23
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sakamakon rashin cike ƙa'idojin babbar kotun jihar Kano da hukumar hana yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa, EFCC ta yi, an samu tsaiko kan sauraron ƙarar da aka shigar kan kare ƴancin shugaban jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai. Jaridar 'Daily Trust' ta ruwaito cewa, waɗanda su ka shigar da ƙarar sun haɗa da; NNPP, Dakta Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Cif Clement Anele, Ledi Folshade Aliu, Buba Galadima da kuma Rabi'u Musa Kwankwaso kan hukumar EFCC. A yayin da aka tada batun, lauyan da ya karɓi shigar da ƙarar, Robert Hon,…
