Babaji

4788 Posts

Da ƊUMI-ƊUMI: Obama ya goyi bayan Kamala Haris ta zama Shugabar Amurka

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama, ya goyi bayan ƴar takara Kamala Haris ta yi nasara a zaɓen shugabancin ƙasar da ke tafe bayan da shugaban Joe Biden ya ƙudiri aniyar janyewa daga tsayawa takara. Sanarwar ta fito ne a ranar Juma'a, kwanaki kaɗan da Kamala ta shelanta tsayawarta takarar kujerar shugabancin ƙasar. Wata ɗaukar bidiyo, ta nuna yadda Obama ya kira ta a waya, yana mai cewa shi da matarsa, Michelle suna goyon bayan ta tare yi mata alƙawarin samun gudunmawarsu ga kai wa nasararta. 'NBC News' ta ruwaito cewa, kasancewar Obama shi ne baƙin…
Read More

Ƙungiyoyin Islama sun buƙaci a hana ɗaukar sanya hijabi da sunan fashi a cikin fina-finai

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƴancin al'ummar musulmi (MURIC) da cibiyar lamuran al'ummar musulmi (MPAC) sun buƙaci a ɗauki tsauraran matakai ciki har da dakatar da wani fim da ke nuna mata sanye da niƙabi ɗauke da muggan makamai suna fashi a bankuna da laifuka masu kama da haka. Jawabin ya fito ne daga mabanbanta ofisoshi a ranar Alhamis da su ka haɗa da Daraktan MURIC, Farfesa Isiaq Akintola da shugaban MPAC, Disu Kamor. A kwanan nan ne tauraruwar masana'antar 'Nollywood', Nancy Isime ta yaɗa hotunan ɗaukar fim ɗin da ake shirin fito da shi a yanar gizo waɗanda su…
Read More

Ba ni da iyayen gida da zan sakawa, Inji Tinubu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kore zargin cewa ya na da waɗanda su ka dafa masa cikin ɗaiɗaikun mutane ko kuma wata ƙungiya a siyasarsa, yayin da ake cigaba da daidaita al'amuran tattalin arziƙi, ya ce shi ya ɗauki nauyin yawon neman zaɓensa ba tare da taimakon wasu mutane ko ƙungiyoyi ba. Tinubu wanda ya karɓi baƙoncin malaman addinin Islama ƙarƙashin jagorancin Sheikh Bala Lau a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis, ya ce nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa iko ne na Ubangiji da kuma shiri na tsanake tare da samun goyon bayan ƴan Nijeriya. Shugaba Tinubu…
Read More

Nijeriya ta sayo man fetur ɗin Dala 2.25bn daga Malta, kwanaki kaɗan da Ɗangote ya zargi akwai ma su ɓoyayyun masana’antun mai a ƙasar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwanaki kaɗan bayan da shugaban matatar mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yi zargin cewa akwai jami'an kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC da ke da ɓoyayyun masana'antun mai a ƙasar Malta, alƙaluma sun bayyana cewa Nijeriya ta sayo man fetur na tsabar kuɗi da adadinsa ya kai Dala biliyan 2.25 daga ƙasar. Wata sanarwa daga 'Trade Map', ta ce a shekarar 2023, Nijeriya ta shigo da man fetur na Dala biliyan 2.8 wanda hakan ya haura da kashi 342 a kan na Dala miliyan 47.5 da aka sayo a shekarar 2013. An gano cewa,…
Read More

Zanga-zangar Tsadar rayuwa: Ƙungiyar matasa ta umarci rassanta 104 su kasance a shirye

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A cigaba da shirye-shiryen zanga-zangar tsadar rayuwa da za a yi a watan Agusta, Ƙungiyar matasa ta ƙasa, NYCN ta umarci ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin ta da su kasance cikin shiri ganin cewa kwanakin na ƙara kusantowa. Sanarwar ta fito daga shugaban ƙungiyar, Sukubu Sara-Igbe Sukubu cikin wata takarda da ya fitar biyo bayan wani taron gaggawa da shugabannin rassan ƙungiyar na Jihohi 36 suka gudanar ta kafar Zoom a rana Alhamis inda ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda al'ummar Nijeriya ke fama da matsanancin rayuwa musamman matasa. Cikin matsalolin da matasan ke buƙatar gwamnati ta…
Read More

