29
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙasashen Amurka, Birtaniya da Canada sun ankarar da al'ummar Nijeriya game yiwuwar aukuwar tashin-tashina yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da za a fara a ranar Alhamis. Ƙasashen sun aika sakonnin ne ta mabanbanta hanyoyi inda su ka gargaɗi mutanensu da su ƙaurace wa artabu da ka iya aukuwa tsakanin jami'an tsaro da ƴan zanga-zanga, su na masu bada misali da ire-iren yadda su ka faru a baya. Sannan, saƙonnin sun iso ne bayan da manyan ƴan kasuwa a jihohin Abuja, Sakkwato, Kano, Katsina, Ogun, Osun, Zamfara, Gombe da wasu yankunan Nijeriya su ka buƙaci a tsaurara tsaro…
