28
Jun
Daga FAROUK ABBAS Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya karbi baƙuncin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a gidansa da ke Abuja a ranar Alhamis, kwanaki kaɗan bayan kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ziyara a Daura, Jihar Katsina. A ƴan kwanakin nan ne El-Rufa'i na jam'iyyar APC, ya yi ta ganawa abokanan hamayyarsu na siyasa ciki har da ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma ziyartar shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa a Abuja da ya yi. El-Rufa'i, wanda tsohon ministan Abuja ne, na ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa za a basu muƙaman…
