Babaji

4788 Posts

Yaran Nijeriya sun roƙi Tinubu ya dakatar da zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga KAHLID IDRIS DOYA a Bauchi Ƙungiyar yaran Nijeriya, NCCF sun koka wa Shugaba Tinubu kan cewa ya ɗauki matakan da demokradiyya ta bada dama wajen dakatar da zanga-zangar gama-gari da ke tafe a watan Agusta. Jagorar ƙungiyar, A'isha Hassan Saraki wacce ɗaliba ce makarantar 'Sunshine International', ta gana da manema labarai a ranar Asabar inda ta ce a matsayinsu na jikokin Tinubu, su na kira gare shi da ya bi hanyoyin da doka ta amince da su wajen magance matsalolin Nijeriya. A'isha mai shekaru 8, ta ce a madadin iyayensu da ma ƙasa baki ɗaya su na roƙo da…
Read More

Ƴar Tinubu ta soki zanga-zangar tsadar rayuwa, ta ce yin hakan kan mahaifinta ya yi wuri

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴar Shugaba Tinubu, Folshade Tinubu-Ojo ta caccaki zanga-zangar tsadar rayuwa da aka shirya yi a Nijeriya, tana mai cewa hakan wa ƙoƙarin da mahaifinta ke yi wa ƙasar ya yi wuri. Folshade wacce ita ce babbar 'Iyaloja' ta Jihar Legas ta faɗi hakan ne a lokacin da take ganawa da taron ƴan kasuwa cikin wata ɗaukar bidiyo a ranar Lahadi a Jihar Legas. A lokacin da ta ke magana da mata ƴan kasuwa ta harshen Yarbanci, Folshade ta yi kira gare su da su gargaɗi ƴaƴansu game da haɗurran zanga-zanga, ta na mai bada misali da…
Read More

Dalilan da su ka dawo da layukan man fetur a Abuja da Legas – NNPCL

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ce tseko da ake samu daga wuraren jido man fetur su suka haifar da wahalarsa a Abuja da Legas. Wata sanarwa da Jami'in yaɗa labara NNPL, Olufemi Soneye ya fitar a ranar Asabar, ta ce kamfanin na ƙoƙari wajen shawo kan matsalar, kamar yadda 'Blueprint' ta ruwaito. Ya ce, suna cigaba da aiki tuƙuru da masu-ruwa-da-tsaki domin ganin an warware matsalolin da ke haifar da layukan. Soneye, ya ƙara da cewa su na fatan nan ba da jimawa ba za a dawo sayen man yadda aka saba a wuraren…
Read More

An dakatar da Cynthia ta Nijeriya daga gasar Olympics bisa gwajin ƙwayoyi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An dakatar da ƴar wasan 'boxing' ta Nijeriya, Cynthia Ogunsemilore daga shiga gasar Olympics sakamakon gwajin ƙwayoyi da aka yi mata a ranar Asabar a yayin da ake cigaba da shirin wasanta na farko. Hukumar gwajin ƙwayoyi ta ƙasa-da-ƙasa, ta ce bayan gwajin Cynthia an tabbatar cewa ta na shan maganin 'furosemide wanda yana daga cikin ababan da hukumar ta haramta wa ƴan wasa. Shafin ATI ya wallafa cewa, a halin yanzu an dakatar da ita har sai an warwara matsalar kamar yadda ya ke a cikin dokokin kwamitin gasar. Sannan, hakan ya nuna cewa Cynthia…
Read More

Gwamnati ta ƙaryata jawabin ‘Tinubu Speaks’ da ke yawo

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A wani yunƙurin gaggawa game da wani jawabi da aka yi wa laƙabi da 'Tinubu Speaks' da ake danganta shi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata abin da ke ciki tare da nesanta Shugaban da shi. A ranar Asabar ne Mai magana da yawun Shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya yi watsi da saƙon, yana mai cewa ba gaskiya ne abin da ake jingina wa Shugaba Tinubu. Ana yaɗa ƙirƙirarren labarin ne a kafafen sada zumunta kan cewa wani jawabi ne da Tinubu ya yi inda ya ke magana game da ƙalubalen da…
Read More

