Babaji

4796 Posts

Bom ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a Borno

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Aƙalla mutane 19 ne su ka rasa rayukansu a yayin fashewar wani bom da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne su ka dasa a wajen cin abinci a ƙauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno. Lamarin, ya auku ne a ranar Laraba, kwanaki bayan da mayaƙan su ka kai hari ofishin ƴan sandan Jakana da ke ƙaramar hukumar inda aka kashe ɗan sanda da wata mata tare da ƙona motocin sintiri guda biyu. Wani jami'in gwamnati daga ƙauyen, ya ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:50 na dare inda mutane ke…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta taƙaice filin wasan MKO Abiola a matsayin wajen zanga-zanga a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake shirin fara zanga-zangar tsadar rayuwa a gobe Alhamis, babbar kotun birnin tarayya Abuja, ta taƙaice wa ƴan zanga-zanga yin gangaminsu a filin wasa na MKO Abiola a cikin birnin. Mai Shari'a Sylvanus Oriji ya bayar da umarnin hakan a lokacin da ya ke yin hukunci kan wani saƙon neman maslaha da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya shigar. A cikin takardar, Wike ya buƙaci kotun ta dakatar da shugabannin zanga-zangar biyar daga yin zagaye a kan titina, unguwanni, ofisoshi da wasu wuraren da al'umma ke wasu harkoki a Abuja. Daga ranar 1 zuwa 10…
Read More

An tsaurara tsaro a Majalisar Dokokin Nijeriya yayin da mambobi ke zaman gaggawa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A yayin da ake shirye-shiryen fara zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, ƴan majalisar dokoki suna gudanar da zama na gaggawa zauren Majalisar. Sakamakon haka ne aka tsaurara matakan tsaro a kewayen Majalisar, biyo bayan zargin zanga-zanga ka iya ɓarkewa da za ka iya haifar da dakatar da zaman. A ranar Lahadi ne ƴan Majalisar Dokokin su ka sanar da batun wanda hakan ya shafi kwanaki hutunsu na shekara da su ka fara a makonnin da su ka gabata. Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan majalisar wakilai, Rotimi Akin ya fitar ta ce, zaman…
Read More

Zanga-zanga: Gwamnatin Katsina ta umarci a gaggauta rufe makarantu a jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci a rufe dukkan makarantu a faɗin jihar. Sanarwar ta fito daga mai magana da yawun ma'aikatar ilimin ƙananan makarantu, Ɗanjuma Sulaiman inda ya ce gwamnatin ta ce a sanar da mutane musamman iyayen yara cewa hutun zai fara ne daga ranar Laraba. Ya ƙara da cewa, hutun shi ne mafarin hutun zango na uku, ɗaya daga cikin zango-zango da makarantun ke yi a shekarar. Ya yi kira ga iyayen da su ɗakko ƴaƴansu da ke karatu a makarantun kwana zuwa gidajensu, ya na mai cewa dokar ta shafi makarantun kuɗi da…
Read More

Gwamnan Kano ya gayyaci ƴan zanga-zanga gidan gwamnati, ya yi gargaɗin tashin-tashina

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani nau'in tashin-tashina ba yayin da ake gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Gwamnan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin ƴan kasuwa, sarakunan gargajiya da malaman addini a Fadar gwamnatin jihar da ke Kano a ranar Laraba. Abba Kabir ya ce, "zanga-zanga babu inda za ta kai mu. Ina kira ga waɗanda su ke ƙoƙarin aiki da ƴancinsu na yin zanga-zanga da su kaucewa nuna kowace irin halayya da gurɓatattu zasu yi amfani da…
Read More

‘Yan zanga-zanga sun ƙi amincewa da buƙatar Sufeton ‘Yan sanda ta yi a keɓaɓɓun wurare saɓanin kan titina

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Talata ne waɗanda su ka shirya zanga-zangar 'EndBadGovernance' da za a yi a watan Agusta su ka ƙi amincewa da buƙatar Sufeton 'Yan sanda, Kayode Egbetokun, ta neman su gudanar da ita a keɓaɓɓun wurare madadin fitowa kan tituna. Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da tsare-tsaren yadda zanga-zangar za ta gudana, a wani zama da aka yi da jagororin tafiyar da rundunar ƴan sandan. Egbetokun ya ce "ba dai-dai ba ne a yi gangami a kan titi da nufin yin zanga-zanga. Wasu kuma na shirya yin tashin-tashina". Lauya Ebun-Olu Adegboruwa (SAN)…
Read More

Zanga-zanga: Gwamnatin Tinubu na buƙatar taimakon ƴan Nijeriya don tabbatar da ayyukanta, inji Shettima

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mai girma Mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya aika saƙon neman taimakon ƴan Nijeriya kan ƙaddamar da shirye-shirye da ayyukan Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya na mai cewa shugaban ƙasar na nufin al'umma da alkhairi. Ya ce, jita-jita a wasu wurare na cewa Shugaba Tinubu na adawa da cigaban Arewa ko Musulunci ba haka ba ne, ya mai buga misali da cewa hakan da zai nuna yayin raba manyan muƙamai da Tinubu ya yi na ma'aikatu, hukumomi da ofisoshin wasu ɓangarori. Shettima ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin tawagar ƴan jarida…
Read More

DA ƊUMI-ƊUMI: Masu shirya zanga-zanga sun sanar da wuraren haɗuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Talata, 30 ga watan Yuli, masu zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya su ka fitar da wuraren da za a haɗu wanda za a fara daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta. An samu bayanin ne cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun wani lauya mai suna Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) wanda shi ne Antoni Janar na masu shirya zanga-zangar inda a ciki ta ke cewa, saƙo ne zuwa ga Sufeto Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun. Takardar, ta zayyano wuraren da za a yi zanga-zangar da kuma nuni ga muhimmancin hakan…
Read More

Hukumar ‘Yan sanda ta sanar da fara horar da sabbin jami’ai bayan rikici da rundunar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da ƴan sanda, PSC ta sanar da lokacin fara horar da sabbin jami'ai bayan sa'insa tsakanin ta da rundunar kan jadawalin waɗanda aka ɗiba. Yayin da PSC ta fitar da sanarwar ɗaukar sabbin jami'ai 10,000, a ranar 4 ga watan Yuni, rundunar 'Yan sanda ta ƙi amincewa da hakan, ta na mai cewa akwai rashawa da ƙin bin hanyoyin da su ka dace wajen ɗaukar ma'aikatan a cikin hakan. Duk da matsayar rundunar, PSC ta ƙi sauya jadawalin wanda hakan ya sa Ministan harkokin Ƴan sanda, Ibrahim Gaidam ya shiga cikin lamarin tare da…
Read More

Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da aikin titin Magami-Ɗansadau

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanya hannu kan fara aikin hanyar Magami zuwa Ɗansadau wacce za ta kai tsawon kilo mita 108. Gwamnan ya gabatar da hakan ne a yayin zama da Majalisar Zartarwar Jihar a Fadar gwamnatin Zamfara a ranar Litinin. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, hakan na zuwa ne la'akari da ƙoƙarin da gwamnatin Jihar ke yi kan matsalolin tsaro da ya addabi mutanen yankin. Dauda Lawal, "ya ƙaddamar da ƙwantiragin aikin ga kamfanin Gini na Ɗantata da Sawoe kasancewar sa wanda ya…
Read More