30
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Mai Shari'a Kudirat Olatokunbo Motonmori da aka fi sani da Kekere-Ekun a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) ta 23 a ranar 30 ga watan Satumba, 2024, a majalisar lauyoyi da ke Fadar shugaban ƙasa a Abuja. An haifi Kekere-Ekun ne a ranar 7 ga watan Mayu na shekarar 1958 a Landan, a ƙasar Birtaniya. Ta yi karatun Shari'a a Jami'ar Legas inda ta samu digirin farko a shekarar 1980 wanda bayan kammala karatun makarantar shari'a ne, sai aka tabbatar da ita a matsayin lauya a ranar 10 ga watan…
