Babaji

5715 Posts

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu ya tafi hutu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Laraba zuwa ƙasar Birtaniya don fara hutunsa na shekara wanda zai ɗauki tsawon mako biyu. Zai yi amfani da lokacin ne don hutun aiki da kuma yin nazari ga ayyukan gwamnatinsa na gyare-gyaren harkokin tattali, kamar yadda mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Mista Bayo Onanuga ya faɗa cikin wata sanarwa a Abuja. Bayan hutun ya ƙare ne shugaban zai dawo Nijeriya.
Read More

Gwamnan Zamfara ya yi bikin cikar shekaru 28 da ƙirƙiro jihar, ya buƙaci a yi addu’ar samun Zama lafiya

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci a ƙara kaimi wajen addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya a daidai lokacin da ƙasar ke bikin cika shekaru 64 da samun ƴancin kai. Jihar Zamfara na cikin jihohi shida da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta kafa a ranar 1 ga Oktoba, 1996. Gwamna Lawal, acikin wani saƙon fatan alheri da kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Talata, ya ce ranar 1 ga watan Oktoba rana ce ta musamman ta yin tunani akan irin gwagwarmaya da sadaukarwar da kakannin da suka yi fafutukar…
Read More

Buɗaɗɗiyar wasika ga gwamnatin Nijeriya: An bar jaki an koma dukan taiki akan Lafiya

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu! Cikin girmamawa gare ku shugabanni da Jami’o’in Lafiya na ƙasa ta baki ɗaya. Na ɗauki alƙalamina ne domin na kiraye ku akan wani ganganci da kantafi da rayukan al’umma da na ga hukumar haraji ta Nkjeriya ta yi a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Kano, wato 'Best Choice Specialist Hospital' da ke unguwar Gadon Ƙaya kan shataletalen Tal’udu. Wasu daga cikin marasa lafiya da wasu iyaye sun kawo wa jaridar Alfijir labarai ƙorafi akan yadda jami’an hukumar tattara harajin suka zo tare da jam’ian tsaro da bindigogi su na musu barazana akan sai dole…
Read More

N423b: El-Rufa’i ya musanta zargin ya na da hannu a rashawa, ya sha alwashin rantsewa da Ƙu’rani

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya tabbatar da cewa babban dalilin shigar sa harkar siyasa ita ce don ya yi wa al'umma aiki, ba wai ya sauya akalar dukiyoyinsu ba. El-Rufa'i ya faɗi hakan ne a yayin wata hira a gidan Rediyon Freedom a Kaduna inda ya yi watsi da zargin sauya akalar kuɗaɗe a gwamnatinsa, ya na mai cewa a wadace ya ke kafin ya fara jagorancin jihar. A kwanakin baya ne Majalisar Dokokin jihar ta zargi gwamnatin El-Rufa'i da sauya akalar kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 423. Saidai, tsohon gwamnan…
Read More

Iran ta kai wa Isra’ila hare-haren makamai masu linzami

Rundunar sojin Isra'ila ta ce Iran ta ƙaddamar mata da hare-hare masu linzami. Sanarwar da rundunar sojin Isra'ila ta fitar, ta ce hare-haren sun fito ne daga Iran. Iran ta tabbatar da ƙaddamar da hare-haren kan Isra'ila, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar Iran ya tabbatar. Isra'ila ta buƙaci ƴan ƙasarta su kasance cikin shiri tare da neman wurin fakewa idan har sun ji ƙara ta gargaɗi. Masu aiko da rahotanni sun ce an kakkaɓo wasu makaman a sararin samaniyar Jordan. Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce harin makamai masu linzami kusan 100 Iran ta harbo. Sai dai rahotanni sun…
Read More

Ranar ‘Yancin Kai: ‘Yan sanda da masu zanga-zanga sun yi arangama a Abuja da Legas

