27
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake cigaba da shirin zanga-zanga a faɗin Nijeriya, lauyan kare ƴancin Ɗan Adam, Inibehe Effiong ya aika da saƙo ga Sufeto Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun inda ya buƙaci a bai wa masu zanga-zangar kariya. Effiong ya ce zanga-zangar lumana a dokar Nijeriya ta halatta, dan haka akwai buƙatar hukumomin tsaro su ba su kariya, ya na mai kafa hujja da sakin-layi na 39 da na 40 na kundin dokar ƙasa. Ya ƙara da kira ga Sufetan, ya umarci dukkan kwamishinoni da ɓangarorin da ke da alhakin bayar da tsaro ga al'umma domin…
