30
Jun
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya roƙi a yi bincike kan zargin rage kuɗaɗen giratuti na tsofaffin ma'aikata ƙarƙashin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje. A lokacin da ya ke jawabi a bikin ƙaddamar da zango ba biyu na biyan giratuti da na ma'aikatan da suka mutu, Abba ya ce akwai Naira biliyan 5 da aka rage na ƴan fansho mutum 4,000 cikin kuɗin wanda babu bayanai a kan su, don haka ya buƙaci hukumar da ke da alhaki a kai, ta yi bincike. Abba ya shawarci ƙungiyar ƴan fansho ta ƙasa (NUP), da ta shigar da…