NIS ta dakatar da ɗaukar hutu ga ma’aikata kan zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI La'akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da ke tafe a watan Agusta, hukumar shige da fice, NIS ta sanar da dakatar da neman zuwa hutu ga ma'aikatanta na wucin-gadi. Kwamturola Janar ta hukumar, Misis Kemi Nandap ta bada umarni ga shugabannin shiyyoyi da na jihohi da kuma na yankuna, inda ta ce akwai buƙatar aiki na musamman a kan iyakokin ƙasa domin tabbatar da tsaro a lokacin zanga-zangar. Cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Kenneth Udo ya fitar, hukumar ta ce tana shirye-shirye domin tsare duk wani kutse da ka iya tunkaro ƙasar…
Read More

Majalisar Wakilai ta shirya neman a tsige Kyari daga shugabancin NNPC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Majalisar Wakilai ta yi barazanar kiran a tsige shugaban kamfanin man fetur na Ƙasa (NNPC), Mele Kyari idan ya cigaba da takurawa ayyukan matatar Ɗangote. Mataimakin kakakin majalisar, Philip Agbese ya faɗi hakan a yayin hira da manema labaru a Abuja. Haka nan, Agbese ya ce Majalisar ta bayyana goyon bayanta game da tsige shugaban hukumar tace man fetur ta Ƙasa (NMDPRA), Umar Farouk, yana mai cewa NNPCL da NMDPRA sun nuna kushewarsu da ƙiyayya ga matatar Ɗangote wanda hakan ya haifar da matsaloli wa ƙasa Nijeriya. Ya ƙara da cewa, tuni dai Majalisa ta umarci…
Read More

Ki bayyana yadda za a magance matsaloli madadin takura wa zanga-zanga, CISLAC ga Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Cibiyar tabbatar da dokoki wa al'umma, CISLAC ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta tsara jadawalin magance koken ƴan ƙasa a madadin sanya takunkumi ga zanga-zanga. Daraktan CISLAC, Kwamared Auwal Musa Rafsanjani ya nuna buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa game da matsalolin hauhawar farashi, rashin aikin yi, rashawa, rashin tsaro da kuma rarrabewar cibiyoyi. Rafsanjani ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakin bada kariya ga masu zanga-zanga, yana mai cewa dokar ƙasa ta amince da zanga-zangar lumana. Haka nan, ya bukaci ƙananan hukumomi da jihohi su bi hanyoyin da suka dace wajen fuskantar matsalolin…
Read More

Ku bada ƙarfinku ga zaɓe maimakon zanga-zanga – Kwankwaso

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da laifuka shida na siyasa da tattali yayin da ya buƙaci al'ummar Nijeriya su mayar da hankali kan zaɓe ba zanga-zanga ba. Kwankwaso ya faɗi haka a ranar Asabar cikin wata sanarwa da ya fitar game da batun zanga-zangar 'EndBadGovernment', yana mai nuna damuwa kan halin da Nijeriya ta tsinci kanta inda ya danganta hakan da gazawar gwamanti tun daga shekarar 2007. Ya ce, shugabanci mai kyau da adalci na girmama dokar ƙasa, bayyanawa ga kowa,…
Read More

Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargaɗi kan zanga-zangar gama-gari a Nijeriya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya yi gargaɗi game da zanga-zangar gama-gari da ake shirin yi a Nijeriya wanda ake tsammanin farawar sa daga 29 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta. Sanarwar ta wacce ta fito daga ofishin, ta ce zanga-zangar ka iya haifar da tare hanyoyi, madakatun bincike, cinkoson ababan hawa da artabu na gaba-da-gaba duk da cewa ba a san takamaiman wuraren da hakan za su faru ba. Domin kaucewa faɗawa cikin haɗari, ofishin jakadancin ya bada shawarwari kamar haka; Bibiyar gidajen jaridu na gida domin samun labaru da ɗumi-ɗuminsu, nisantar tarurruka,…
Read More