A na zargin Matawalle da taimaka wa Yahaya Bello wajen tserewa zuwa Nijar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A na zargin ƙaramin ministan tsaro, Muhammed Bello Matawalle da shirya ficewar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da ake zargi da sama-da-faɗi da dukiyar al'umma daga Nijeriya zuwa Jamhuriyar Nijar da taimakon jami'an tsaro. Wani ɗan jaridar bincike mai suna Jackson Ude ya faɗi haka ta kafar X a ranar Alhamis. Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati, EFCC ta na tuhumar Yahaya Bello da aka zarge shi da handame sama da Naira biliyan 80 a lokacin da ya ke gwamnan Kogi inda ya yi ta ƙoƙarin kaucewa kamawa da kuma bincike. Ɗan jaridar…
Read More

Gwamnatin Tinubu ta yi barazanar garƙame mahandaman shugabannin ƙananan hukumomi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi barazanar gudanar da bincike kan shugabannin ƙananan hukumomi da su ka sauya akalan kuɗaɗen asusun ƙasafi na ƙasa (FAAC). Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya faɗi hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin taron ƙungiyar Marubuta Ƴancin Ɗan-adam inda ya ce duk wanda aka samu da laifin handame ƙuɗin ƙaramar hukuma, to za a kulle shi a kurkuku. Idan ba a manta ba, a ranar 11 ga watan Yuli ne kotun ƙoli ta yi hukuncin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi inda…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: DSS ta sako matasan da ta kama kan shirin zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴan sandan farin kaya ta DSS, ta sako Injiniya Khalid Aminu da Sanusi Aliyu waɗanda ta kama su a kwanakin baya kan zargin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi wa laƙabi da 'EndBadGovernance'. Sanarwar haka ta fito daga Omoyele Sowere, ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar AAC a zaɓen 2023 a wani rubutu da ya yi a kafar sadarwa. An kama Khalid ne a safiyar ranar Alhamis don zargin gayyato mutane shiga zanga-zangar gama-garin a jihar Kaduna, yayin da a irin haka aka kama Sanusi a ranar Talata a jihar Sakkwato, 23 ga watan Yuli. Rahotanni…
Read More

Zanga-zanga: Masu amfani da wayoyi da motoci ake hari, DHQ ta gargaɗi al’umma

Daga BALA MUHAMMAD Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), ta ce ta gano wani shiri da wasu ɓata-gari ke yi na kai hari wa masu motoci da masu amfani da manyan wayoyi da kuma mallakar wasu kadarori a cigaba da shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar 'EndBadGovernance' a za a yi wata mai zuwa. A ranar Alhamis ne, Daraktan ofishin kan harkokin yaɗa labarai, Manjo Janar Edwerd Buba ya faɗi haka a yayin ganawa da manema labarai a Abuja inda ya ce sun gano akwai maƙarƙashiya da ka iya haifar da tarzoma a lokacin zanga-zangar, yana mai cewa mutane da dama na goyon…
Read More

Ajaero ya bayyana matsayar NLC kan zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ta musanta batun cewa ta janye daga zanga-zangar tsadar rayuwa da ake shirin yi faɗin Nijeriya, ta na mai cewa ba ta ɗaya daga cikin waɗanda su ka shirya ta. Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ya bayyana haka cikin wata takarda da ƙungiyar ta fitar a ranar Talata, inda ya ce ba za su janye daga zanga-zangar da ba su suka tada batunta ba. Ya ce ƙungiyar tana da tsarinta na cikin gida game da yin hukunci kan ababan da su ka shafi al'umma cikin har da zanga-zanga. Ya ƙara da cewa…
Read More