIN). Mai Shari'a Yelim Bogoro ya ce tsarin gwamnatin tarayya da ya buƙaci sadar da layuka da lambobin katin ɗan ƙasa ya tabbatar da cewa maslahar ƙasa amfani ne gare ta, don haka tana sama da dukkan ƴancin kowaye a ƙasar. Waɗanda takardar ƙarar ta zayyano sun haɗa da; shugaban ƙasa, Antoni…