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake bikin cikar shekaru 64 da samun ƴancin-kai a Nijeriya, wasu masu zanga-zanga sun fito kan tituna a Jihohin Abuja da Legas don nuna damuwa kan halin matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar. Blueprint ta ruwaito cewa a yayin hakan ne masu zanga-zangar suka yi artabu da jami'an tsaro. Omoyele Sowore, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar AAC shi ya jagoranci zagayen a Legas. Ƙungiyoyin al'umma da dama suka shirya zanga-zangar wadda sun yi makamancin ta a kwanakin baya game da halin tsadar rayuwa da al'umma ke ciki…
Read More

Matsin Rayuwa: Na san ku na jin jiki, amma ina daf da sama muku mafita mai ɗorewa — Tinubu ga ƴan Nijeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ƴan Nijeriya ƙudirin gwamnatinsa na samar da mafita mai ɗorewa domin rage musu raɗaɗin matsin rayuwa da suke ciki. Ya bayar da tabbacin ne a jawabinsa da ya yi wa ƴan ƙasa kan bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ƴancin-kai. “Ina sane da halin ƙunci da dayawa daga cikin ku ke fuskanta a cikin waɗannan lokuta masu ƙalubale. “Gwamnatinmu ta san cewa yawancinku suna fama da tsadar rayuwa da neman aiki mai tsoka. Ina so in tabbatar muku cewa ina jin koken ku,” inji shi. Tinubu ya roƙi ƴan Nijeriya da…
Read More

MƊD ta ƙaddamar da bugu biyu na muryoyin Sahel

Ofishin babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman a yankin Sahel, ta fara bugu biyu na "Muryoyin Sahel: Tattaunawa, Hanyoyi, da Magani" a kan yunƙurin da aka samar da bikin ƙaddamar da shi a shekarar 2021. Wannan shiri tare da haɗin-gwiwar Hukumar Shirin Ci-Gaba na MƊD (UNDP), da Ofishin MƊD Mai Kula da Yammacin Afirka da Sahel (UNOWAS), da kuma UNICEF, na da nufin ƙarfafa wa matasa gwiwa a matsayin muhimman abubuwan ci-gaba a yankin. Yayin da yankin Sahel ke fuskantar manyan ƙalubale kamar sauyin yanayi, rashin tsaro, da kuma taɓarɓarewar tattalin arziƙi, an tsara shawarwari na bana ne domin…
Read More

‘Yancin-kai (Independence)

Daga MUHAMMAD BALA GARBA Gobe ranar Independent,Wahala ba mu daina sha ba. Shekaru sittin da ɗori,Ba mu sauya ginin ƙasar ba. Ga shi ƴanci aka ba mu,Bautuwa ba mu daina yi ba. Ilimi an kassara shi,Rashawa ba a bar batun ba. Ba ruwan sha babu NEPA,Me ya sa ba zan koka ba? Babu noma babu kiwo,Ba mu san daɗin ƴanci ba. Lafiya an wargaza ta,Shi ya sa ba zan murna ba. Ga shi fetur na ta tashi,Ga shi ba noma muke ba. Ga abinci yana ta tsada,Ba a ƴan salari muke ba. Ga matasa babu aiki,Kuma gwamnati ba ta kula…
Read More

Zargin Rashawa: Gwamnatin Tarayya ta naɗa kwamiti don binciken hukumar gyaran hali

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta naɗa kwamitin bincike game da batun zargin rashawa da saɓa wa ƙa'idodin aiki a Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCos). Ministan Harkokin Cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya ƙaddamar da kwamitin a ranar Litinin a Abuja inda ya ce kwamitin zai yi bincike game da zargin jami'an hukumar da bai wa Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky mafaka. Ministan ya ce, akwai buƙatar a tsaftace hukumar don tabbatar da gaskiya da adalci. A kwanakin baya ne ministan wanda shine shugaban hukumar haɗaka ta hukumomin Civil Defence, gyaran hali da shige-da-fice (CDCFIB),…
Read More